Chapter 24
Chapter 24
farkon had'uwa ta dake jiki na ke bani ke alkhairi ce a gare mu". "Mum ba komai mudai dage da addu'a", da hakan ta fice daga d'akin ta koma falo gurin su Yusrah. * * * * Sai kiran azzahar sannan Alamein ya tashi daga bacci wanka ya fad'a ya kimtsa ya yi masallaci saga can ya wuce gidan su. Bayan an gaisa ne Mum take gaya mai abinda Zajlah ta yi da kuma shawarar da ta basuwa na kiran d'aya daga cikin Malaman su don yiwa Dad addu'a. Baiyi k'asa a gwuywa ba ya yi makarantar tasu Zajlah, da Ustaz Yusuf ya ci karo suka yi magana ya bashi tabbacin zai rik'a zuwa da safe Ustaz Lukman ko bayan isha'i. Godiya ya yi sosai had'e da d'auko kud'i ya bashi, nan ya nuna mai bazai kar6a ba sai dai gobe d'in in ya zo. ** ** Yau sati biyu kenan ana kula da yiwa Dad addu'a had'e da mayar da ruwan zam-zam da Zajlah ta yi mai addu'a ruwan sha da kuma shafe mai jiki, jiki kam Alhmdulillah don yana magana yanzu kuma har yana iya takowa da k'afa daga d'akin shi zuwa gate abin sai son barka. ** * ** D'an zaman da suka yi da Yusrah ya sa ta k'ara sanin kan waya sosai don har whatsap ta bud'e mata kuma ta saka ta group na gyaran jiki dana kwalliya, sai kuma group d'in musha karatu saboda gwada karatun littattafan soyayya, inda take samun littafai har ta rasa na za6a ta karanta. Tana bud'e data ta shiga whatsap ganin cewa ba'a turo AL'ADUN WASU (SIS BATUL) ba ya sa ta rufe data ta hau d'inkin ta da Yusrah ta kawo kusan turmi takwas. * * * Soyayya mai tsafta da kulawar juna ake bugawa tsakanin Salmat da Salis tamkar su had'e juna saboda tarairaya. * * Inda kuma 6angaren Yusrah da Imran soyayya ta k'ullu sanadiyyar zaman da ta yi a gidan Mum shiko Imran yana saman hanyar duba jikin Dad kusan kullum. * * * 6angaren Zajlah kuwa kullum sai ta gyarawa Alamein d'akin shi sannan in ta yi girki za ta ajiye kowanne kuma yana ci, kamar yanda inta gaida shi yake amsa mata cikin sakin fuska sai dai bayan hakan babu wata alak'a tsakanin su. Kamar kullum yau ma ta gama had'a breakfast ta d'auko ta kawo dining ta tarar dashi zaune ya had'a kai da gwuywa, ga alama yana cikin damuwa, bayan ta ajiye ne ta koma kitchen ta d'auki na ta kayan abincin ta yi falon ta. Kasa cin abincin ta yi sai juya cokali da take yi a plate duk jinta take yi ba dad'i, waya ta janyo ta kira Salmat suka gaisa sannan ta kora mata abinda ke damun ta. "Yanzu ne ya dace ki nutsi ku ajiye duk wani shirme da kuka yi a baya saboda mijin ki na cikin tsananin neman taimako da mai bashi shawarwari, saboda haka don Allah ki rik'a bashi kulawa ki ajiye komai a gefe". "Tabbbb Salmat yau ke da kan ki ke furta hakan?, ke fa kika ce in gyara mai zama amma yanzu ke ce mai yi mai yak'i". "Alamein d'in ne ya zamo abin tausayi shi da ubanshi, har dai yanayin da suke fuskanta yanzu dole a tausaya masu, amma kar kiyi saurin bada gari daga shawarwari ki zurma, don nasan ki da raunin zuciya sai anja aji", cikin dariya da zolaya take maganar. "Ke dai kika sani, Allah ya shirye ki", daga hakan ta kashe wayar ta bita da kallo tana nazarin kalaman Salmat. "Lallai ni