Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

sai dai ba yanda za suyi hakan suka bashi sallama d'in tare da shawarwari na kula da yanayin jikin na shi. Hakan suka d'ungumo suka dawo gida wanda da murnar su Zajlah suka fito taryar su, sai gashi sunyi turus saboda sun zata za su ga Dad ko da da sanda ne ko kuma yana d'ingishi sa6anin ganin da suka yi an tallafo shi daga mota, dukan su sai da suka zubar da hawaye. Godiya Mum ta yiwa su Imran sosai na ganin irin yanda suke ba da kulawa ga ciwon Dad, kuma basu zauna ba tun faruwar abin kullum suna asibiti. "Lallai kun zama abokanen arzik'i, samun irin ku a wannan zamanin sai an tona, Allah ya yi maku albarka yasa ka maku da khairan", tana maganar tana hawaye. "Amen Mum, amma kakki damu wannan ba komai bane yi wa kaine, kuma Dad tamkar uba yake gare mu duk abinda muka yi mai ba fad'uwa ce a gare mu ba, fatar mu kawai a gare shi addu'ar samun sauk'i". Da hakan suka fice daga gidan suna masu tausaya wa zuwa ga Dad. Zajlah ta so ta kwana gidan amma Mum ta nuna mata tunda sun dawo ta tashi ta koma gidan ta had'e da yi mata godiyar d'awainiya da kuma kulawa da ta basuwa akan ciwon Dad, hakan dai ta had'a kayan ta ta wuce don ba hakan taso ba musamman da taga Yusrah ta dawo gidan da zama gaba d'ai. Hakan dai ta kakka6e y'ar k'urar da gidan ya yi sannan ta yi wanka ta kwanta, wata zuciya ke ce mata biki kyauta ba Zajlah ke fa sai da kika gyara inda za ki kwanciya sannan kika kwanta ya kama ta ki gyara wa bawan Allah na shi gurin, wata ke ce mata sassaucin da fa kika samu rashin lafiyar Dad ce amma yanzu in kika shiga sabgar shi zai iya wulak'anta ki, wannan shawarar ta fi duba wa ya sa ta yi kwanciyar ta. * * * "Son ka ga har 10:00pm ta yi kuma Dad ya samu bacci ka tashi kaje gida ka kwanta". "Mum kibar ni na kwana anan, ko na je gidan ba bacci zan samu yi ba". "Bazai yuyu ba Son ko matar ka d'azu na kora ta gida saboda haka kai ma ka fice gobe ka dawo". Ba don ran shi ya so ba ya fice daga gidan wanda ko sai da safe bai yiwa Mum ba, shi ala dole an 6ata mai rai. Ko da ya shiga gidan tsab komai ta gyara sa6anin d'akin shi dake fama da k'ura birjit, ganin cewa bazai iya kwana d'akin ba haka kuma bazai iya ta6a k'urar ba ya sa ya d'auko blanket ya dawo falo ya yi shimfid'a ya kwanta, da tunane-tunane fal a ranshi 6arawo ya yi gaba dashi. ** ** Washe gari Kiran sallar farko ya tayar da ita daga baccin duk da bata cikin tsalki, wannan sabo ne duk baccin da take yi da ankira sallah za ta tashi, alwala ta yi ta d'auko littafin ta na azkar tana karanta wa, sai wurin k'arfe 07:00am ta fito domin samun abinda za ta dafa taci. Turus ta yi a falon ganin shimfid'ar shi alamar nan ya kwana, ji ta yi ba dad'i a ranta ko ba komai ya ci ta kyautata mai matsayin shi na mijin ta kodon gudun fad'awa fushin ubangiji, saboda tasan hakk'ok'in miji akan matar shi kuma tasan na mata akan mijin ta. A fili ta furta "insha Allah Alamein daga yau zan kula da hakk'in ka a kaina ko da ba zaka kula da nawa ba". Kitchen ta fasa shiga ta yi d'akin shi duk da gaban ta dake