Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

dai yanda ta ajiye hakan za ta zo ta d'auke shi sai dai ta bayar sadaka wa almajirai. Tun safe take hada-hadar tarbon k'awayen ta da suka yi mata alk'awarin kawo mata ziyara yau d'in. Tana gama ayyukkan ne ta yi wanka ta shirya cikin wata shadda brown fitted gown, ko minti biyar bata yi da shirin ba sai ga su sun zo su hud'u Salmat ce cikon ta biyar d'in su. Hakan suka baje sai hirar makarantar suke ta zubawa, wanda a ciki ne suke gaya mata Ummulkhairi ce matar Ustaz Yusuf ya yin da Safiya ake maganar ta da Ustaz Lukman. Da la'asar ne suka ta shi wuce wa ta rik'e Salmat kan ce wa sai zuwa marece za ta wuce, da hakan suka fice suka bar ta. Hira suka dasa tsakanin su inda Zajlah ta kwashe yanda maganar auren ta ta kasance ta gaya wa Salmat, hak'urin nan dai da Yusrah ta ba ta shi Salmat ta ba ta had'e da nuna mata muhimmancin biyayya. "Ni yanzu ba ma wannan ke damu na ba irin yanda zan yi in tafiyar Baba saudiya ta yi, saboda ko ganin shi ban yi barranta na in gaya mai zan je gida". "Hakan za ki jure gaskiya, kuma ki rik'a kula da gyara mai part d'in shi in har ya fita tun da ya zama dodon ki, Allah ni wannan in ni ce cikin wata d'aya zan gama dashi". Murmushi kawai Zajlah ta yi, da hakan suka yi girkin dare suka k'are. Ba yanda bata yi ba kan Salmat ta tsaya har a gama magrib sannan ta wuce tak'i, "in ma na tsaya wa kika ajiye da zai kai ni in nayi dare? Ga wannan unguwar ta ku kuwar ka banza, ko misk'ilin mijin ki za ki sa ya mayar dani?". "Ina nagan shi ni kaina barranta na insa ya mayar dake, ke dai ayi ta sha'ani". Suna cikin hakan ne sai ga Alamein ya shigo gidan, saboda falo suke tsaye suna maganar za ta wuce. . Ba k'aramin mamaki ya yi ba yanda ya jiyo maganar mutane a falon, saboda yau kwanan shi biyu ko motsin ta bai jiba, abincin da yake gani saman dinning ne ke ba shi tabbacin tana gidan, ba don hakan ba da yace ba mutum a gidan. Ba don suna gab da k'ofa ba da ko sallamar shi ba za su ji ba, saboda iya la66an shi sallamar ta tsaya, gaida shi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa, Direct hanyar part d'in shi yayi, "am ji mana Malam". Muryar ta daki kunnen shi cak ya tsaya ya juyo yana yi mata kallon raini had'e da 6acin rai tattare a fuskar shi na jin haushin Malam data kira shi. "Baban mu zai wuce saudiya zuwa jibi in kai bai da darajar da ko gaisuwar surukai kaje yi mai to y'ar shi na da buk'atar zuwa ta gana da mahaifin ta", cikin isa da gadara Salmat ke gaya mai maganar, don ita ba ta hak'urin wulak'anci. Ba k'aramin k'ok'arin ta Alamein ya gani ba na tsaya ta gaya mai magana a gadaran ce, saboda ita ce Mace ta farko da hakan ta ta6a had'a su har ta dubi k'wayar idon sa ta so ka mai magana. "Kin san ce maki aka yi da aka ta shi d'aura auren a k'afa ta aka d'aure igiyoyin uku akace duk inda zan fita tana manne dani da za ki ce min za taje gida, in ta iya ta biki kuje tare kar ta dawo gidan ba damuwar Alamein bace". "Wannan sunan ga alama kuskure akayi gurin rad'a ma shi, ina ga wanda