Chapter 8
Chapter 8
samun wa'anda za ki tura ayi maganar don bazan sa kai na ba cikin abinda yaro na bai so ba". "Shikenan ba matsala za'a yi yanda ya dace tunda Abban Yusrah na da rayuwar shi, kuma ko da ran ka shi ne waliyyin shi". Da hakan ta fice daga d'akin ta shirya sai gidan su Zajlah. Bayan sun gaisa da Mama Inno ne ta sako mata buk'atar da ke tafe da ita kan tambaya in ba'a tsaidawa Zajlah miji ba kan za su turo manya domin ne mawa yaron su ita. Nan Mama ke tabbatar mata ce wa Zajlah ba tada miji, har suka ajiye kan ce wa za'a turo manya, da hakan Mum ta fice daga gidan. ** Yana batun fice wa ne suci abinci Mama inno ta tsayar da shi take gaya mai abinda ke faruwa. "Kin ga abinda nake gudu, shiyasa nake matsawa Mal Abu kan ce wa yasamu mata yayi aure tunda ya samu lafiya kafin yaran nan su samu mazajen aure, ga shi har an fara zuwa neman su bai da mata, kuma bai dace ayi auren d'aya daga cikin su bai da iyali ba". "Yo in haka ne abar min maganar zan tuntu6i k'awata Asabe in har ta amince sai ayi auren nan da sati d'aya tunda dukan su ba yara bane kuma tana da hankalin ta da nutsuwa, kasan ita ma mijin ta rasuwa yayi". "To shikenan sai munji daga gare ki duk yanda kukayi". Da hakan ya sa kai ya fice zuwa mazaunin su yana mai labarta wa Mal Abu maganar neman auren shi tunda ya k'i nemo wa da kanshi had'e da gaya mai za'a zo neman auren Zajlah. "Ba komai Mal Inuwa Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi, na gode sosai da karamci Allah yabar zumunci". Amein ya furta a tak'aice. Saboda hakan yake jin Mal Abu tamkar d'an uwan shi na jini. ** BAYAN SATI BIYU Anyi auren Mal Abu da Asabe wanda ta tare gidan, suna zaman su na fahimta akan su duka ba yara bane, kuma Asabe Mace ce mai hak'uri da sanin ya kama ta don bata san inda take aza Zajlah ba kan kulawar da take ba ta. Cikin hakan ne Zajlah da Salmat suke zama duk gidan da suke so tsakanin wurin Mama Inno da wurin Mama Asabe. A 6angare d'aya kuwa k'anen Baban Alamein wato Alh Muttak'a Mum ta nema had'e da d'ora mai nauyin maganar auren Alamein, domin halayyar su ba d'aya ba shi da Dad, mutum ne mai karamci da iya zama da mutane. Wanda karamcin shi da sanin halayyar shi ya sa yana tunkarar su Mal Inuwa da magana take nan aka ba shi Zajlah, saboda a tunanin su yaron gurin shi ne ke son ta. . Ustaz Yusuf ne da Ustaz Lukman ke tsaye suna tattauna wa akan tafiyar da tsarin makantar su kan musabak'ar da za'ayi nan da next year. A tsayen da suke ne suna tattaunawar d'alibai ke wuce wa ta gurin suna gaida su ciki kuwa har da su Zajlah. "Wai har yanzu baka tunkari yarinyar nan da maganar cewa kana son ta ba?, kasan fa ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kar wani ya yima shigar sauri". "Bazai ma kawo ba saboda ina nan da shirin tunkarar ta kwanan nan insha Allah, akwai abubuwan da nake jira ne da komai ya kammala zan tunkari mahaifin ta". "To Allah yataimaka yasa kuma rabon kace, da na yima murna sosai saboda hankali da nutsuwar yarinyar". A hakan dai suka k'are tattaunawar suka shiga cikin makarantar domin fara karantar da d'alibai kamar kullum. ** Tun ranar da aka sanarda shi