Chapter 25
Chapter 25
"To amma wannan ta su mai sauk'i ce akan wacce ta kunno kwana biyun nan, a rayuwa ana so mutum komai dukiyar shi yarik'a sayen kadara yana ajiyewa saboda ranar da lalura ta taso zai iya fitarwa ya saida yayi lalurar shi ba tare da wani ya ji shi ba". Zajlah dai zurum ta yi tana sauraren Mum, saboda har yanzu bata fahimci ina ta saka ma gaba ba, a tunanin ta irin dukiya ta Dad bazai ma yuyu ba ace cikin kashi d'ari an ta6a ashirin ba, amma dai bari ta saurare ta har takai k'arshe. * * * ASALIN MU "Mu haifaffin garin Jega ne, ni da Dad d'in ku auren zumunci aka yi mana sanadiyyar mahaifin shi da mahaifi na uwa d'aya uba d'aya, inda tun muna yara iyayen su suka yi hatsarin mota suka rasu, hakan ya yi silar dawowar su gidan mu da zama shi da k'anen shi Muttak'a wato Abban Yusrah". "Hakan Baba na ya rik'a su amana had'e da basu tarbiya gwargwado duk da ba wani hali ne dashi sosai ba, ko da suka dawo gidan da zama dama mahaifiya ta ta rasu tun gurin haihuwa ta sai wata mata da Baba ya auro". "Daga baya soyayya ta k'ullu tsakani na da Kabiru wato Daddyn ku har muka yi aure, shekarar mu kusan bakwai da aure Allah bai bamu haihuwa ba sai daga baya aka samu cikin Son wanda haihuwar shi ta sa Kabiru ya d'auki son duniya ya d'ora mai kuma nan yaci sunan mahaifin shi wato Aminu. Haihuwar shi da wata bakwai ne Allah ya yiwa mahaifina Baba Sani rasuwa inda matar shi Aisha ta gama wanka ta k'ara gaba sanadiyyar bata haihu dashi ba, shi ko Muttak'a ya auro Balkisu mamar su Yusrah". "Hakan zama ya kasance tsakanin mu iya mu saboda bamu da wasu dangi na kusa, Son na da shekara biyar na haifi Saudat lokacin ne Allah ya k'ara bud'awa Dad hanyar samu yana bawa yaran shi kulawa da kuma soyayya wacce ko ni kaina na ta6a su to zan had'u da fushin shi ranar". Lokacin ne kuma arzik'in shi ya k'aru ta hanyar wani babban aminin shi mai kud'i wato Alh Ibrahim wanda yake shahararren mai kud'i sosai, kusan lokaci guda akayi auren mu da nashi, Allah cikin ikon shi matar shi ta samu ciki gurin haihuwa ta rasu ita da abinda ta haifa bak'in cikin hakan ya sa kaf ya had'a dukiyar shi ya ba Dad ajiya, saboda gaskiya babu wanda yasan dangin shi Sana'a ce kawai ta had'a su ko ga hira bai ta6a cewa ga dangin shi ba, don ko neman auren gidan mu aka shige mai gaba, wancan lokacin kurmi ya yi shirin tafiya da zai wuce ne Dad d'inku ke ce mai yaushe zai dawo? Gaya mai ya yi babu rana, sannan ya ce mai in Allah ya yi mai rasuwa ya bashi dukiyar shi kaf. Daga hakan Mum ta yi shiru hawaye na mata zuba cikin k'unar rai. . Zajlah ce ta ni sa had'e da rarrashin Mum ta d'auko mata ruwa tasha sannan ta cigaba kamar haka. "Da hakan ya wuce kurmi wanda bayan kud'in abinci da suturar jikin shi bai fita da komai ba dai-dai da gidan shi sai da ya saida sannan ya bar garin nan. Dad ya so ta6a kasuwanci da kud'in da Alh Ibrahim ya bashi ajiya na nuna mai hakan bai dace ba sannan yabar kud'in ma'ajiyar su ya cigaba da juya nashi gwargwado Allah ya bud'a mai hanyar samu ba laifi. Bayan shekara hud'u da tafiyar shi ne mummunan sak'o ya risk'e mu cewa Allah ya yi mai rasuwa sanadiyyar gobara data tashi