Chapter 21
Chapter 21
baya. Suna kawowa motar direban Dad na kunno kai a guje, inda ta Alamein ke daga waje ko rufe ta bai yi ba. Mum ce da Saudat suka fito a rud'e inda idon kowa cikin su har sun kumbura, maigadin su ta ba umurnin ya shiga motar Alamein yakai ta asibiti saboda ba za ta iya zama ba, don direban su da Alamein suka wuce da Dad. Nan Zajlah da Saudat suka fad'a motar aka fice dasu sai asibitin Aisha Buhari, wanda ko da suka isa har an shiga A&E dashi sai direba ne da Alamein ke kai kawo a wurin, wanda duk iya nazarin shi ya kasa gano miye silar wannan abin. Juyawa ya yi zuwa ga direba had'e da je fo mai tambayar silar wannan abin. . "Wallahi Yalla6ai yanda ka ganshi hakan Haj ta kira mu muka tarar dashi, bamu San takamemen meke faruwa ba, sai dai ka jira k'arasowar Haj kaji, Allah dai yata shi kafad'ar Alh", yana maganar yana shartar majina. Da hanzari Mum ta fito had'e da tambayar su abinda ake ciki, Alamein ya bata amsa cikin k'arfin hali cewa tun shiga dashi ba wanda yafito har yanzu. "Mum wai miye silar wannan tashin hankalin?, saboda ni dai a sani na Dad ko hawan jini bashi da barranta na inyi tsammanin shi ne ya ta shi". Nan ta kwashe abinda tasani ta gaya mai. Wayar ce ya buk'aci gani inda aka yi sa'a Mum ta fito da ita, kar6a yayi ya binciko last call d'in wayar ya kira, kawai Mum ganin shi ta yi zaune da6as a k'asa sai hawaye ke biyar idon shi. Mutum mutumi ya koma saboda magana kan ta bai iya ta sai dai kaga la66an shi na motsi sai ido da yake saki tamkar sabuwar gawa, hawayen da bakin dake motsawa kawai zai tabbatar ma yana raye ba don hakan ba sai dai kace a sume yake. Cikin tashin hankali Mum ta dafa kafad'ar shi had'e da jero mai tambayoyi cikin rud'u da firgici, wanda shi ko bin ta kawai yake yi da ido. Cikin tashin hankali Zajlah ta samo ruwa a cup gurin masu jinya ta zo gab dashi tana jijjiga kafad'ar shi, addu'a ta yi sosai a ruwan ta bashi ya sha kuma ta dinga Shafa mai su a fuska tana mai k'ara karanto wasu addu'o'i tana tofa mai, inda gaba d'aya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye kan tausaya wa yanayin da suke ciki. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai Mum ke furta wa wanda ta fara jin nutsuwa na sauko mata. Sa6anin Saudat dake wata irin gunza tana fisgar gashin kanta tamkar wata sabuwar kamun hauka. Ajiyar zuciya Alamein ke sauke wa kad'an kad'an saboda wani sanyi da yake ji yana sauko wa tun daga saman kanshi har zuwa yatsan shi. Hannun ta ya janyo da take rik'e da kanshi tana tofa mai addu'a ya d'ora saman k'irjin shi dake dukan tara-tara, ruwan ta kuma d'ora mai a baki ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya ya zube a jikin ta tamkar gawa. K'arar da ta saki ne ta janyo hankalin mutane da dama suka yo gurin, wasu nurse ne guda biyu suka tallafe shi aka shiga d'ayan d'akin dashi na kusa da Dad. (Wayyo ni Jegal meke faruwa haka?, zuciya ta duk ta cunkushe saboda rashin sanin takame-men me ke faruwa da d'a da uba) . Babban tashin hankalin su rashin sanin takamemen abinda ke faruwa, suna hakan ne Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Dad, cikin rud'ani suka tare shi kan cewa ya ake ciki? "Ina son ganin wani daga 6angaren marar lafiyar amma kuma namiji ba Mace ba", daga