dukan uku-uku, ga mamakin ta tana tura k'ofar ta ji ta a bud'e turus ta yi ganin yanda d'akin ya yi uwar k'ura. Ita da na ta ta kasa kwana cikin shi ina ta ga na shi da tun auren su bai ga gyara ba, karfa ta mayar da mijin ta KAZAMIN MIJI (SIS JABO), duk tsaftar namiji ba kowa ne daga cikin maza zai iya gyaran d'akin shi ba saboda haka za ta tashi tsaye a wannan 6angaren. Gyaran d'akin ta shiga yi sosai, sannan ta fad'a toilet kayan shi k'anana ta saka a wash machine ta wanke sannan ta wanke toilet d'in, kayan wanki ta had'a ta fito dasu ta kaiwa Baba maigadi akan cewa don Allah yasamu mai wanki da guga yaba shi ya wanke, "aiko yaro na sana'ar shi ce zan kai mai ya wanke". Godiya ta yi mai sannan ta koma gidan ta d'auki turarukan d'aki ta je d'akin shi ta fesa, kitchen ta wuce ta yi masu girki ta saka mai a kuloli ta kai dinning table, Baba maigadi ta kaiwa sannan ta ci na ta ta fad'a wanka. ** ** 6angaren Alamein kuwa daga masallaci ya rok'i liman a saka Baban shi a addu'a sannan ya fitar da kud'i ya bada a raba sadaka, daga nan gidan su ya wuce domin duba jikin Dad. ** ** K'arfe 11:00am ta kammala duka ayukkan gidan sannan ta fice zuwa gidan su Alamein, a gate suka had'u tana rik'e da kula a hannu kamar ta wuce komai ta tuna ta tsaya ta gaida shi, nan ya amsa ba yabo ba fallasa ta shige gidan shi ko ya fice zuwa gida. . Yana komawa gidan ya nufi dining table ya ci abinci kad'an duk da yana ganin yau ya ci dayawa akan tun fara ciwon Dad bai ta6a cin abinci irin yau ba, d'akin shi ya nufa domin ya yi wanka ya koma gidan su, yana tunkarar hanya k'amshi na tarbon shi har ya sadu da k'ofar, yana turawa ya yi turus yana kallon d'akin saboda yanda komai ya fito tsaf sai k'amshi dake tashi d'akin, saman gadon ya je ya kwanta yana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba dashi. ** ** Tana shiga gidan ta gaisa dasu ta bawa Mum Kular abincin da ta zo wa Dad dashi, "dama kenan jira kike yi gari ya waye ki fito tamkar wacce ke zaune saman k'aya", cewar Mum. Murmushi kawai ta yi saboda tana son zaman gidan musamman yanzu da Yusrah ke gidan saboda Allah ya had'a jinin su sosai. "D'auko kular muje kiga Dad jiki ya yi sauk'i akan jiya", masha Allah Mum Allah yak'ara sauk'i". Da hakan suka shiga d'akin ta ganshi ta yi mai ya jiki duk da ba iya kar6awa yake yi ba sai dai yayi alamar amsawa da kai. "Mum akwai zam-zam a gidan nan?". "Eh akwai Zajlah har galan d'aya da rabi". "Mum kawo rabin galan d'in muga". Bayan ta kawo ne Zajlah ta karanta (falak', Nas, Ikhlas) kowaccen su k'afa uku-uku sannan ta had'a da (Ayatul kursiyyu) had'e da wasu addu'o'i na yayewar lalura ta tofa. "Mum gasu nan ki rik'a bashi yana sha kuma ki rik'a shafe mai jikin shi dasu, insha Allah zansa a gayawa Ustaz Yusuf ko Ustaz Lukman su rik'a zuwa suna yimai addu'a, ba abinda addu'a ba za ta yaye ba sai in ba'a kai kuka gurin ubangiji ba, ubangiji Allah ya tashi kafad'un shi ya yaye lalura". Mum har da hawayen ta na jin dad'in kasancewar Zajlah a cikin zuri'ar ta, "tun

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38