Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ni kad'ai gurin mahaifiya ta kuma ita ce ta farko a gare shi, ta biyu keda yara bakwai ta k'arshe kuma yara hud'u. Allah ya yiwa mahaifiya ta rasuwa tun ina da shekara bakwai a duniya sanadiyyar hakan na tashi wulak'ance a gidan wanda dai-dai da abinci sai mak'wabta sun bani ko kuma gidan abokai, da hakan na tashi har na girma ba wani canji na zamantakewa ta a gidan, ana hakan ne ciwon ajali ya kama mahaifin mu sanadiyyar hakan yaga cewa nine babba a cikin yaran shi yasa ya damk'amin duka kaf dukiyar shi a zuwan in rai ya yi halin shi in nemi malamai a raba mana gado, lokacin haukar k'urciya yasa na gudo da kud'in kaf saboda tunani na ta hakan ne zan d'ebe takaicin k'iyayyar da matan mahaifi na da y'an uwa na ke nuna min". "Haka kawai raina ya bani in gudo Jega da zama, da hakan na shigo garin ina y'an sana'o'i na har Allah ya rik'amin wanda daga baya ne muka had'u dakai har mutunci mai k'arfi ya k'ullu, lokacin da abubuwa suka faru har na d'auki dukiya ta duka na baka nabar gari, wani k'anen mahaifi na ne yaji inda nake har ya aiko sau biyu yana nema na, hakan yasa na had'a komai na baka na yanke hukuncin zuwa gari mai nisa don ma kar aji labarin inda nake". "Daga bayan nan ne nake ta mafalkai kan mahaifin mu na takure cikin k'abari yana rok'o na kan in d'auke mai wani k'aton dutse dake saman kanshi, ko in ganshi yana cemin wannan ce amanar da na baka. Da hakan hankali na ya yi mugun tashi kuma naji ina so in je gida sannan in dawo nan in kar6i hakk'in marayi in kai masu". "Abinda yasa na furta ina da sila da abinda ya shafe ku kuwa shine, hakk'in marayu bazai ciyu kuma a zauna lafiya ba, saboda dukiyar kaf banda ko kwabo cikin ta in ba an raba gado bane an bani hakk'i na, saboda haka ina mai baka hak'uri da abubuwan da suka faru". Nan kowannen su ya nisa had'e da jimamin wannan tarihi na Alh Ibrahim, nan aka yi lisafi kan abinda ya bada sai gashi kaf har kud'in gidan Alamein sun shige ciki kuma ana neman k'ari, sanadiyyar kud'in can baya sun fi na yanzun daraja sosai, hak'uri suka bawa Alh Ibrahim kan cewa yabari gobe yadawo za'a had'a kud'in, da hakan ya fice daga gidan. **** Ba k'aramin tausaya masu yayi ba kan k'addarar da ta hau Kansu ba, har ga Allah yana so yataimaka masu, amma yafi so ya raba su da lalura in yaso daga baya ya taimaka masu, saboda tabbas dukiyar maraya cin ta lalura ce, shi kanshi baiji dad'in abinda ya aikata ba, don da ya mutu hakan baisan da wanne ido zai tsayu gaban ubangiji ba, da hakan ya yi alk'awari a ranshi cewa da an raba gado an bashi nashi kaso zai dawo yakawo ma Dad saboda sun yimai halacci a zaman takewa musamman Baban Maryam wato Mum inda ya zamo tamkar mahaifin shi sanadiyyar amintakar shi da Dad. *** 6angaren su Mum kuwa sabon nazari aka shiga ta neman mafita, "gaskiya Dad mutumen nan bai yi halacci ba, yanzu duk zaman takewar da kuka yi bazai iya yafe sauran kud'in da babu ciko ba?". Alamein ke wannan maganar cikin kumfar baki. Murmushi Dad ya yi had'e da girgiza kai sannan ya furta "Son ko da yace ya barmin bazan yarda naci ta ba, musamman yanzu dana san cewa hakk'in marayu ce, yanzu abinda nake so dakai