Chapter 6
Chapter 6
har zuwa izifi sittin. ** Tun lokacin da yarinyar ta hana ma saurayin marin ta take kwana kuma ta tashi da ita aranta, saboda yarinyar ta burge ta sosai, sai tunani take yi ina ma ace y'ar tace ke da halayyar wannan yarinyar. Hakan take gurin Fadeel wanda duk yanda ya so yafige yarinyar a cikin zuciyar shi abin ya faskara. Duk inda zuciyoyin mutum biyu suke da tunanin ta suke kwana kuma suke tashi, duk inda suke farautar ta domin su ganta abu ya faskara. *** Falon ta shigo ta d'auki remote domin canja tashar, abinda ta ga an nuno ya hana mata canjawa sai gata zaune jagwaf saman kujera. "Saudat! Saudat!! Saudat!!!". Gigice ta fito daga d'akin ta ta fad'o falon saboda kiran da Mum ke ta k'wala mata. Plasma d'in ta bi da kallo saboda itace Mum ke nunawa da yatsan ta, ita dai bata ga komai ba bayan yarinya tana rero karatun Qur'an cikin baiwa kowane harafi hakk'in sa had'e da tajweed. "Mum me ke faruwa halan? Ban fahimci me kike nuna min ba fa". , Nan Mum ta yi mata bayanin yarinyar. Hakan itama Saudat ta ji yarinyar ta burge ta sosai. "Ina so kishirya zuwa anjima ki rakani makarantar su yarinyar nan, dama na yita neman ta duk inda nake sa ran ganin ta bangan taba". "Yanzu Mum me za kije kiyi mata? Sai kita neman yarinya tamkar wacce ta k'ulla maki wani abin arzik'i". Mugun kallon da Mum ta bita dashi ne ya sa taja bakinta ta tsuke. 05:00pm Dai-dai wannan lokacin Mum ta faka motar ta k'ofar makarantar, da Ustaz Yusuf ta fara cin karo k'ofar makarantar. Nan ta yimai bayanin abinda ke tafe da ita, mashin d'inshi yahau yayi mata jagora har k'ofar gidan su Salmat, godiya ta yita yimai har da fitarda kud'i taba shi saidai bai kar6a ba yajuya yakoma. Mota ta hakimce tana wani yatsinar fuska saboda k'ofar gidan da taga sun tsaya wai nan Mum tazo kuma gurin k'aramar yarinya. "Fito mushiga ciki mana". "Shiga ki fito Mum zan jira ki a mota". Fad'a ta dinga yi mata sannan ta fito har da wani handkerchief tana toshe hanci. Gidan suka shiga inda Mama Inno ta yi masu tarbar da ta dace duk da batasan su waye ba. Bayan sun gaisa Mum ke yi mata bayanin gurin Zajlah tazo. Nan Mama ta kira su daga d'aki suka fito. Durk'usawa sukayi har k'asa suka gayar da Mum, bayan ta amsa ne take ta yabon musabak'ar su data gani ana ta haskowa a cikin kowace tasha. Nan ta d'ora da gaya mata itace ta hana wani saurayi ya mara. Har ga Allah ta manta da abinda ya faru sai yanzu data tuna mata. "Laaah Haj wallahi ba komai, ai yiwa kaine don ni ma zanso a daraja nawa iyayen". Da hakan Mum ta basu dubu goma-goma suna ta godiya, itako ta fice daga gidan. , Da sannu Fadeel ya binciko gidan su Zajlah wanda karo uku kenan yana zuwa k'ofar gidan su amma sai jikin shi yayi sanyi yaka sa tunkarar ta yakoma. Yau dai da k'arfin gwiywar shi ya tashi na tunkarar ta yaga ya mata gaskiyar lamari ce wa yana son ta. K'ofar gidan ya zo, amma a tunanin shi na zai iya tunkarar ta yau sai gashi abin ya gagara, ta gaban shi suka zo suka wuce ita da Salmat domin zuwa koyon d'inkin su gidan wata mata dake k'arshen layin su. "Ni fa Zajlah abin nan ya fara d'aure min kai, in har kin lura kusan kwana uku kenan duk muka wuce zanga wannan motar". "Kuma fa abin