Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

ita gidan, sanin cewa Mum za ta iya ne man shi a waya ya sa ya kashe ta duka. Akan idon shi ta shigo gidan ta ajiye abincin sai da ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya ci abincin ya ko ma d'akin shi. Kwata-kwata bai son abinda zai janyo alak'ar had'uwar su ko da ta second biyu ce, kwance ya yi yana ta tunanin yanda wai kamar shi za'a yi mai auren dole, don bai ga abin so ga Mace ba. Wasu lokuta in har yana tuna lokacin degree d'in shi yanda friends d'in shi ke rud'ewa in suka ga Mace abin har haushi yake bashi over, don ganin yake yi rashin abinyi ke sa ka 6ata lokacin ka ga Mace. In har bai manta ba akwai lokacin da wata Lubna ta mak'ale mai tana bibiyar shi wanda shi ba ta ko gaban shi, ranar ta tarar da shi zaune dasu Imran kawai ta rungumoshi wait gaisuwa ce, marin da ya kifa mata ne ya dawo da hankalin tsirarun mutane dake gurin nan take aka ta mata dariya tun ranar bata k'ara kula shi ba, da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba dashi. (Alamein asuba ta gari inji Jegal, lolx.) * ** ** WASHE GARI Misalin k'arfe 11:00am Mum ta kira Alamein kan cewa ya d'auko Zajlah ya biyo ya d'auke ta su wuce, rasa ina zai saka ran shi ya yi ta yanda zai gaya wa Zajlah ta shirya su wuce d'in, wata dabara ta fad'o mai take ya lalabo lambar ta da Yusrah ta kira shi da ita. Text message ya tura mata kamar haka ( ki fito Mum na jiran mu). . Ta dai ji wayar ta ta yi k'ara kuma ta d'auko taga alamar abu a sama amma bata gane miye ba, saboda bayan saving number da call ba abinda Yusrah ta ko ya mata, asali ma bayan Yusrah da Mum ba wanda ya ta6a kiran ta a waya. Ba sarwa tayi kawai ta fad'a wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa tana zaune saman mirror tana taje kanta aka banko k'ofar d'akin da k'arfi wanda sai da ta razana da sauri ta zabura. Gashin kan ta ya kama da k'arfi ya fizgo cikin rinannun ido yake nuna ta da d'ayan yatsan. "Ke wace irin dak'ik'iya ce da zaki banzatar da ni a mota fiye da minti ashirin?, waye bawan ki ko wa kika ajiye?, kinsan ba don darajar Mum ba wallahi baki yi darajar ko da takalmin Alamein su ta ka wannan k'azamiyar unguwa ta ku ba". Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta ga shi har lokacin yana rik'e da gashin kanta. Wayar shi da Mum ta k'ara kira a karo na uku ya sa ya sake ta had'e da kai mata muguwar harara. Nan ya d'aga kiran had'e da ce mata ga sunan zuwa, cikin tsawa ya ce mata "fice muje banza kawai dak'ik'iya". Hijab d'in ta ta janyo daga saman gadon ta saka suka fice wanda har lokacin hawayen idon ta basu kafe ba. ® . Gaban motar ta je shiga saboda gudun ta zauna baya yace ta mayar dashi direban ta, ashe duk da hakan bata tsira ba harara ya bi ta da ita had'e da furta "baki yi matsayin da zan zauna gaban mota ni da ke ba sai dai ki koma baya, jahilar banza kawai". Sum-sum ta ko ma bayan mota ta takure sai zuciyar ta ce ke mata wani tuk'uk'i. Da hakan har suka iso gidan, Mum ta fito sai dai ta ce dole Zajlah ce za ta shiga gaba ita ko ta zauna baya, akan ta matsa ne ya sa ta fito had'e da durk'usawa ta gaida ita. Tallafo ta ta yi cikin sauri had'e da tallafo ha6ar ta sai ga hawaye shaaa, "me ya same ki Zajlah? Son ne ya 6ata ma ki rai?", duk cikin rud'u take tambayar ta. Kai ta girgiza alamar ba komai, "haba Zajlah yau fa ranar murna ce gare ki za ki je gida kiga iyayen ki, ni da na zata ina fitowa inga bakin ki har kunne kan farin ciki" murmushi ne d'auke a fuskar ta alamar zolaya. Hakan ya saka Zajlah ta d'an murmusa "Mum fa ba komai ina d'auko hijab ne zan saka naji abu ya fad'a man a ido, kuma na duba banga komai ba sai wani zafi da nake ji a cikin idon". Sannu Mum ta mata had'e da saka bakin ta ta bushe mata idon sannan ta rik'a hannun ta ta saka ta gaban motar ta rufe sannan ta shiga baya ta zauna. Unguwar su Zajlah ya nufa wato Birnin yari, ran shi 6ace sai wani cin magani yake yi, har suka isa ba wanda yace uffan har Mum d'in saboda kowa da abinda yake sak'awa a ranshi. Sai dai tunanin Mum har yau babu wani cigaba tsakanin zaman takewar su kawai Zajlah na 6oye mata ne, lallai tabbas yaro man kaza. Da hakan suka iso gidan inda Zajlah bata ko jira su ba ta fad'a gidan su Salmat, Mama Inno ta tarar zaune tsakar gida tana gyaran wake, saman ta ta fad'a tana razgar kuka wanda ya sa ta kayar mata da gaba. *** A can 6angaren Alamein kuwa Mum na fitowa daga motar ya je zuwa juya akalar motar shi ya koma gida Mum ta bishi da harara. "In ita gidan za ta wuni sai aka ce ma ni ma nan zan wuni?, wato ka fi k'arfin ka fito mu shiga ka gaisa da mahaifan yarinyar nan ko?, wai kai sai yaushe ne za kayi karatun ta nutsu a rayuwar ka?". Cikin 6acin rai ta kama hanyar shiga gidan ta bar shi, dole ba don yana so ba ya rufe motar ya mara mata baya da handkerchief saman hancin shi yana yatsinar fuska tamkar Wanda ya shigo cikin jeji. *** Mama Inno ta tallafo ta had'e da jera mata tambayoyin meke faruwa wanda amsa tak'i fitowa sai dai ambaliyar hawaye. Suna hakan ne sai ga Mum ta shigo gidan da sallamar ta had'e da murmushi a fuskar ta, hakan ya sa Zajlah ta fad'a d'aki. Shimfid'a Mama Inno ta yi masu had'e da yi masu kyakkywar tarba cikin fara'a da sakin fuska, Mum ta furta "kin ga y'ar tawa da sangarta muna kawowa k'ofar gida tana fasa kuka, ita da ya kama ta yau ta zamo cikin walwala baki har kunne", cikin zolaya Mum ke furta maganar. "Yo ai kad'an kenan daga aikin Zajlah, ba dai shagwa6a ba har dai in tana gaban Baban ta". D'agowar da Mum za tayi ta ganshi k'erere saman kan ta, muguwar hararar da ta zabga mai ya sa ya janye handkerchief d'in da ya toshe hanci dashi, sannan ya d'osa na gefen ta ya zauna tamkar mai tsoron zama saman allura. "Mu shiga can wurin Mal Abu d'in?". Maganar tace ta dawo dasu hayyacin su su duka biyun. D'aki ta shiga ta d'auko hijab had'e da sako Zajlah gaba suka shiga gidan na su. Nan aka gaggaisa inda suka tarar Baban ta bainan yana gurin Sana'ar shi ta kayan gwari, Mama Inno ce ta fita ta samu yaro don yakiro su Mal Abu. Cikin minti goma sai gashi sun iso, nan dai aka

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38