Chapter 7
Chapter 7
ke alfahari dasu. . Mamaki fal a ran Saudat na miye silar zuwan Mum gidan su wannan kucakar yarinyar, ga shi tana so ta tambaye ta sai dai kuma bata ga fuskar tambayar ba. Bayan sun dawo ne direct bedroom d'in Dad ta wuce, zaune yake k'asa saman carpet ya jingina jikin shi da kujera yana karatun jarida. "Daddyn Alamein hutawa kawai ake yi"?. "Ba dole ba tunda yanzu kin rage So na da tattali na, ina ga aure zan zo in yi ko zan samu mai bani kulawa", yana maganar ne d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar sa. Murmushi Mum ta yi sosai had'e da tattara hankalin ta guri d'aya ta k'ara matsawa gab dashi. "Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama, ka ga inka nemo mata sai a had'a da naka auren dana son ad'aura rana guda". "Yaushe Son ya nemi mata banda labari? Yaron da ko mata bai cika kulawa ba ina yaga macen da yake so?". "Sanin hakan ne ya sa na nemo mai mata da kaina, yarinya y'ar asali y'ar gidan mutunci mai ilmi". Wata irin zabura ya yi ya kai duban shi zuwa gare ta. . "Kina nufin Son ne za ki yiwa auren dole? Ko ni da nake uban shi ba'a yimin auren dole ba barrantana shi da yake cikin k'urciyar shi", yana maganar ne cikin fad'a-fad'a. "Dad'i na dakai duk yanda ake magana cikin kwanciyar hankali indai aka ta6o yaran ka cikin second d'aya za ka birkice". "Duk duniya ba ni da farin cikin da ya wuce na yara na, babu takura ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta". Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna. Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira. "Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?". "Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil". "Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba". Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin. "Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai". "Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin. Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai. "Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana". Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai. "Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum". Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya. "Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?". "Alamein". Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina. "Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku". "Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe. "Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure". "Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani". Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri. Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi". "Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa. . Cikin sauri suka gaggauta shiryawa suka hau hanyar makaranta. Suna fita suka ci karo da mutumen kamar kullum sai dai sa6anin kullum yau ya fito ya jingina da motar yana waya idon shi akan su tamkar maye. Hakan suka gilma ta gaban shi suka wuce, sallamar da ya yi ce yasa Salmat ta ja birki ta tsaya had'e da rik'e hannun Zajlah dake neman fincikewa. Amsa sallamar ta yi sannan ta nemi ci gaba da tafiya, ganin ce wa in ya k'yale damar shi ta k'arshe za ta wuce, nan ya furta. "Don Allah ki taimakamin da number k'awar ki ina so zanyi magana da ita, na yi tunanin bai dace in tsayar daku saman hanya ba shiyasa nake neman lambar muyi magana a tsanake". Tana ta yar da kanta karaf idon su suka had'e take hoton abinda ya faru ranar ya dawo mata tangaragan, da sauri ta kauda kanta had'e da furta. "Malam kayi hak'uri banda waya kuma an yimin miji, sai an jima". Hannun Salmat ta fincika da k'arfi suka fice wanda Salmat sai mamakin ta take yi fal a ranta. "Haba (ZAZ) wannan abin dame yayi kama?, ke ce fa a kullum ke yi muna nasiha kan ce wa wulak'anta d'an Adam bai da kyau amma ga shi yanzu kin yi da kan ki". . Nan Zajlah ta ba ta hak'uri had'e da ba ta labarin abinda ya faru, sannan ta d'ora da ce was' "a ganin ki wannan ko mijin aure na rasa ya dace da rayuwa ta?". "Duk da hakan ya kama ta ki yi masa uzuri don baki sani ba ko godiya zai yi maki, ko kuma yana tafe da wani abu mai muhimmanci". "Ko ma miye yanzu shi ta sha fa don ba ya gaba na". Da hakan suna tattauna wa har suka kai makaranta. ** "Daddyn Alamein banji kace komai ba har yanzu kan maganar yarinyar, wallahi ina hango alkhairi ne tattare cikin wannan auren in har ta yiyu". "Me kike so ince? Ai magana na hannun ki saboda yanzu ke ce mijin ni ne matar, tun da har kika iya k'udurta neman auren ba da yawu na ba". "Haba abin bai kai haka ba, yanzu ya kamata mukai k'arshen magana kan turawa gidan su yarinyar, in kuma har kana ganin abar maganar ne wallahi ba matsala sai abar ta". "Tu da kin yi magana da Son har ya amince ni me zance? Yanzu ki fara bincika wa kiji in har ba'a yiwa yarinyar miji ba sai kiyi k'ok'arin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38