Chapter 28
Chapter 28
ba. ***" 6angaren Alamein kuwa ba k'aramin mamaki ne ya cika mai ciki ba da ya shiga d'akin ta da sunan fitar da na ta kayan ba, saboda wayam ya gani ba komai kuma ya san dai ko da aka kawo ta da kayan d'akin ta, asali ma gaban shi aka had'a su saboda ranar Mum ta takura shi dole sai ya tsaya gidan har a k'are aikin sannan in fita zai yi ya fita. D'akin ya gani da alamar an d'auke kaya a gurin, to ko ta kai kayan ta ne wani gurin? Ko kuma ta sa ankai mata can gidan? Ganin bai samu amsa bane ya sallami masu kwashe kayan daga d'akin ta, saboda akwatunan tufafin ta tun safe ta saka almajirai suka kai mata, kujeru kuma da sauran tarkace dama ya sa an fita dasu. Ba'a gama ba sai kusan k'arfe d'aya na rana, saboda wasu na kwashe wa suna kai gidan su can kuma da masu had'awa. Dama part d'in da aka basu babban falo ne mai d'auke da d'aki biyu da suke fuskantar juna kowannen su ciki da falo sai toilet a cikin su, kamin a Shiga falon akwai kitchen da store, sai kuma 6angare d'aya toilet d'in tsakar gida. D'aki d'aya aka saka mata na ta kayan a falo sai katifa uwar d'aka, shi ma aka saka mai na shi kayan d'ayan d'akin. Da hakan aka kammala komai na gyara gurin. Zajlah da Saudat suka taya Mum girkin dare sai da suka gama ne sannan ta shiga part d'in su ta yi wanka akan tsabar gajiyar da take ji, abinci ta ci sannan ta je ta kwanta saboda dama Mum ta sako masu nasu wanda dashi ta shigo ta d'ibi na ta ta ajiye mai sauran. Bata fi minti goma da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da ya shigo bai ji motsin ta ba hakan ya sa ya ci abinci ya yi wanka, jin ya yi yana son yaduba ya yanayin k'afarta yake, da hakan ya doshi d'akin ko da ya shiga tana kwance uwar d'aka saman katifa daga ita sai wata night gown mai d'an sharara sai dogon wando gashin kan ta ya bazu saman filon da ta yi matashi dashi, kallo d'aya ya yi mata ya kauda kai saboda wani abu daya ji ya tsirga mai, kuma bai ta6a ganin mace a irin yanayin da ya ganta ba, bakin katifar ya dawo ya zauna ya kai duban shi ga k'afarta yaga gurin har ya soma haushi kad'an, hannu ya kai zai ta6a gurin kuma ya fasa daga hakan ya zabura ya fice daga d'akin tamkar wanda aka tsikara. *** Tana tashi da asuba ta gabatar da sallah had'e da azkar d'inta sannan ta koma saman katifa ta zauna saboda ba aiki za tayi ba don Mum ta gaya mata da safe za'a kawo masu breakfast, tana so ta shiga part d'in su ta taya Mum aiki kuma tana ganin ta yi sauko dayawa, don tasan saurin karyawar su gidan k'arfe 10:00am. Kud'in ta ta jawo ta irga ta koma maidawa ta ajiye a tunanin ta lokacin buk'atar su bata yi ba. Bugun k'ofa ta ji ya sa ta zabura ta fito ta bud'e, Mama talatu ce ta kawo masu kayan breakfast bayan ta kar6a ne ta gaida ta ta koma daga ciki, abinci ta ci sannan ta shiga wanka bayan ta kimtsa ne ta shiga gurin su Mum. **** Bayan azzahar ne Salmat ta kawo mata ziyara, bayan ta gaisa da Mum ne take tambayar jikin Dad inda Mum ta gaya mata ya samu sauk'i sosai. Part d'in Zajlah suka koma aka baje sai hira ake ta zabgawa had'e da