hakan ya shige office ya bar su tsaye tamkar gumaka a chochi. . "Mum me zai hana a kira Abban Yusrah a gaya mai abinda ke faruwa, tunda ga Alamein shi ma akwance". Wayar Dad dake hannun ta ta mik'a mata alamar ta kira. Alh Muttak'a ta gani rubuce nan ta kira kusan sau uku sai ana hud'u aka d'aga, bayan ta gaida shi cikin nutsuwa ta kora mai bayanin abinda ke faruwa, nan yace gaya nan zuwa. Suna hakan ne direba ya kawo wayar Alamein da ake kira dake cikin mota, Zajlah ce ta d'aga wayar suka gaisa take kora ma Salis abinda ke faruwa, nan ya ce mata shi ma gayanan zuwa . Kusan tare suka iso asibitin, Imran, Salis da kuma Abban Yusrah, ga alama Imran da Salis sun san me ke faruwa amma ganin tsananin tashin hankalin da ake ciki ya hana masu furta komai. Office d'in likitan suka shiga nan yake ce masu "sanadiyyar abinda ya samu Alh wanda ko mu bamu san miye ba ya yi silar mutuwar 6arin jikin shi had'e kuma da hawan jini na farat d'aya wanda ke barazana da rayuwar shi". Su duka ukun "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" suke furtawa, cikin tsananin tashin hankali Abban Yusrah ke furta "wannan wane irin tashin hankali ne dake neman rayuwar d'an uwa na?, ya Allah ka tada kafad'ar Yaya". Imran ne ya yi gyaran murya had'e da ce ma Abban Yusrah "Abba wannan abin yana da nasaba ne da k'onewar ma'aikatar Dad gaba d'aya wacce ba'a san miye silar hakan ba, yanzu hakan daga can muke wanda har yanzu wutar ke ci". "Shi ne ma kiran da muka yiwa Alamein domin yasan yanda zai gayawa Dad maganar cikin kwanciyar hankali, ashe an samu wanda ya gaya mai har ya yi silar jefa wad'annan iyalai cikin tashin hankali". "Innalillah" Abban Yusrah ke ta nanata wa wanda shi ma ga alama ita ce tayi tasirin samun nutsuwar shi da yanzu shi ma ya zube a sume. "To yanzu likita me ake ciki akan ciwon na shi?". "Za ku jira nan da awa hud'u domin samun farfad'owar shi sannan a hau mataki na gaba". Hakan yasa suka fito jiki a mace tamkar wa'anda k'wai ya fashewa a ciki, cikin k'arfin hali Mum ta tunkare su domin jin me ke faruwa. Ganin cewa 6oye mata bai da wata fa'ida ya sa cikin nutsuwa da lallami had'e da nasiha suka gaya mata me ke faruwa. Ba k'aramar bajin ta ta yi ba gurin aro juriya ta yafa ba, bayan "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai "Hasbunallah wa ni'imal wakeel" kawai take nanatawa. Zajlah kanta ba k'aramar gigita ta shiga ba na jin k'addarar da ta sauko ma wa'annan iyalin ba, k'arfin hali ta yi sosai sannan ta tunkari Saudat domin rarrashin ta ganin irin yanayin da ta shiga. Likita ne ya fito daga d'akin da aka shiga da Alamein, cikin sauri suka tunkare shi had'e da jero mai tambayoyi na jin wanne yanayi yake ciki. . "Za ku iya shiga ku duba shi, amma plxxx banda hayaniya saboda yana buk'atar hutu". Haka suka rik'a rigen-gen shiga d'akin. Kwance yake kanshi yana kallon ceiling wanda kallon ne kawai yake yi amma bai da takamemen abinda yake kallo, saboda tunane-tunane da suka dask'are zuciyar shi wanda yake jin tamkar ma ta dai na aiki. Sannun da suke jero mai ya d'an dawo dashi hayyacin shi wanda ba bakin sai ido kawai da yake bin su dasu, sai kai da yake kad'awa alamar amsawa. "Mum kinji me ya samu Dad? Mum Dad
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38