Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
Download Book

da bata labarin da Baba zai wuce su Mama da Anty Salmat har da kuka suka yi, dariya sosai yarinyar ta basu yanda ta zak'e tana bada labari da kwatan ta yanda su Salmat suka yi. D'inkin Yusrah ta janyo tana dubawa had'e da furta "anya Sis ke kika yi wannan d'inkin?, ko wata ke zuwa tana taya ki?", cikin zolaya take maganar. "Tabbb ka ma kan ki ai wannan oga ce a gurin d'inki, tare fa muka fara koyon d'inkin amma yanzu ko wacce ta koya mana ta wuce ta musamman breast cup tamkar ta auna su". "Kai Salmat ki rage sharri fa, ni dai kawai d'inki ke birge ni shiyasa na mayar da hankali na iya". "Kin manta ana gab da auren ki da muka je gidan Zainab mai d'inki muka tarar ta saka wani style gaba ta zuba tagumi akan ta kasa had'a shi sai da kika kar6a kika had'a?". "Na tuna uwar k'wakk'wafi". Keken ta hau ta k'arasa had'a rigar sannan suka koma d'ayan d'akin a falon ta, lemo da ruwa ta kawo masu sannan aka zauna dasa wata sabuwar hira. "To ku tsaida hirar hakanan kuje kitchen ku ne ma mana abinda za muci, saboda ni dai na gaji bazan iya girki ba". Salmat ce ta bi ta kallo had'e da "furta matar nan dad'i ya maki yawa, mu da muke bak'i mu za mu ne mawa kan mu abinci, to tsaya ma da bamu zo ba waye zai dafa maki?". "Manta kawai barta ta huta, nasan gajiya biyu ce saman kanta ga ta Brother na, ga ta keken d'inki", tana maganar had'e da kashewa Salmat ido d'aya. "Ku dai kunga bone wallahi, tahowa zanyi in gayawa su Baba duk ayi maku aure, saboda na fahimci inda kuka dosa". "Kai rufa mana asiri, mu fa yanzu ake renon mu komai bamu sani ba", cewar Yusrah. "Shi ne naga da rarrafe kuka zo gidan nan k'arewar raino, ku dai yi sauri ku fitar da Maza musha shagalin biki". Salmat ce ta furta "ni kam bazan yi aure ba sai kin haihu hud'u tukuna", "Tunda haihuwar kashi ce, wallahi da kin shiga uku in na haihu hud'u kina gida, Allah sai dai mu bada ke sadaka koda a lima mai ne". Dariya suka yi sosai nan Yusrah ta kama hannun Salmat suka fice zuwa kitchen domin samun abinda suka girka. Ita ko Naja'atu ta janyo tana ta ba ta labari sai dariya take yi, ji take yi tamkar farin cikin ta yad'ore hakan. ® . Suna tashi daga office ya ce ma Alamein suje yau gidan shi zai je duba ajiyar shi, jin hakan ya sa Imran yace shima baza'a barshi a baya ba. Hakan ta sa suka d'unguma su duka suka biyo shi, wanda sai fargaba yake yi in ba abinci za suje ci ba, duk da babu abinda basu sani a zaman takewar su ba, sai dai yanzu yana jin nauyin suje gidan ba su da abinda zasu ci. Dabara ce ta fad'o mai na kawai ya nuna masu zai biya gurin Mum yakai mata sak'o, saboda sanin in dai daga office suke direct suka yi gidan to abinci ne na farko da Mum za ta tarye su dashi. Sai dai kash ba yanda bai yi ba Salis ya kafe kan cewa shi fa sai ya je yaga ajiyar shi sannan in zasu wuce su biya su gaida Mum d'in. * * * Abinci suka yi kusan kala uku suka saka a kuloli, saboda cikin su ba wanda yasan cewa ta daina yin girki da Alamein, asali ma Salmat ce ta sa ayi girkin haka a cewar ta gidan Amarya har