Chapter 11
Chapter 11
basuyi ba kan siyen wani abu da zai shiga dashi gida yak'i, Salis ya nuna zai siya kuma ya hana. Dai-dai da rakiyar da akewa Ango d'akin Amarya cewa yayi ya hutar dasu, hakan ya fice ya bar su nan da mamaki fal a ransu. Da shigar shi gidan ko ta kan Amarya bai bi ba yayi part d'in shi, kayan jikin shi ya rage yayi wanka duk da bak'ar yunwar da yake ji hakan ya dunk'ula ya kwanta don rabon shi da abinci tun goma na safe. ** Kiran asubar farko ta tashi daga baccin, sallah ta fara gabatar wa sannan ta zauna zaman lazimi wanda bata tashi daga gurin ba sai bakwai na safe. Carpet d'in sallar ta ninke sannan ta d'an kimtsa d'akin, k'ullewar da cikin ta yayi ne ta tuna rabon ta da abinci tun la'asar d'in jiya. Bugun k'ofar da ta jine yasa ta saka hijab d'inta ta fito falon, kayan abinci ta gani jere a dinning table d'in. Gate ta nufa inda take jin k'arar ta bud'e k'ofa Sagiru k'anen Salmat ta gani da kula had'e da babban jug. Gayar da ita ya fara yi sannan ya mik'a mata kayan had'e da juyawa zai koma. "Kashigo mana daga ciki". "Aah zan ko ma islamiya ne ko yanzu break muka fito Mama ta aiko ni". "To mu shiga in baka kud'in mashin ko?". "Mama fa ta bani, ga ma mai mashin nan na tsaida waje zai ko ma dani". "Duk dai salon kar ka shigo ne, to ya yi ka gaida su na gode, ka gaya wa Salmat ina dubin ta". Da hakan ya wuce ta rufe k'ofar ta juya zuwan falon, abinda taci karo dashi ne ya saka ta razana wanda saura k'iris jug d'in yafad'i daga hannun ta. Tana doso falon karaf idon su suka had'e yana mai aika mata da mugun sak'on harara tamkar fararen idon shi su fad'o k'asa. Gaban ta ne ya yi mugun fad'uwa had'e da razana, ba k'aramin k'ok'ari ta yiba gurin rik'e kayan da ke hannun ta har za ta ratsa shi ta wuce part d'in ta komai ta tuna ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, ba tare da ta jira zai amsa ba ta wuce kawai. Mamaki ne fal a ranshi sai kuma d'imbin haushi dake cunkushe da zuciyar shi na ganin ce wa ga abinci Mum ta aiko masu tun d'azu amma don rainin hankali ta kira gidan su akawo mata abinci. Wata zuciyar ke yimai tuni kan cewa ka gaya mata an kawo abinci? Ko kuma jiya da ka yi kwanciyar ka ka yi tunanin me za taci?. . Hannu ya bud'a alamar ba ruwan shi ko a jikin shi. Abin sai damun shi yake k'ara yi yanda ya ga wannan mitsitsiyar yarinya wai itace matar shi, a tunanin shi ma ko sa'ar Saudat k'anwar shi bata yi ba aiko k'auye an rage wannan bala'in. Hakan dai ya zauna saman dinning table ya d'an tsakuri abincin kad'an saboda tun ranar da maganar ta 6ullo bai k'ara saka wani abincin kirki a bakin shi ba, har wata rama ya yi sai tsawon da manyan ido. ** 6angaren Zajlah kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba na mugun kallon da ya bita dashi, tun jiya take ta nazari ko za ta kamo makamar auren amma kash data had'a zaren zai tsinke. Saboda tun tashin ta ko a tarihi bata ta6a ganin angon da ya shigo gida daren amarcin sa bai waiwayi Amarya ba sai a kanta. Yanzun take d'ora abubuwa akan mizanin awo ko za ta samu wanne zai rinjayi wani, sai dai abin sai k'ok'arin gagarar ta yake yi. Ba komai bane wannan sai zuwan Mum