Chapter 37
Chapter 37
ankarar dashi ya fito da sauri, taimaka mata ya yi ta wanke bakin ta sannan suka koma falon. K'amshin tafashen naman na bugun hancin ta ta k'ara fitowa tana wani aman. "My Zaz me kika ci hakan yake ta sakaki amai?", a rud'e yake jero mata tambayar, gaya mai ta yi ya kashe risho d'in ya kawo mata gyalen ta za ta shiga gurin Mum, hakan ya kawo mata suka wuce part d'in Mum gaba d'ayan su. Gaida Mum kawai suka yi ya jefo mata maganar "Mum kinga My Zaz sai amai take ta lezawa har ta kasa zama part d'in mu". Duban ta ta maida ga Zajlah sannan ta ce' "me ke damun ki halan?", duk da tana zargin shigar ciki ne da ita, amma tana so ta tabbatar da zargin ta. "Mum tafasar nama ce ba naso shiyasa", murmushi kawai ta yi had'e da yi mata Allah ya sauk'ak'a sannan ta d'ora da cewa "sai ki ajiye girkin har zuwa lokacin da cikin zai yi k'wari, in yaso a rik'a baku anan". Kunya ce ta kori Zajlah ta yi d'akin Mum ta bar su ita da Alamein, don dama tana zargin cikin saboda watan ta biyu bata ga al'adar ta ba. Bayan ta d'aga ne Alamein ke ta damun Mum da tambayar abinda ke faruwa, nan ta gaya mai ciki ne da Zajlah d'in. Kan murna bai tsaya ta k'arasa bayanin ta ba ya fad'a d'akin Mum d'in don nuna wa Zajlah tsabar murnar shi. **** Akwana a tashi ba wuya a gurin ubangiji, saboda Yusrah ita ma ta sauka, sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba, sanadiyyar hakan yasa Imran ya hana ta zuwa gida wankan jego, dole cikin dangin mamar ta aka tura mata wata domin kulawa da ita yanda ya dace. **** Dak'yar ya barta ta je barkar Ummulkhairi matar Ustaz Lukman, saboda a cewar shi yana kishin ganin ta tare da Ustaz d'in, "banda abinka HUBBY ni da zanje barka me zai had'i na da Ustaz?, wai ma tsaya wa ya gaya ma Ustaz Lukman ya yi "So" na?", da mamaki fal a ranta ta jefo mai tambayar. Sai da ya k'ara had'e fuska sannan ya yi mata bayani kamar haka, "lokacin ciwon Dad kinsan su ke zuwa yiwa Dad addu'a, to nan ne Ustaz Yusuf ke yimin nasiha kan in rik'e ki da kyau, saboda ke Mace ce mai hankali da nutsuwa kuma nayi dace, inda har yake gaya min da yanzu Ustaz Lukman ne mijinki, ba don ma yana kula da mahaifi na ba gaskiya da na sallame shi wancan lokacin, saboda dana kalle shi wani k'unci nake ji". "Su kishi manya, to ni dai tashi muje ba dad'ewa zan ba sai ka jira ni mu dawo tare", da hakan suka fice domin zuwa barkar. A DALILIN GATA Part 31-35 (the end) . Zaune suke suna cin abinci da uban tutse-tsen cikin ta wanda haihuwa ko yau ko gobe. " HUBBY ya kama ta kabar ni naje gida wankan jego, kasan fa daga na farko shikenan ba komawa za'a k'ara yi ba". "Yanzu My Zaz za ki iya tafiya kibar ni cikin tarin kewar ki?, kinsan irin K'aunar da ke tsakanin mu bazan iya jure rashin ki a tare dani ba, ya kama ta ki tausaya min". Zugum ta yi bata ce komai ba saboda ko ita tasan ba zata iya nisa dashi ba sai dole, ya koya mata k'aunar shi mai zafi yanda bata iya nisanta dashi, "My Zaz in kina ra'ayin zuwa bazan takura ki ba, ko yau zaki je sai ki had'a kayan ki, amma nasan zan takura fiye da tunanin ki". "Ba komai Hubby na