Chapter 5
Chapter 5
umurnin abinda za'a dafa abincin rana, bedroom d'in ta ta wuce duk ranta jagule. 02:30 Talatu mai aiki ce ta gayawa Saudat ta fad'awa Mum an kammala komai. Bedroom d'in ta wuce ta gaya mata sak'on k'are girkin, nan Mum ta bata umurnin kiran Brother su had'u falon Baban su. Bayan sun kammalu anyi lunch an k'are ne ta kai duban ta ga Al'amein. "Za ka iya tuna ranar da kashigowa Dad d'inku cikin 6acin rai har kana gaya mai ka mari wani dattijo?". "Mum me ya kawo wannan maganar?, ai ina ga ta wuce, ko kuma wani fad'an za'a maimaita min?". Yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi. "Kaba ni amsa kawai". Ta furta a tak'aice. "ina ga za'a yi sati biyu ko kwana goma". "Wannan dai-dai yake da maimaita abinda ka aikata akan fuskar mahaifiyar ka", tana kaiwa k'arshe ta fad'a bedroom d'in Dad. Cikin razana su duka uku suke kallon junan su kowanne 6acin rai kwance a fuskar shi musamman Al'amein da har jiyojin kanshi sun fara bayyana. A DALILIN GATA Part 6-10 . "To wai Dad wa ye ya isa har ya d'aga hannu ya kai wa Mum mari kuma ya zauna lafiya a garin nan?". "Son ni ma wannan shi ne abinda nake tambaya, amma nasan ba wanda zai bamu wannan amsar sai ita kanta, kuma nasan mu shekara muna tambaya ba za ta gaya mana ba". , "Dad mushiga daga ciki muji ko za ta gaya mana d'an gidan uban waye shi". Ce war Saudat. Hakan suka d'unguma sai bedroom d'in Dad domin sa mun amsar tambayoyin su. "Mum Alamein ta shi kigaya min wane isasshe ne zai d'aga hannu duk garin nan yadakar min Mata?". Wani guntun murmushi ne ta saki a fuskar ta had'e da girgiza kai alamar ina tausayin tsarin ku. "Wannan shi zai tabbatar muku ce wa duk abinda kayi na alkhairi ko na sharri za ka had'u da makaman cin shi ko mai dad'ewa". "Kuma kai da kake ta da jiyojin wuya me za kayi akai ko da na gayama wa ya mare ni? Ko ka manta shi wanda ka mara yana da y'ay'a kuma sun san darajar shi". "Me kake tunani a wancan lokacin in har ace ko da ka mare shi wani d'an shi na gurin? Ko kana tunanin dukiyar ka za tasa in har suna gurin su k'yale ka?". "Mum ni fa mutumen laifi ya yimin, har ta ya ya zai zo yana tafiyar ganin dama a saman titi". "Haka zalika nima laifi nayi yaron ya mare ni". Cikin damuwa Dad ya bi ta da kallon mamaki, ya rasa ga ne ita wace irin Mace ce da batasan y'ancin kanta ba. Durk'usawa ya yi gabanta ya d'ora hannuwan shi saman k'afafun ta tamkar yayi kuka yake ji ya furta. "Don Allah Mum ki gayamin ya akayi hakan ta faru? Kuma in kin san waye ki gayamin shi please and please Mum?". Murmushi ta yi sosai har hak'oran ta suka bayyana, sannan ta kwashe ko mai ta gaya masu had'e da yaba halayyar yarinyar. Sai lokacin suka saki fuskokin su har Al'amein na furta "wallahi ya kuru da ya aikata wannan d'anyen aikin da ya had'u dani". "Inna san waye shi ko in ban sani ba? Ko kuma inna gaya maku waye shi za ku d'auki mataki?". Da hakan dai ta k'ara janyo hankalin su had'e da k'ara lurar dasu kan muhimmancin girmama na gaba dasu, wanda Dad ke zaune yana sauraren su. ** Duk abinda aka saka ma rana zai zo indai da rai da lafiya. Yau ne ake shirin gabatar da musabak'a ta gari wadda za'a gabatar a makarantar su Zajlah saboda