Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

kwanaki ma haka, wanda yanzu auren Zajlah da Alamein ke cikin wata na biyu amma ba wani canji tsakanin su kowa sabgar gaban shi yake yi, inda Zajlah d'inkin ta kawai ta saka ma gaba don tana samun customers da dama ta gurin Salmat, Yusrah da kuma Shema'u. * * 6angaren Salmat kuwa magana ta yi nisa tsakanin ta da Salis inda manya suka shiga gida har an saka ranar auren su. Aikin ta ta gama cikin lokaci saboda za taje gida wurin ganin Baban ta daya dawo daga saudiya jiya. Ba tada niyyar gaya mai komi saboda dama yanzu kusan kwana biyu sai taje gidan Mum, wani lokaci ta shiga gidan mak'ociyar ta Shema'u, ko yanzu a waya ta kira Mum ta shaida mata za taje wuni gida, hakan ya sa tace taje kawai ita ma za tazo daga baya. Bayan ta kimtsa ne ta fita sai da takai saman titi sannan ta samu keke napep ta shiga sai gidan su, da murna ta fad'a gidan ta gaisa da Mama Asabe, gurin Baban na ta taje ta lafe tamkar wata mage, bayan sun gaisa ne yake ta ba ta labarin Makkah yana saka mata albarka har da guntun hawayen shi. "Haba Baba miye na kuka a ciki?, ai wannan abin farin ciki ne a gare mu duka". "Dad'i ne yayi man yawa Zajlah yanda na tai Makkah ta sanadiyyar ki, lallai tabbas y'ay'a mata rahama ne, gashi Allah bai bani d'a namiji ba amma kin zame min tamkar d'a dubu". . "Ba komai Baba, adai yi ta saka mu a addu'a, Allah yasa anyi hajji kar6a66e", "Ameen" ya furta a tak'aice. Ferfesun kifin da ta yi mai ne had'e da alalen dankalin turawa sai so6o da jinja data had'o mai ta zube gaban shi. "Zajlah Duke ina zan kai way'annan kayan? ai sun yi yawa", yana maganar farin ciki fal ranshi. "Baba ba komai kaci sai ka k'oshi, nasan ka yi kewar abincin Nigeria". Naja'atu ce ta zo tana furta "Baba in baza ka iya canyewa ba ni zan taya ka, kaga ma yau komai banci ba". Dariya ta basu sosai. Kayan aka d'iba akace ta kaiwa Mama Inno ta dawo sannan ta fice. Sai zuwa bayan la'asar ne Mum ta iso ita da sarkin jin kai wato Saudat, sai wani sha k'amshi take yi tana yatsinar fuska tamkar anyiwa zawo yayyafi, saura k'iris Zajlah ta kwashe da dariya ganin yanda take yiwa fuska. Kaji ne dak'wa-dak'wa Mum ta soyo ta zo ma Mal Abu dasu, ba k'aramin dad'i Zajlah ke ji ba ganin yanda Mum ke tarairaya da ita da kuma mahaifan ta, godiya suka zuba sosai wanda har suka sa Mum na jin nauyin hakan da suke yi mata. Basu wani dad'e ba suka fice daga gidan. D'aki suka wuce bayan wuce war Mum suna hira, inda magana d'aya ga ta biyu Salmat ta ce Salis kaza. "Ke tsaya! Wai ke nan nuna min za kiyi kinsan soyayya kenan?, sai wani zak'ewa kike yi ba kida hira sai ta Salis". "Habawa yarinya sunan ki sorry, gaskiya har tausayi kike ban da baki san dad'in "So" ba, yarinya da kin more rayuwarki". "Rashin sanin gard'in So wani lokaci ya fi sanin So d'in kwanciyar hankali, ni kinga yanzu hankali na kwance, ke ko kullum la66an ki basu huta da furta Salis kaza ba". Dariya Salmat ta yi sosai, inda a 6angare d'aya take tausaya wa rayuwar auren Zajlah da take ganin an tauye ta dayawa, saboda wannan auren sunan shi farin cikin uwar miji k'uncin surukar ta. ** ** ** Bayan sati biyu ne dubban mutane suka shaida auren