hak'ura, farin cikin ka shine muradi na har kullum, ni ma nafi so kullum ingan ni tare dakai. Yanzu yaushe ne za mu tare sabon gidan mu?". "Ina ga mubari sai Allah ya sauke ki lafiya kamin suna sai mu tare can ayi suna ko?". "To Allah yanuna mana lokacin", da hakan suka cigaba da tsara yanda abubuwan zasu kasance. *** Baban Zajlah Allah ya bud'e hanyar samu har ya sayi wani fili bayan shi ya had'e da gidan shi ya yi gyara gwargwado, saboda a tunanin shi tilon y'ar shi za ta dawo gida wankan jego, baisan sun riga sun kitsa komai ita da mijin ta ba. *** K'arfe 01:00am ta falka da nak'uda inda tun tana juriya har ta tayar da Alamein daga barci, gigice ya tashi ta gaya mai yakira mata Mum, hakan ya fice ya kira Mum suka zo tare ji yake yi tamkar yad'auke mata ciwon da ke tattare da ita. Magana yake wa Mum kan suje asibiti, ganin haihuwar ta zo gadan-gadan ya sa tace yad'an tsaya suga yanda za'ayi. Duk addu'ar da tazo bakin Zajlah furtawa take yi saboda ta galabaita iya galabai ta, suna batun zuwa asibiti ta sunkuto y'ar ta sannan namijin ya biyo baya, je kaga murna gurin Alamein da Mum. Nan dai Mum ta kimtsa yaran ta kaiwa Alamein sannan ta dawo ta kimtsa Zajlah, tea ta had'a mata mai kauri ta bata tasha. Ko da Mum ta fito falon ya saka yaran gaba yana kallo yana murmushi, "To baban twins aje a kwanta ko?, ba ni yaran inje dasu tunda yanzu 02:30am, kuma nasan da wuya su nemi mamma cikin daren nan". "Gaskiya Mum sai dai ki kwana nan ko kuma in biyo ki part d'in mu kwana can mu duka", baki ta saki galala tana kallon shi. "Anya ko Alamein yanda nake murnar na samu jikoki za ka iya bani yaran nan?". "Ba dai in baki duka ba ko Mum?, ai kyautar d'a sai Allah, zan dai rik'a baki aro koda na awa biyu ne", yana maganar ne had'e da murmushi a fuskar shi da alamar zolaya. Ita ma Mum murmushi ta yi ta d'ora da cewa "to mara kunya ai yara nawa ne saboda y'a ta ta yi nak'udar su ba kai ba, in yanzu tace ta bani sun zama nawa", ganin cewa tabbas baida niyyar bata yaran ya sa ta fice daga part d'in. Duk abinda suke yi Zajlah na jiyo su daga d'akin tana murmushi, sai gashi yana k'wala mata kira, hakan ta janyo jiki ta fito falo d'in, "d'auki yaran mu shiga daga ciki, ni ban iya d'aukar jinjirai ba". Kallon mamaki ta bishi dashi, "amma ko Hubby ka kai, yanzu ma ko yaran baka iya d'auka ba ka hana Mum taje dasu?, to kasan yanda za kayi dasu saboda ni bacci nake ji gaskiya", da hakan ta juya zuwa komawa d'akin. Lalla6a ta ya yi sannan ta dawo ta d'auki namijin sannan ta runguma mai macen suka koma d'aki suka kwanta. Sallar asuba kawai ya yi ya dinga kiran mutane a waya yana gaya masu k'aruwar da suka samu, sai da safe aka kaiwa Dad yaran ya yi masu addu'a had'e da sanya masu albarka. Kamin kace kwabo gida ya cika babu masak'ar tsinke y'an barka, inda Mum ta yi-ta yi dashi akai Zajlah gida ya k'iya, hakan tasa wata k'anwar Mama Inno da Naja'atu suka dawo gidan da zama domin taya ta rainon jinjirai. **** Ana saura kwana biyu suna ne su Salmat, Yusrah, Saudat da Shema'u suka je kimtsa mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38