kullum bai rasa bak'i. Bayan sun k'are girkin ne suka kimtsa gurin sannan suka koma falon ta, abin dariya ko da suka shiga Naja'atu na ta zuba bata lura da Zajlah ma bacci take yi ba. Dariyar su ce ta tayar da ita daga baccin da ya d'auke ta, zama suka yi suna dariyar ta suna furta "neman kud'i da wuya yarinya". "Ai ni ba kud'i ne nake nema ba, rage zango ne nake yi saboda ban aikin komi". "Ashe in aka bada kud'in wannan d'inkin in d'auka kenan", cewar Salmat. Yusrah ta ce' "Sis ni ma zan kawo customers kwanan nan tunda na ga ke expert ce a 6angaren d'inki". Hararar su kawai ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa Yusrah ta saka ta gaba da cewa sai ta yi mata kwalliya don tasan yanzu Brother bai nesa da dawowa, hakan ta saka ta gaba ta yi mata make up had'e da wani nad'i tamkar an d'aura gwaggwaro. (Saura k'iris waya ta ta su6uce ta fad'i, sai dai na rik'e ta gam saboda gudun rasa wacce zan kawo maku rahoto, tabarakallah ahsanul khalik'een kawai nake na natawa, lolx). Baki Salmat ta saki tana kallon Zajlah had'e da furta "lallai make up na fitar da 6oyayyen kyau, to ni ma ba za'a barni a baya ba azo a tsantsara min tawa". * * * Da dosowar su gidan k'amshin abinci ne yatarye su, mamaki fal a fuskar Alamein sai dai kawai ya dake kuma ya basar. Falon suka shiga sai dai wayam ba kowa sai dariyar su ce ke tashi daga falon Zajlah. Masauki suka yiwa kansu suka zube a falon. Hayaniyar da suka jiyo a falo ce ya sa Yusrah ta lek'o, da d'an sauri saurin ta ta iso falon tana mai fad'in "oyoyo Brother na", cikin sakin fuska ya amsa ta sannan ta gaida su Salis. D'akin ta koma ta gaya masu wanda Zajlah kamar kar ta fito sai dai mutuncin su Imran gare ta sun wuce ta yi masu haka, gyale ta janyo ta yafa sannan ta tunkaro hanyar zuwa falon. Duk zumud'i da zagwad'in ta na saka Salis a idon ta sai gashi wata kunya take ji tana dabai baye ta, jin batajin motsin Salmat bayan taba ya sa har za ta bud'e k'ofar kuma ta juya ta saka ta gaba suka fito falon. Gaisawa suka yi wanda Salmat da Zajlah d'in ko ta kan shi basu bi Ba, shi ko kallo guda ya yi ma Zajlah ya ji wani abu ya tsirga mai take ya mayar da kanshi k'asa yana latsar waya ganin cewa tana tare da y'ar uwar ta mai tsiwa. Kamar kullum falon ta suka koma suka ci na su abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon su dukan su. "Ka d'auki ajiyar ka mu wuce, in kuma baka ta shi ba ni in fice", a fad'ar Imran. Salmat ya nuna da yatsa "kaga ajiya ta nan", kallo aka bita dashi wanda ya yi silar k'ara jin kunyar ta tamkar ta nitse. Zajlah kanta ta yi mamakin faruwar hakan, inda Alamein ke dubin me Salis ya hango a wannan fitsararriyar. Da hakan dai suka ke6e suka k'ara tattaunawa tsakanin su, inda soyayya mai k'arfi ta d'inke tsakanin su. Sai da suka yi girkin dare suka ci sannan kowa ya kama gaban shi. Alamein ko anci darajar Yusrah don ita ke saka mai abinci wanda Zajlah bata nuna mata cewa ita kad'ai ke girkin taba, kuma tasan ganin mutane ya sa shi kan shi yaci abincin. . Awanni sun shud'e,

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38