Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ya yi sanyi musamman Saudat da tasha jinin jikin ta tana jiran ko ta kwana, amma ita gaskiya tunda bai kai da marin mahaifiyar ta ba tana son shi a hakan don ta hango nadama k'arara a fuskar shi, amma dai za ta jira taji daga iyayen ta. "Kar ka damu kanka akan wannan abin, saboda zan iya cewa wani wa'azi ne na daban ya sauka akan mu duka, don yaro na bai wuce sati da marin wani dattijo ba muka yi karo da kai, kaga ko naka mai sauk'i ne akan na shi". "Yanzu muna lokacin da y'ay'an masu kud'i basu cika d'aukar talakan mutum da wata k'ima ba, ko kuma sun d'auki cewa dukiyar su za ta sa su taka mutum son ransu kuma su taka banza, suna ganin bashi da wani tsayayye ko kuma a'ah bai da k'imar da za su dube shi da gashi tunda yana talaka". "Shin shi yayo kan shi talaka? Ko kuma shi ya rok'i Allah yabar shi hakan? Ko kuma wani laifi ya yiwa ubangiji shiyasa ya barshi hakan?, ko d'aya, iko ne da kuma banbancewar ubangiji tsakanin bayin shi". "Ni dai ina mai shawartar Ku da girmama mutum ko da ko baku San inda ya fito ba ta hakan na Ku iyaye za su yi daraja ko a bayan idon Ku, kuma indai ni na haifi Saudat na baka ita halak malak", tana duban Dad ta furta hakan. Sannan ta d'ora da cewa "Dadyn Alamein Allah yasa ban yi kaud'i ba", tana maganar tana murmushi. Jikin kowa sai da ya mutu a falon, saboda yanda Mum bata d'auki lamurran duniya a bakin komai ba, da wata ce tabbas da hakan za ta gilma Katanga tsakanin Saudat da Fadeel. "Ba komai Mumyn Saudat, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa", fad'ar Dad kenan da shi ma yake magana cikin sanyi jiki had'e da jin dad'in yanda Allah ya bashi mata mai hankali da nutsuwa, lallai tabbas ya yarda da akace in Allah ya baka mata ta gari to ka samu rabin addinin ka sai dai ka cika rabin tsakanin ka da ubangijin ka, kuma sai yanzu yake hango illolin gatan da ya yi nuna wa yaran shi don yasan ba don ita ba da yanzu gidan shi ya rushe gaba d'aya. "Ku tashi ku koma sit room ku k'arasa zancen ku, siriki na Fadeel a gaida gida". Nan dai suka fahimci Mum Mace ce mai son raha. Da hakan suka koma sit room suka cigaba da hirar su sai yabon Mum Fadeel da Farouk ke yi, inda ita ko Saudat ke jin dad'in yabon da akewa mahaifiyar ta. **** Yana falo yana kallo Zajlah ta shigo ta zauna saman d'ayan kujera sannan ta yi mai sannu da hutawa, bai amsa ba kawai ya taso ya zo saman kujerar da take zaune ya zauna. "Ba ni aron wayar ki zan d'an yi wani abu da ita". Jin ya matse ta har cinyoyin su na gugar juna ya sa ta mik'a mai wayar, a zaton ta ta shi zai yi sai ga shi ya k'ara gyara zama, xender d'in wayar ta ya bud'e ya kamo pix d'in ta da Saudat ta d'auke ta kwana biyu da suka wuce, saboda in bata manta ba ranar ta dame ta da zolayar cewa ta had'u shiyasa ta matsa ta yi mata pix d'in. Tsam ta zabura daga gurin ta koma d'akin ta falo ta kwanta saman kujera, sai mamaki take yi yanda yake shisshige mata kwanan nan, da kuma son kusancin shi da ita, duk yanda take kauce mai sai ya sako ta a lamurran shi, wanda ita ko ko kad'an bata son hakan. (Tau fa Alamein sunan ka sorry, ni dai Jegal na tausaya ma daka bari Zajlah ta gano lagon ka). Alamein sosai yana ganin cigaba a cikin kasuwancin shi, abin kawai sai dai hamdala don yanzu ne yake jin shi mutum kamar kowa kuma yake sanin ya lamurran duniya ke tafiya. Haka kawai ya ji yana sha'awar siyo ma Zajlah wani abu saboda kyautata wa tsakanin su, musamman yanzu da yake ganin cewa da bazar tace yake rawa, in ya tuna cewa tun auren su kawo yanzu bai ta6a siyen wani abu ya bata ba har kunya yake ji, dai-dai da cefanen gidan bai san ya yake tafiya ba, ita ke yi ko Mum bai sani ba, tabbas yanzu yasan cewa ba k'aramin gata Mum ta yi mai ba, gashi duk abinda suke tak'ama dashi sun rasa lokaci d'aya amma gashi ADALILIN GATAN da Mum ta yimai na aura mai nagartattar mata basu shiga k'unci sosai ba, ba abinda yake so irin ya tsokane ta ta dinga fad'a tana cuno baki, wai ita a dole an ta6a ta, yanayin ta da yanayin maganar ta na burge shi, a hakan ya wuce B.L.B plaza ya yi mata siyayya sannan ya hau hanyar gida. Da sallamar shi ya shiga gidan lokacin tana kitchen tana girkin dare, direct ya risk'e ta kitchen d'in, nan ta yi mai sannu da zuwa sannan ta juya ta cigaba da aikin ta. "Ga wannan na siyo maki Zajlah", yanda ya furta sunan na ta ne yasa tsigar jikin ta tashi, ji take yi duk duniya ba wanda ya kaishi iya furta sunan ta. Ta so ta share shi kuma zuciyar ta ta kasa juren hakan, wai me yasa kwanan nan kusancin da yake yi da ita yake janyo mata jin wasu abubuwa a tattare da ita?, ko fita ya yi yanzu har matsuwa take yi bai dawo ba, tana so ta gansu guri d'aya yana tsokanar ta hakan na mata dad'i duk da ba wata doguwar hira ke had'a su ba. Hannun ta ya kama ya damk'a mata ledar da ya shigo da ita, daga hakan bai saurare ta ba ya yi part d'in su Mum. Acan ne Mum take bashi labarin ashe mai neman Saudat ne suka yi karo ranar, nan ta zube mai yanda suka yi daya zo gidan, jikin shi ne ya yi sanyi da hakan had'e da al'ajabin wannan lamari, lallai tabbas Allah mai juya lamurran shi ne yanda ya so, yana nan suna hira da Mum ta k'are girkin ta ta shigo part d'in rik'e da kula data sako ma Dad tuwon semovita da miyar agushi ta ji kifi. "K'arasa ciki ki kai mai y'ar albarka", cewar Mum kenan, da hakan ta wuce d'akin Dad saboda inda sabo yanzu kam ta saba don har zama take yi su yita hira ita dashi, bayan ta kai mai ne ta dawo falon lokacin Saudat ma ta fito nan suka baje ana ta hirar yanda auren Saudat zai kasance. Kiran magrib ne ya tada kowa daga gurin domin gabatar da farali, part d'in su suka wuce inda ya yi alwala ya wuce masallaci ita ko ta fad'a na ta d'akin domin sauke farali. *** Bai shigo gidan ba sai da ya yi sallar isha'i sannan ya wuce ya yiwa Mum sai da safe ya koma part d'in su, abinci ya tarar a dining table kamar kullum amma bai ji motsin taba, hakan ya sa ya fad'a d'akin ta. Zaune take saman sallaya tana karatun K'ur'an cikin k'ira'ar ta mai sanyi da kuma dad'in saurare inda take karanta suratu

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38