Chapter 13
Chapter 13
tunda an kawo komai na amfani a store. . Suna cikin girkin ne Alamein ya fito daga part d'in shi ya yi waje sai ga shi ya dawo falon had'e da Imran da Salis, sai wani dake aiki company dayace zai zo taya shi murna. Falon suka zube dukan su inda Saudat ta gayar dasu ta cigaba da latsar wayar ta. A tare suka fito daga kitchen d'in ita da Yusrah, gyalen ta ta k'ara janyowa ta rufe jikin ta saboda wannan shi ne karo na farko da Maza za su ganta ba hijab a jikin ta, har k'asa ta durk'usa ta gaida su had'e da yi masu sannu da zuwa, nan suka amsa cikin sakin fuska da walwala. Part d'in shi Yusrah ta wuce ta kawo masu ruwa da lemu, itako Zajlah ta koma kitchen domin k'arashe aikin. "Tabbb da sallamo wata k'anshin girki yadoki hanci na sannan a kawo min ruwa da lemu, kawai abari in na yi lunch na danne da ruwan", Salis kenan sarkin barkwanci. Hakan suka kwashi dariya duka falon sa6anin Alamein dake wani cin magani. Abincin suka jera ma su Imran a falon bayan sun gama, suka wuce da na su part d'in Zajlah saboda ta gayawa Yusrah ba za ta iya cin abinci gaban Mazan ba saboda bata saba ba. Ba k'aramin dad'i Alamein ya ji ba da suka wuce part d'in ta, saboda a tunanin shi in har zai cigaba da ganin ta falon zuciyar shi za ta iya tashi ya kasa cin abincin, don ko yanzu zai ci ne saboda tabbacin ba ita tayi girkin ba Yusrah ce. Bayan sun gama cin abinci ne har da santin su suka tashi za su wuce, su Zajlah ne suka fito domin suyi sai an jima nan sukayi godiya suka ba ta kud'i wanda ta kasa kar6a saida Yusrah ta kar6a suka yi masu fatan alkhairi da d'orewar zaman lafiya. Saudat ce ta ce su sauke ta gida ita ta gaji da zaman gidan, shi ma Alamein makulin mota ya d'auko domin suje tare tunda sun ce za su biya su gaida Dad. "Ai kai mun yanke ma fita har company sai nan da wata d'aya", inji Imran. "Saboda ga mai laifi an yanke mai hukuncin gidan yari ba", cewar Alamein. Dariya sukayi sosai sannan suka fice daga gidan har Saudat d'in, akabar Yusrah da tace sai marece za ta koma, wanda hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Zajlah ba. , Hira suka shiga yi sosai ita da Yusrah, saboda gaskiya yarinyar ta yi mata ba tada girman kai irin na masu kud'i, kuma ga alama za ta girme ta kad'an. Tunani take tayi a ranta kan ta tambayi Yusrah asalin ya auren su yake ko kuma ta k'yale ta, saboda gaskiya har ga Allah abin na damun ta sosai. Bayan sun yi sallar La'asar ne suka shiga kitchen domin girkin dare, duk da tana tunanin mawuyacin abu ne yaci abincin ta don tana tunanin k'ila ko d'azun bai ci ba. "Me ya kama ta mu girka abincin dare?". Maganar ce ta dawo da ita daga hayyacin ta, ta kai duban ta zuwa gare ta ta sauke ajiyar zuciya. "Me kike ganin yayan ku ya fi ra'ayi da dare d'in?, duk da ban tunanin in ya shigo zai ci abincin". "Ko da wasa kar kiyi tunanin tunda ba shi yagan ki yace yana So ba za ki rage shi da wani abu na kyautata wa, a tunani na ta hakan ne za ki janyo hankalin shi zuwa gare ki". "Nasan ce wa watarana Brother zai yi alfahari da auren ki ADALILIN GATAN da Mum tayi mai. Saboda har kullum in dai namiji zai jure ya auri Mace ma'abuciyar ilmin addini to tabbas babu shi babu dana sani, yanda tarbiyar yara ke ta6ar6arewa yanzu ka samu mai d'ora yaran ka akan hanya ma abin alfahari ne". "Amma yanzu abinda mutane basu gane wa musamman Maza har kullum burin su shi ne su auri Mace wayayya kuma y'ar boko, basu san ce wa da wayewar waje k'ara ta gida ba". . "Nasan matsalar Brother mai sauk'i ce, saboda shi kwata-kwata matan ne basu burge shi, asali ma ko taro ake yi muddin akwai Mata gurin bazai halarci taron ba, ni kai na da nake k'anwar shi ta jini sai shekaranjia ne Mum ta matsa mai ya kar6i lamba ta, kin ga ko irin shi bazai yi wuyar shawo kai ba tun da idon shi basu bud'e da soyayyar kowace Mace ba". "Saboda haka ki dage ki janyo hankalin mijin ki, in zama ya yi dad'i za ku dace sosai da Brother, kar ki biyewa zugar k'awaye". Hakan dai ta yi ta tsara mata irin abubuwan da ya dace tayi da way'anda basu dace ba har suka k'are girkin. Zajlah ta kai duban ta zuwa ga Yusrah had'e da furta. "Ni yanzu abu d'aya nake so ki samo min customers na d'inki tunda kin ga ba karatu nake yi ba sai dai zaman gida". "Ba yanzu ba kam sai an gama kula da yaya na sannan, kuma ai ni ban tabbatar kin iya d'inki ba, kar in kwaso atamfofin k'awaye na ki yanka ba dai-dai ba Brother ko ya biya su", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Ke dai ki samo za kiyi mamaki". Da hakan suka kammala ayukkan had'e da kimtsa gida sannan Yusrah ta yi haramar wuce wa, leda ta cika mata da kayan sha fa cikin na lefen ta, kuma ta had'a mata da dubu biyu cikin kud'in da su Salis suka ba ta, dak'yar ta karb'i kayan tayi mata godiya. * * * * Alamein na shigowa gidan ko takan abincin bai bi ya wuce part d'in shi, duk da kamin ya fito daga gidan Mum ta yi mai nasiha dai-dai gwargwado kan kula da hakk'in yarinyar mutane wanda ya nuna mata zai yi insha Allah. Sa6anin yanzu yana doso gidan ya ji gaba d'aya ranshi duk ya 6aci shiyasa ya k'i kula abincin ya wuce kawai. Kuma dama bai saba da cin abincin kowa ba sai na Mum, don ko yanzu sai da ya sa Saudat ta d'ebo mai abinci ya ci sannan ya fito. * * * Tana jin shigowar shi tana part d'in ta wata zuciya ke ce mata ta fita tayi mai barka da dawo wa, wata na ce mata kar kije ya maki wulak'anci. Gaskiya ba k'aramin fad'uwa gaban ta ke yi ba akan irin muguwar hararar da yake zabga mata. Da hakan ta yanke shawarar zaman ta d'akin ta, wanka ta yo had'e da alwala ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi addu'o'in ta sannan ta kwanta duk da irin tsoron da take ji. Tunani kawai take yi anya za ta iya biyar shawarar Yusrah kuwa?, saboda a tunanin ta ko kyautata wa mutum na tafiya ne da samun fuska, kawai dai ta yanke ma kanta in har ta ga fuska za taci gaba da kyauta ta mai, da hakan 6arawo bacci ya yi awon gaba da ita. . Yau ta kama Alhamis dai-dai da kwanan ta biyar kenan a gidan Alamein, wanda sai ta wuni ta kwana basu had'u dashi ba, kuma har ko yaushe ta yi girki za ta ajiye mai sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38