aka k'udurta daban wannan ya fito a fatar baki daban, saboda kwata-kwata sunan bai dace da mutane irin ku ba". "Amma ina mai baka shawara daka canja takon zamantakewar aure saboda in kai ba'a ta6a ganin ka aka furta ana son ka ba, to Zajlah har masoya sai da ta ture, ba'a kawo ma ita saboda rashin mashin-shi ni ba, darajar iyaye ka ci". Ba ki sake ta barshi ta fizgi hannun Zajlah wacce ta zamo mutum mutumi tana kallon Salmat ta kasa ta6uka komai, falon suka bari don ta taka mata. Sai da suka kai gate sannan ta ja ta tsaya, "yanzu ke har wannan namiji ne za ki tsaya shakkar tunkara don kina son fita?, Allah in ni ce wannan sai dai mu gasa juna wanda ya gasu shi zai yi bayani, kin ji ance in masara ta ji wuta ita ke fad'i". "Allah ran da duk kika jibgu hannun mutane ba ruwa na, kinga haka ranar kika so kawa k'anwar shi magana". "Tabbb su jibga manya, ke ni fa zan iya d'aukar rainin hankali daga talaka d'an uwa na ban d'auka ga mai kud'i ba wallahi, saboda abin sai yayi yawa in kayi sake, don mutum bai ga uba na yawon maula gurin shi ba barranta na ya wulak'anta ni". "Kuma yanzu kin ji da kunnen ki abinda ya furta, saura kar ki shirya kije ma Baba ban kwana, ni wallahi da ni ce to ya bud'e shafin yawo sai inda mai ya k'are". Sosai Zajlah ke mamakin rayuwar Salmat don kwata-kwata bata yo halayyar Mama Inno ba, don tun suna yara ba ta d'aukar raini. Hakan ta sa kai ta fice daga gidan had'e da jadda da mata ce wa sai sun gan ta kamin wu cewar Baba. ** ** *** Fadeel ya shiga damuwa sosai saboda tabbatar da ya rasa yarinyar har abada, domin akan idon shi aka d'aura auren ta da wani, ya san ba k'aramar asara yayi ba saboda samun nutsuwa irin ta ta ga y'an matan yanzu abu ne mai wuya, da hakan ya hak'ura sai dai har kullum yana fatar samun Mace natsattsiya tamkar ta, Fadeel kenan da Zajlah ta yiwa nasiha da zai mari Mum. Ustaz Lukman ma hakan ya yakice Zajlah daga zuciyar shi har ya furta wa Safiya k'awar Zajlah yana son ta saboda gudun yakuma nauyin baki. . Yau dai abinda ta k'udurta data gama girkin breakfast gidan Mum za ta je tayi mata wuni, hakan ya sa ta gama girkin ta cikin lokaci ko ta kan Alamein bata bi ba ta fice saboda sanin cewa yana company. Da shigar ta gidan Mum ke ta tarairayar ta, bata san ina za ta d'ora taba kan murna ita dai yarinyar ta yi mata har ga Allah don tana ganin mutuncin ta sosai. Ganin cewa Mum ta shiga kitchen ne ya sa ta bi ta domin taya ta girki, "ai da kin koma falo kawai, saboda ba girki ne zan yi ba Daddyn ku ne kawai zan yiwa ferfesun kifi". . "Ba komai Mum kawo in d'ora". Hakan ta ba ta girkin saboda matsa mata da tayi kan ta ba ta, suna hira da mai aikin Mum ita ko tana aikin har ta kammala. "Ni fa har yawu na sun tsinke da wannan girkin naki, duk gida ya d'auki k'amshi haka", cewar Mama Talatu. "Kai Mama ai ban ma iya girki sosai ba saboda ko da na tashi gidan mu ban san mahaifiya ta ba sai mahaifi na, Mama Inno kuma bata cika ba mu girki sosai ba duk da mu ma ba zama muke yi

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38