Chapter 29
Chapter 29
tunanin komai ba ya gaya mai address d'in gidan shi. Suna gama waya Mum na doso d'akin na shi, nan yake gaya mata zai yi bak'o duk da bai san waye ba, ya dai ce mai tsohon aminin shi, take nan gaban Mum ya bada rass, saboda jikin ta na bata Alh Ibrahim ne, ganin jikin ta ya yi sanyi ya sa yake tambayar ta ko lafiya, cikin yak'e take bashi amsa da ba komai, "bara inje ad'an tanadi d'an abin motsa baki wa bak'on", da hakan ta fice daga d'akin ba tare data jira me zai ce ba. Wayar Alamein ta kira had'e da gaya mai duk inda yake yayi sauri yak'araso gida. Lokacin yana tare dasu Imran suna process d'in wane business ya kama ta su fara, nan ya yi masu bayani da sauri ya wuce gida. A gate suka had'u da juna dai-dai yana waya da Dad yana gaya mai gashi ya iso gidan, nan Alamein ya tsaya suka gaisa Alh na ta mamakin girman shi, da hakan ya yi mai jagora cikin fargaba suka doshi hanyar shiga falon. Sai yanzu Mum ke nadamar rashin gaya mai da basu yi ba, ba akan komai ba sai akan matsalar ciwon da yakan iya tashi farat d'aya wata babbar matsala ta samu, saboda ko dawowar su Alamein gidan bata gaya mai ansayar da gidan su bane, kawai ta ce mai wani gyara ake yi gidan in an gama za su koma, wanda ga wancan lokacin take hango hakan a zuwan mafita sai yanzu take nadamar aikata hakan. A DALILIN GATA Page 26-30 . Alamein gaba Alh yana biye dashi suka shigo falon, karaf idon su suka had'e guri d'aya inda Dad ya yi mutuwar zaune, idon shi ya fara murzawa domin tabbatar da ba mafalki yake yi ba, bud'ar bakin shi kenan zai kira sunan shi wani irin tari ya taso mai, yi yake yi ba k'akk'auta wa, da saurin Alamein ya taso ya dafe mai gaba had'e da jero mai sannu ba adadi, Mum ce ta mik'o kofin ruwa Alamein ya bashi. "Dad ka kwantar da hankalin ka duk abinda ake ciki munsani kuma insha Allah komai zai zo normal", Alamein kenan dake son kwantar wa Dad da hankali, saboda tsorace yake kar ciwon shi ya tashi. Cikin ikon ubangiji ba wani abu na tashin hankali daya samu Dad, sai dai daka ganshi kasan juriyar da ke tare dashi ba tashi bace shi kad'ai sai da ya aro wata. Mum kanta hankalin ta tashe yake, hakan dai ta jure ta baje ma Alh Ibrahim kayan motsa baki da abinci, bayan gaishe-gaishe ne na yaushe rabo Dad ya kai duban shi ga Alh Ibrahim had'e da furta "muna zaune kawai sai ga sak'on rasuwar ka ta risk'e mu, wanda bamu yarda da hakan ba sai da na garzaya da kai na kurmi sannan aka tabbatar min da hakan, sai kuma yanzu gashi ka dawo, meke faruwa halan?". Gyaran murya ya yi sannan ya fara basu labari kamar haka, "lokacin da wutar ta tashi gidan gaskiya bana ciki na fita siyen tea bakin titi, saboda akwai wani da Allah ya had'a jinin mu dashi wato Alh D'anjimma wanda kusan tare muke lamurran mu dashi, duk wasu abubuwa tare muke yi". "Daren da wannan abin ya faru kuwa, muna kwance ciwon ciki ya taso ma Alh D'anjimma inda ya tada ni yake gayamin, hakan ya yi silar fita ta domin in sawo mai tea, don na ga koda ya kwanta bai ci komai ba, bayan na siyo mai tea ne na nufo hanyar dawowa kawai naga gidan ya kama da wuta sosai, wanda tsabar rud'ewa tasa na koma titin ban shirya