kasancewar makarantar ta su ce babba kuma itace kan gaba a duk sauran makarantin nen garin su. Daga kan y'an izifi biyu aka fara har zuwa kan izifi sittin wanda aka share sati d'aya ana gudanarwa tsakanin makarantu biyar dake garin. Inda aka k'are kuma makarantar su Zajlah ta zamo gwarzuwa a musabak'ar wanda har da Zajlah da Salmat acikin gwarzayen, saboda Zajlah ta yi haddar izifi talatin inda Salmat ta yi izifi ashirin. Bayan kwana ki bakwai ne aka gabatar da ta Jaha a garin Birnin kebbi, daga nan akayi ta k'asa gaba d'aya inda Zajlah ta zo ta d'aya a cikin y'an izifi talatin Salmat kuma ta biyu a cikin y'an izifi ashirin. Sun sa mu kyaututtuka da dama wanda ya had'a da kud'i da keken d'unki Zajlah harda kujerar Makkah wanda sanadiyyar hakan har da guntun hawayen ta na farin ciki. Ko Malaman su kaduba lokacin za kaga farin ciki kwance fal a fuskokin su musamman Ustaz Lukman dake kula da 6angaren masu haddar da kuma wani abu da yake ji kwance k'asan zuciyar shi akan Zajlah. Mahaifin ta farin ciki fal a ran shi harda hawayen shi, ji yake yi ina ma ace yana gani da idon shi yaga wannan rana ta farin ciki da y'ar shi ta zamo gwarzuwar shekara. Hakan suka tarkata suka dawo gida farin ciki fal ransu, sai mak'ota ke ta shigo masu murna da Allah sanya alkhairi. Sun samu kud'i sosai musamman Zajlah da tazo ta d'aya, har gida Ustaz Lukman ya biyo su had'e da kyaututtukan da suka sa mu mota ta kawo masu har k'ofar gida. "Za ku sa mu shigowa makaranta ranar assabar?", ce war Ustaz Lukman. "Ustaz a bamu sati d'aya mana mud'an huta sannan mu shigo". "Sati d'aya ya yi yawa gaskiya saboda bazan jure...... Sai kuma ya canja akalar maganar. "Shikenan Zajlah ku shigo zuwa ranar Larba, tunda kunga yau ta kama Assabar". "To Ustaz mun gode sosai". Da hakan suka shige gidan su Salmat d'in. . Kamin su shiga gidan ne Salmat ta kai duban ta zuwa ga Zajlah had'e da furta. "Yau kin yarda da abinda nake cewa Ustaz Lukman son ki yake yi?". "Ke dai ina ga aure kike so shiyasa kullum maganar ki ba ta wuce ta So ba". "Kina ji fa yau har da furta cewa bazai juri rashin ganin ki ba, sai ya juya maganar saboda kar mu gane inda ya dosa". Dundu ta sakar mata had'e da janyo gashin kanta sai da ta yi k'ara, da hakan suka shiga gidan. Mama Inno ce ta tarye su dukan su ta rungume sai albarka take saka masu har da guntun hawayen ta. "Zajlah yau burin ki zai cika da yardar ubangiji saboda ya yi maki hanyar samun kud'in da za ki kula da matsalar idon mahaifin ki". "Wallahi Mama ina jin tsabar kud'in da nasamu tun a can matsalar Baba ce nafara kawo wa, sai kuma samun abin Sana'a da zai raba mu da yawon bara". "Don ko babu kud'in zan soke matsalar bara tunda na samu keken d'unki zan tashi da koyo har in iya". "Gaskiya kam kinyi tunani mai zurfi, yanzu sai abubuwa sunyi sauk'i ku had'u ke da Salmat kuje koyon d'inki". Da hakan aka shigo da kayan da suka samu gidan su Salmat, inda kowannen su ke da keken d'inkin sai Salmat dake da kud'i dubu d'ari biyu Zajlah ko na da dubu d'ari biyar da kujerar Makkah da shugaban k'asa ya baiwa duk wanda ya yi na d'aya a matakin haddar su tun daga izifi biyu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38