shaida ce ciwon Dad ya sa Alamein ya sauya, saboda daga ranar da abin ya faru kawo yanzu babu hantara ko kallon raini, ko don yana ta lafiyar ubanshi ce bansani ba". A fili take ta maganganun ta ita kad'ai inda dai ta d'an ci abincin kad'an ta tashi ta mayar da kayan kitchen, turus ta yi a falo ganin yanda ta barshi hakan ta dawo ta tarar da shi tamkar ko yatsan shi bai motsa ba, kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo kanshi ta yi tsaye saboda rashin takamemen ta ina za ta fara, don gaskiya har yanzu tsorace take ga kutsa kanta cikin lamurran shi. A duniya tak'i jinin ganin babban mutum cikin damuwa duk sai taji ta kasa nutsuwa a ranta abin yai ta damun ta, hannu ta kai za ta ta6o shi ko me ta tuna ta fasa oho, zaune ta yi nesa dashi kad'an saman kujerar da yake zaune, gyaran murya ta yi amma kuma a banza ko motsi bai yi ba. Tsoro ta ji sosai na ko ya suma ne a hakan, cikin sauri ta kai hannun ta saman kafad'ar shi ta girgiza shi kad'an ya zabura cikin razana, yana tayar da kan shi idon su suka had'e guri d'aya nan take bugun zuciyar su ya halba lokaci d'aya. . Ganin ya k'i d'auke idon shi akan tane ya sa ta yi saurin kauda na ta idon, saboda ba zata iya jurar kallon fararen idon shi da suka rine suka koma ja ba kan tsananin damuwa tamkar wanda ya ci kuka ya k'oshi, yatsun ta ta dinga wasa dasu kanta na nok'e k'asa. Hannu ya kai ya tallafo hab'ar ta had'e da yi mata alama da d'ayan hannun na me aka yi?. "Na ga tun d'azu baka ci abinci bane shiyasa", "Ayyah kar ki damu zanci yanzu, nagode da kulawa". Wata zuciya ke ce mai me zai hana ka gaya mata damuwar ka tunda ita ta kasa jure taka damuwar har tazo ta yi ma magana, d'ayar ke ce mai kakka tsaya gaya mata komai, me za ta iya yi akai? Salon ka ja ma kanka raini daga gurin ta tunda wuri haka. Tamkar guguwa haka ya ta shi ya nufi d'akin shi ya barta nan zaune sake da baki, "tabbas mai hali ba ya canja halin shi, irin hakan nake gudu shiyasa ba nason sa kaina cikin lamurran shi, ko ma miye Allah ya yaye", a fili take maganar ta ita kad'ai, da hakan ta wuce na ta d'akin. * * * Zuwa la'asar ne ta gama ayukkan ta ta ji tana ra'ayin shiga tak'ara duba jikin Dad, har ta kimtsa ta fito ko motsin Alamein bata ji ba hakan ya sa ta ficewar ta. Tana isa gidan ta gayar da Mum haka ma Dad don jiki ya yi kyau sosai yana magana kuma yana d'an fita sai dai tafiya ba mai nisa ba. Abu d'aya ya yi mata tsaye a rai ganin yanda kwana ukun da bata zo gidan ba Mum ta kod'e ta jeme duk ta fita hayyacin ta tamkar wacce ta yi jinya. "Mum hala ciwo kika yi bansani ba?". "Wallahi a'ah Zajlah jarabobin rayuwa ce kawai da suka yi yawa". "Mum indai ciwon Dad ne ai Alhamdulillah don jiki ya yi dama sosai, sai dai a k'ara dagewa da Addu'a". "Tabbas a rayuwa anason bawa ya yawaita addu'ar Allah ya kare shi da miyagun k'addarori, to su ne suka hau kan Daddyn ku". "Tun lokacin da yafara wannan ciwon abubuwa ke ta kunno kai, wanda masu bashi da way'anda k'addara ta rutsa da dukiyar su suke ta kunnowa neman abar su".
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38