ba, banyi aune ba kawai mota tayi watsi dani gefen hanya, nan mutumen ya fito yana neman agaji kan a taimaka mai amma ina hankalin mutane ya yi gurin ceton rayukan mutane da wuta ke ci, hakan mutumen ya cicci6e ni ya saka a mota daga hakan bansan me ya faru ba saboda loosing memory na da nayi, ina tare da wannan mutumen daya zamo ubangida a gare ni a cikin garin Abuja wanda na yi nema tare dashi har Allah yasa na samu d'an abin hannu na". "Bayan y'an shekaru ne ya aura min d'iyar shi Binta wacce miji ya rasu ya bari da d'iya biyu tagwaye har sun girma, bayan auren mune muka samu k'aruwar yara uku wanda har lokacin bana tuna komai a rayuwa ta ta baya". Daga baya ne ubangida na kuma siriki na Alh Usman ya aike ni Lagos gurin wasu harakoki na shi a hanyar dawo wa tane na samu hatsari wanda bayan farfad'owa ta na dawo hayyaci na, lokacin Husain da siriki na na gefe na ina masu kallon rashin sani, bayan an sallamo ni ne yake min bayanin abinda ya same ni". "Bayan sati d'aya da hatsari na ne nake yawan mugun mafalkai wanda na rasa gane masu, sai dai suna tsorata ni sosai kuma abin yana da nasaba da abinda ya faru sama da shekaru Arba'in da suka wuce, sai yanzu nake hango illar abinda na aikata wanda son kai da rud'in shaid'an ya kai ni da aika ta hakan, sanadiyyar hakan yasa tunanin komawa gida ya dawo kai na, da hakan na gayawa suriki na zan je gida in dawo, daga nan na zarce asalin garin mu sokoto na yita bincike har na gano dangi na na asali, inda na nemi yafiyar gagarumin laifin da na aika ta zuwa gare su had'e da alk'awarin gyara akan( BABBAN KUSKUREN DA NA TAFKA, SIS RASH KARDAM)". "A gurin kasuwanci muka had'u da Alh Taheer inda naji Jega rad'am a bakin shi, nan hira ta 6arke tsakanin mu har nake tambayar shi ko yasan ka, yake gayamin kai abokin shi ne, da hakan na kar6i lambar ka wanda gashi Allah ya yi had'uwar mu yanzu". Kowa falon ya jinjina wannan labarin na Alh Ibrahim, sannan Mum ta bashi nasu labarin bayan tafiyar shi, da hakan ya jajanta masu k'addarar da ta hau kan su, wanda har ya fara zargin kan shi da yana da nasaba da abinda ya samu Dad. Cikin nadama k'arara a fuskar shi yakai duba zuwa gare su yana mai cewa "ina mai baku hak'uri da abinda ya faru, saboda bazai rasa nasaba da abinda na aika tane ya shafe ku ba". Cikin rud'ani da tashin hankali suka sako mai ido caaaa, wanda ya kasa had'a ido dasu ya nok'e kan shi k'asa. ......... Cikin rawar murya da fargaba Alamein ke jero mai tambayoyi, wanda bayan ido da Dad ke saki bai da wani abu da zai iya furtawa akan mutuwar jiki, inda dama tun shigowar Alh Ibrahim kawo yanzu kalma guda bai samu furtawa ba. Nan Alh ya cigaba da bada labari kamar haka, "kamar yanda na gaya maku ni d'an sokoto ne to haka abin yake, asalin zamana nan Jega da kuma dukiyar da na barma na k'ara gaba to ba tawa bace hakk'in marayu ce". "Kamar yaya, bangane ba", wannan karon Dad ne ya yi k'arfin halin jero mai wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Mahaifin mu ya kasance mutum ne mai dukiya a wancan lokacin, matan shi uku da yaran shi goma sha biyu, na kasance
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38