shawarwarin abubuwan da suka shafe su. . Akwana a tashi yau satin su biyu kenan a gidan su Alamein, wanda har yanzu babu labarin Alh Ibrahim sai dai a ko yaushe suna masu sauraren zuwan shi, jikin Dad kuma ya yi sauk'i sosai sai dai bai iya doguwar tafiya haka kuma bai cika son doguwar magana ba don in ta yi tsawo ji yake yi tamkar numfashin shi ya d'auke. Kusancin su ya sa abubuwa sunyi sauk'i sosai a zamantakewar su, saboda Alamein na ba ta kulawa gwargwado, kuma wani lokaci sukan had'u part d'in su Mum a baje ana ta hira, amma fa baza su iya hira tsakanin su ba saboda kowa tsorace yake da wani. *** 6angaren Zajlah an samu k'aruwar wayewa a gare ta ta hanyar Anty Shema'u da kuma group-group na whatsap musamman na kwalliya da ake turo videos na kalar kwalliya iri-iri, wasu ma in an turo bata gane ba to gidan Shema za taje tayi mata bayani in ma ta kama ta zauna tayi mata to za ta yi mata da kanta. Tun lokacin da aka yi mata aure Mama Asabe da Mama Inno basu zo gidan taba sai kwana biyu da suka wuce, koshi don ta dame su ne kan basu tahowa kuma Mum tasa baki shiyasa suka zo, inda taji dad'in zuwan su sosai. ** Yau saura kwana biyu auren Yusrah da Imran, su Zajlah babu zama musamman da Mum ta mayarda Yusrah gidan kacokan, a cewar ta ita za ta shirya abar ta, duk wani kayan had'in gyara na jiki ko na Mata a tare Mum ke had'a masu shi wato Yusrah da Zajlah, inda Zajlah ta fito real amarya sai wani k'amshi suke zabgawa ita da Yusrah. Kamar yanda Yusrah ta k'udurta ma ranta tun auren Zajlah haka ta gaya wa Mum cewa makarantar su Zajlah za'a yi mata walima saboda bata son bidi'o'in nan na raya Al'adu, ba k'aramin dad'i suka ji ba na za su ziyarci makarantar su, ko banza sun San cewa tsarin Malaman su da d'aliban na burge mutane da dama. , A gurin walimar ne suke jin labarin auren Ustaz Yusuf da kuma Ustaz Lukman sati biyu da suka wuce, inda matar Ustaz Yusuf ke basu tabbacin har mazan su sun zo auren kuma tare da gudummuwa, nan suka yi masu fatar alkhairi aka k'are walima kowa ya kama gaban shi. Washe gari bayan d'aurin aure ba'a gabatar da komai ba sai dare amarya ta tare a gidan ta dake ni'ima inda basu da wani nisa sosai da Salmat, Zajlah ne da Saudat suka tashi za su fice ta dafa kan Yusrah had'e da furta "muna jiran baby nan da wata goma, saboda ke ga su wance anji hud'uba ta sai wani tartsin yawu ake mana", tana maganar ne had'e da kallon Salmat tana murmushi. Sanin cewa tsokanar ta ne take yi ya sa ta yi shiru ta k'yale ta sanadiyyar yanzu baki ya mutu ko dogon surutu bata so. Da hakan suka watse suka bar Yusrah had'e da yi mata fatan alkhairi. *** Bayan kwana uku ne da auren Yusrah Alh Ibrahim ya diro garin Jega, direct wayar Dad ya kira kuma akayi sa'a da babu kowa a tare dashi, kuma gashi su Mum basu yi mai bayanin komai ba. Wayar ya d'aga suka gaisa ba tare da yasan waye ba, daga baya Dad ke tambayar shi waye halan saboda bai gane mai magana ba, amsa ya bashi da cewa wani tsohon aminin shi zai kawo mai ziyara, ba tare da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38