gidan da suke zaune, wanda wancan lokacin Dad yaso share maganar sai da na takura shi kan cewa yashiga mota yaje kurmi don tabbatar da zancen, hakan ya sa ya shirya ya je wanda bai dawo ba sai da tabbacin duk wanda ke gidan bai fita ba sanadiyyar wutar dare data tashi ba zato ba tsammani. Bayan rasuwar shi da wata uku ne Dad ke maganar dukiyar margyayin wanda sai da aka nemi malamai had'e da takarda daya rubuta na tabbacin tunda baida kowa in ya rasu Dad ya d'auki kud'in, hakan ya sa kud'i suka zamo nashi. Da su ne ya bud'e company da sauran abubuwan shi na kasuwanci." * * * "Dad ba mutum ne mai son siyen kadarori ba, wanda kullum ina mai bashi shawara kan siyen filaye da kuma shaguna ya bada haya, maganar shi bata wuce yana da dukiyar da ba yaran shi ba har jikokin shi zasu ci su raga wani abu daga ciki". "To yanzu gashi karon farko k'addara ta sauka kan company, kud'in da aka aje account sune ake cirowa ana lalurorin yau da kullum, dai-dai da gida daga wannan da muke ciki sai naku babu ko da filin da za'ayi kiwon kaji a ciki, duk wannan ba shine tashin hankali ba sai tahowar labarin tabbacin Alh Ibrahim yana raye don Alh Taheer abokin Dad da akayi d'awainiyar asibiti dashi shi ya ganshi ra'ayul ayni a Abuja kuma ya bashi tabbacin yana nan tafe kwanan nan". (Ba Zajlah da ake ba labari ba ni kaina Jegal mai d'aukar rahoto ba k'aramar razana nayi ba, don sai da na zaga toilet, lolx). Cikin razana ta tayar da kai ta kalli Mum "yana raye fa? To ya akayi haka? Anya ko inda akace anyi gobarar nan yake?". "Tabbas an ganshi kuma shine, don har lambar Dad ya kar6a don ya kira su gaisa, sai dai ko da yakira ni na d'auka muka gaisa saboda Dad na wanka lokacin, bayani nayi mai kan cewa Dad na asibiti bai da lafiya, ba akan komai ba sai don gudun kar yakira Dad yasan da maganar yayi silar tashin ciwon shi farat d'aya a koma sabuwar jinya, to kinji babbar damuwa ta da kuma tashin hankalin mu ni da Son wanda muke neman mafita kamin abin yazo ga kunnen Dad". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hala Mum kud'in za su kai nawa?", cikin tsananin tashin hankali take maganar don jin take yi tamkar ita wannan musibar ta fad'awa. " kud'in wannan lokacin zasu kai million hamsin, kuma Son yace abinda ke cikin account ba zasu biya kud'in mutumen ba, sannan ba muda masaniya akan komai yanzu Zajlah har sai ya shigo garin nan munji daga gare shi". "Mum ina da shawara d'aya akai in har hakan zai yuyu, saboda a kammala kud'in mutumen kamin ya iso". "Zajlah ba muda wata mafita ta kud'i kuma babu wata kadara da zamu saida mu cika mai kud'in shi, shi ne abin dubawa". "Mum ko mu muke da kadara da zamu saka kasuwa a biya komai cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya ji mu ba". "Ta wacce hanya Zajlah?. "Mum gidan mu za'a saka kasuwa a saida mu ko mu dawo nan gidan mu zauna d'ayan part d'in da ba kowa a ciki". * * * Maganganun ta ne yasa yaja birki ya tsaya don jin me za ta furta, abinda ta fad'a ne ya sa yaja ya yi turus, "me yasa duk iya tunanin mu ni da Mum bamu kawo hakan a zuwan mafita ba?, garin ya ya ta fi mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38