gobe kaje kasa ka motoci na biyu kasuwa, nasan za suyi saurin shiga tunda sabon shiga ne, kabar min d'ayar ta ishe ni lalurar yau da gobe". Baki ya bud'e da niyyar yin magana hannun Dad ya dakatar dashi, "kayi yanda nace kawai", yana maganar yana murmushi, da hakan ya tashi ya koma d'akin shi ya bar su jugum a falon. .......... Washe gari Alamein ya samo mai siyen motocin Dad saboda suna sabon yayi don kaf garin Jega su biyu ke da irin motocin, da hakan aka kammala ma Alh Ibrahim kud'in marayi aka bashi ya wuce da alk'awarin sai sun ganshi. Iya damuwa Mum da Alamein sun shiga wanda ya zamo Dad Allah ya sako mai tawakkalin da basu yi tsammani ba don shi ya zamo mai rarrashi a gare su, (ohhh! Duniya juyi-juyi kwad'o ya fad'a ruwan zafi, abin da mamaki wai liman ya auri karuwa). A cikin ran shi gaba d'aya ji yake yi ya tsani dukiyar shi duk da ya biya hakk'in marayi, sai yana ganin d'an abinda ya yi saura hannun shi tamkar wata k'addarar za ta iya fad'a mai nan gaba. Da hakan dai ya kwantar masu da hankali kowa ya kama gaban shi had'e da tunane-tunanen miye mafita. ***** Bayan kwana uku ne da faruwar wannan lamarin Zajlah na d'aki tana wasu d'inkuna da Shema'u ta kawo mata Alamein ya shigo d'akin wanda ko sallamar shi bata ji ba ganin shi kawai ta yi gaban ta, d'an zabura ta yi alamar razana. "Lallai na tabbatar in kina d'inki ba ki jin motsin mutum, sau uku ina sallama shiru". Gaida shi ta fara yi sannan ta d'ora da cewa "wallahi banji bane", hakan ya samu gefen katifar ta ya zauna ya yi shiru, ganin hakan ita ko ta basar ta cigaba da d'inkin ta. Ido ya zuba mata yana kallon yanda take sarrafa keken d'inkin sannan ya furta "ah ashe k'afa ta yi sauk'i tinda har ana iya d'inki da ita", "eh ai tin ranar ta yi sauk'i". Daga hakan kowannen su ya yi shiru saboda rasa takamemen me za'a fad'a, d'azu ne Salis ya kira yake gaya mai Salmat jiki ya yi tsanani kullum cikin amai da k'arin ruwa take, nan yake jajanta mai had'e da gaya mai za su shigo duba jikin na ta, to shine yanzu yake son gaya mata ta shirya suje amma ya rasa ta ina zai kamo zancen, shine yake ta kame-kame. "In kin k'arasa aikin zuwa bayan azzahar kishirya muje duba jikin Salmat, d'azu Imran ke gayamin bata ji dad'i ba kwana biyu". "To" ta amsa a gajarce ta cigaba da d'inkin ta, hakan ya sa ya ja jiki sum-sum ya fice daga d'akin kamar wani munafuki. Ranar da za suje yiwa Baban ta bankwana kawai ta yi mata sak a rai, "ai ko giyar wake nasha bazan k'ara siyo ma kaina wulak'anci ba, hanyar mota daban ta jirgi daban", hakan ta furta a fili sannan ta yi wani gajeren murmushi na tunawa da message d'in da ya yi mata bata San ya za ta bud'e ba har yaci zalin ta ranar, saboda in har bata manta ba ranar da Salmat da Yusrah suka zo gurin ta har soyayya ta k'ullu tsakanin Salis da Salmat to ranar ne Yusrah ta koya mata yanda ake text message, don ba wai wasik'ar ce bata iya ba a'ah kan wayar ce bata sani ba, wanda sai ranar ta bud'e message d'in da ya turo mata. *** Tana gama girkin tane ta d'iba ta kaiwa Mum, saboda dambun shinkafa tayi Wanda ya ji kayan had'i da zogale, dama in tayi girkin marmari tana

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38