gidan su da kuma zuwan su Imran, sai dai a tunanin ta mizanin awon ta zaifi rinjaye akan zuwan Mum. Ba akan komai ta karkata can ba sai ganin babu tausayi ko kad'an a k'wayar idon angon barrantana shi So ya samu mazauni ko da kad'an ne, kenan hakan na nufin Mum ce mai auren sanadiyyar gajeren taimakon da tayi mata, inko hakan ne wani taimako ya kusa zama masifa domin dai ita wannan bai dad'a ta da komai ba sai tarin k'uncin rayuwa, in ko hakan ne sam babu adalci a cikin wannan lamarin da sake ashe ranar walima k'anwar shi tadinga so ka mata magana, wanda a wancan lokacin har laifin Salmat ta so hangowa na mayar da martani da ta yi. Tabb lallai ko akwai aiki sabo wankan jego da ruwan fridge. K'arar da cikin ta ya yi ne ta dawo daga duniyar da ta lula, kular ta bud'e taga waina da miya ce sai kuma kunun tsamiya cikin jug. Sanin cewa ba ta iya canye ta ya sa ta dake ta fito daga d'akin, kitchen ta nufa ta d'auko plate da cup har ta dawo d'aki bata ganshi ba. Abinci ta ci sai da ta yi k'at sannan ta shiga ta yi wanka ta kimtsa had'e da k'ara kimtsa d'akin na ta. ** 04:30pm Sai hada-hadar shiri ake yi domin y'ar liyafar da Mum ta shirya da za'ayi a gidan ta nan cikin G.r.a d'in wacce za'a yi Mata zalla. Yusrah ta kira ta aike ta takaiwa Zajlah kayan da za ta saka. Duk k'awayen ta da dangi na kusa ko wa ya zo har da iyaye sun hallara gidan Mum. Wata dakakkiyar shadda kalar purple Mum ta aiko mata sai wani k'aton gyale mai kalar ash da takalman ta ash, Salmat ce mai take mata baya har zuwa masaukin da aka yi mata. Mum Faty & Jegal fan's su ne na farko da isowa gurin liyafa, su Bizzy, Yagani, Zainab, Sharubutu, Maryam, Mmn Eman, Hindatu sune kan gaba-gaba, Musha karatu group su ma sun hallara inda Fatima, Aunty Baraka, Maryama, Ummietta wabi, Mrs Zannah ke ta rabon ido, Mumbarin Jabo ma sun iso Innah Habiba da Yasmeeny a sahun gaba. Zauren karatu Serdeeyer, Meenah, Batul A. Go I sune a gaba, sai Zumunci group had'e da Greatest women inda khairat, ummen Alamein, fati salihu, Jamila sahabi suke jagorantar sauransu. Zahra B~B fan's duk ba'a barsu baya ba, Ashnur, Hauwa jidda, Anee fan's Anee, Ayusha, Zayyenab sun hallara su ma, sai kuma y'an Taskar Lubiee. Kallo ne ya ko ma k'ofar shigowa gurin sanadiyyar wasu Mata da suka doso gurin cikin ankon su na materials iri d'aya wato blue sai gwaggwaro da takalman su kalar sky, cikin nutsuwa suke tafiya har suka doso gurin, Stylish, Autar Hjy, Feedoh Deedoh, Munayshat, Miss Hafcy, Queen Miemie sai kuma Miemi Bee, Fulani ced'iya, Hauwa damary, Mrs Umar su ne suka fara ne mawa manyan su gurin zama sannan suka zauna, ba kowa bane wad'annan face Nagarta masu Nagartattar zuciya duk inda suka gilma kallon su ake yi tamkar wasu taurari. Da hakan akaci liyafa cikin farin ciki da walwala abin sai son barka. . Bayan an watse daga liyafar ne Mum ta tsaida ta gidan ita da Salmat a ce war ta su bari mutane su watse lokacin an gama gaisawa tasa direba ya maida su, duk da ba wani nisa ne dasu ba. Ad'an zaman da ta yi na awanni ne ta fahimci tsantsar son da Mum ke yi mata da kuma Yusrah wacce ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38