maganar tsayar da ranar auren shi da wacce bai sani ba ya shiga tashin hankali marar misaltuwa wanda daka kai dubanka zuwa gare shi za kasan ya fice daga hayyacin shi. A kullum tunanin shi da wanne ido zai kalli friends d'in shi da kullum yake cika bakin kan cewa Mace ba ta gaban shi, wanda a kullum maganar shi bata wuce shi aure baya gaban shi. K'arar rufe k'ofa ce ta dawo dashi hayyacin shi wanda kan tsabar tashin hankali idon shi har sunyi ja, guri ta nema ta zauna sannan ta fara magana. "Yanzu Brother kana gani za ka zuba ido a d'aura ma aure da wannan yarinyar? Wallahi talakawa ne sosai kuma da ka ga yarinyar za ka shaida cewa ko boko batayi ba, ko kusa baku dace ba wallahi". "Ya kama ta in ma aure ake so kayi to a baka dama ka zak'ulo yarinya mai class ba kamar waccan kucakar ba". A kasalance ya tashi daga kwancen da yake ya saka filo a bayan shi ya jingina da gado, ido ya sako mata tamkar yayi kuka. "Ni ba ma yarinyar ce ta dame ni ba kamar auren da za'a yimin a dai-dai wannan lokacin da ban shirya ma abin ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba bazan iya bijirewa buk'atar Mum ba a gare ni zanyi mata biyayya insha Allah". "To Brother Allah yaba ka iko, kuma yasa auren ya zamo alkhairi a gare ka kamar yanda Mum ke furta wa". A tak'aice ya amsa da Ameen. "Amma ya kama ta ka gayawa su brother Imran saboda fara shirye-shirye, kaga sati biyu ya rage har auren". Wayar shi ya d'auko ya mik'a mata had'e da bata umurnin ta kira Imran da Salis ta gaya masu yana neman su yanzu. Cikin mintunan da basu wuce goma ba suka iso gidan, Mum suka fara biyawa suka gaida sannan suka wuce part d'in shi saboda ba suda shamaki da gidan. Bayan sun shiga d'akin ne suka tarar da Saudat na rarrashin shi kan ko tea ne yasha Wanda duk ya fara jemewa, dak'yar yasha tea d'in kad'an sannan suka gaisa. Nan Saudat ke labarta masu abinda ke faruwa, kowannen su mamaki fal a ran shi. Sai dai jin cewa za6en Mum ne suka ga cewa lallai gata ne aka yimai. Nan dai suka tattauna yanda abubuwan za su kasance, amma ya jajirce kan ba za'a yi komai ba bayan d'aurin aure, a hakan suka biye mai saboda sanin hali. *** 6angaren Zajlah kuwa mamaki ne fal a ranta kan ce wa an tsayar da maganar auren ta da wanda bata sani ba, kuma har yanzu bai zo gidan su ba, to wannan waye shi? Tasan dai ba wanda suka gani a mota bane. Koda jiya ankawo kayan sa Lalle har da lefe duka, anan take jin ana fad'ar cewa mijin bai Nigeria sai ana saura kwana biyu aure zai dawo. "ZAZ mu gayawa Mama ta fitarwa y'an ajin mu da ta su alawar da kuma malamai". "Wannan aikin na kine, ni dai inkin shirya ki fito mu wuce kinga ko jiya mun kusa makara har Ustaz Yusuf na mana fad'an mun fara rashin mayar da hankali yanzu". "Ke kam yanzu da mayar da hankali da rashin mayarwa duk uwar su d'aya ubansu d'aya, saboda dole ki jingine makaranta". Muguwar harara Zajlah ta sakarwa Salmat wanda yasa cikin sauri ta fad'a d'akin Mama Asabe ta d'ebo iya adadin alawar da zasu baiwa y'an ajin su da malamai suka fice. Ustaz Yusuf ne ke rarrashin Ustaz Lukman kan tashin hankalin da ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38