SALIS YUSUF & SALMAT INUWA Wanda aka gabatar da biki cikin farin ciki da walwala tsakanin ango da amarya duk da ita ma ba wasu events akayi ba. Kullum Zajlah na saman hanyar gida tun ranar da aka saka Salmat a lalle har yau da za'a kai ta gidan mijin ta unguwar ni'ima. Mum, Yusrah da Saudat sun yiwa Zajlah kara sun zo auren, duk da auren ya zamo tamkar 6angare biyu a gurin su saboda amintakar Alamein, Imran da Salis d'in sun taso tare ne tun primary skul d'in su, inda abotar tasu har ga iyaye ta kai. Hakan aka dunk'ula Amarya aka kai ta d'akin mijin ta, sai dai fatar Allah yabada zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba. Sai da kowa ya watse ne daga ita sai Salmat d'in ta duk'ar da kanta dai-dai kunnen Salmat d'in ta furta "to uwar soyayya kamin nan da wata goma muna jiran muga d'an soyayya". Kasa magana ta yi sai hawaye dake yi mata zuba na kewar gida da iyaye, suna hakan ne Imran ya rako ango nan suka yi raha da zolayar juna sannan Zajlah ta bi Imran ya sauke ta gida. * * Bayan kwana biyu Mum na zaune suna hira da Dad take gaya mai tana ganin fa kamar har yanzu babu wani cigaba tsakanin Alamein da Zajlah. "Koma miye Haj Hasana laifin ki ne, saboda kin tauyewa yaron nan rayuwar jin dad'i sosai, don haka gobe zan kira shi yasauwak'e ma yarinyar wannan auren". Bud'ar bakin ta ke da wuya za tayi magana ya yi mata alama da bai son jin komai daga gare ta, da hakan suka je suka kwanta kowa da abinda yake sak'awa a ran shi. K'arfe 02:00am wayar shi ta d'auki k'ara kamar kar yad'aga saboda baisan lambar ba kuma da fargabar waye zai kira shi da wannan tsakiyar daren. D'agawar shi dai-dai take da furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un", wanda ya yi dai-dai da zaburar Mum daga baccin da take yi, wayar ce ta ku6uce mai inda ya tafi luuu ya fad'i k'asa a sume. . Jijjiga shi Mum ta yi had'e da salati a bakin ta inda ko motsi baya yi, waya ta janyo ta kira Alamein sannan ta fito harabar gidan da kukan ta domin kiran direba da maigadi, har part d'in Dad suka shiga a rud'e, duk iya dabarar da za suyi sun yi amma ko motsawa baiyi ba, kukan Mum dana Saudat kawai kake jiyowa wanda gida duk ya hargitse ya koma tamkar safiya. * * * Gigice ya lalabo makullin motar shi ya sauko ya bud'e falon ya fice, inda ya tayar da maigadin shi don yabud'e mai k'ofa, hankali tashe yake yimai bayanin abinda Mum ta gaya mai. Motsin da ta ji ya yi yawa ne har an bud'e falon an fice ya sa ta yaye labulen window d'in ta, cikin tashin hankali ta hango yana yiwa maigadi bayani. Hijab d'inta ta zaro daga cikin wardrobe ta saka ta fito, tana kawowa gate d'in yana ficewa da motar. Baba maigadi ta tambaya abinda ke faruwa, nan ya yi mata bayani kamar yanda Alamein ya gaya mai. "Baba don Allah ka kula da gidan bara in k'arasa a k'afa". "Haba y'ar nan ki duba fa kiga dare ne, kuma ke Mace ce kiyi hak'uri ki koma zuwa safe muji yanda abin ya kasance". "Baba wallahi bazan iya zama ba har sai na ga wanne yanayi Dad yake ciki, da ganin yanda Alamein ya fita kasan abin sai a hankali". Ganin da gaske ta kama hanyar zuwa gidan ne ya sa ya rufe gate d'in ya mara mata

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38