mamaki ba a ganin na cikin motar su waye saboda duhun glass d'in motar". "Ke kika damu da wannan motar, ni fa zan iya ce maki ban ma ta6a lura da motar ba sai yau dakika yi maganar". "Ai ke dama ba komai kike lura dashi ba, inaganin wataran sai halaka ta hau kan ki bakisan za ta zo ba". "Au dama in abu zai same ka zaka san da zuwan shine?". "Ba hakan nake nufi ba, amma dai ana so ka lura da yanda abubuwa ke tafiya saboda tsaro". Dariya sosai Zajlah ta yi, da hakan suka isa gidan da suke koyon d'inki. ** Yau ne aka aje kan za'a yiwa Baban Zajlah aiki a idon shi, Malam Inuwa, Zajlah da Salmat ne suka yi mai rakiya zuwa Birnin kebbi. Asibitin Sir Yahaya ce aka yi mai aiki kuma aka gama cikin nasara wanda sai da suka had'a shi da medical glass saboda rashin ganin abinda ke nesa dashi. Je kaga murna fal a gurin Mal Abubakar inda yake alfahari da y'ar shi k'waya d'aya tak da Allah ya bashi, wacce ta zame mai y'a d'aya tamkar da dubu. *** Wacece Zajlah? Mal Abubukar d'an asalin k'auyen giwa tazo ne shi da matar shi Basira, auren zumunci ne aka yi masu domin mahaifiyar ta da mahaifin shi ne uwa d'aya uba d'aya. Sun ta so tare da Mal inuwa ne tun shigowar shi garin Jega sanadiyyar Sana'ar kayan gwari wanda daga baya har ya samu matsakaicin gida ya saye a kusa dashi ya dawo nan da zama. Allah ya had'a kan matan su wanda inka gansu zaka rantse da Allah y'an uwan juna ne. Basira ta rasu ne tun ranar da ta haifi Zajlah wanda bata ko saka yarinyar a idon ta ba. Lokacin ita kuma Mama Inno ta haifi Salmat da sati biyu, nan ta kar6i Zajlah ta had'a da Salmat tana shayar dasu. (Asalin sunan Zajlatu ne k'awaye ne suka tak'aita shi da Zajlah, abinda sunan ke nufi rayuwa kyakkyawa kuma mai sunan tana daga cikin tabi'ai, me neman k'arin bayani akan asalin sunan da tarihin mai sunan zai iya searching da KISASUT TABI'AT, amma da larabci). Sun shiga tashin hankali sosai musamman Mama Inno da Mal Abubakar, dole suka dangana saboda wanda yafi su son ta ya kar6i abarsa. Zajlah na da shekara takwas a duniya Baban ta ya makance sanadiyyar ya jima yana gani bishi-bishi sai bai d'aukin abin wata matsala ba har abin ya ta6a idon duka ya daina gani, tun yana iya lalurar kan shi har abin ya gagare shi. Lokacin ne sauran tsirarrin dangin shi suka guje shi sanadiyyar ganin ya zama wata lalura a gare su, wanda shi ba hakan yazauna dasu ba don mutum ne mai taimakon dangin shi duk da shi ma ba wani hali ne dashi ba. Sanadiyyar makarantar shi ne Zajlah ta dawo gurin shi da zama domin taimaka mai da wasu abubuwan da ba za'a rasa ba. Zajlah yarinya ce mai kimanin shekara goma sha shida zuwa sha bakwai, chocolate colour ce ba wata kyakkyawa ce ta azo a gani ba sai dai manyan idon ta da gashin girar ta shike fitar da kyawon ta, yarinya ce mai shape sai dai batada k'iba irin sosai d'in nan. Kamin abubuwa suyi tsanani ansaka su makarantar boko iya primary daga nan basu cigaba ba sai makarantar Arabic dasuka mayar da hankali akan ta. Saboda kowaccen su ta yi sauka uku sai kuma hadda da suke yi har Ustaz Lukman ya saka su acikin musabak'a, wanda sanadiyyar ne har duniya tasan da zaman su inda iyayen su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38