Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

kaiwa su Mum, nan take gaya mata za taje ganin Salmat bata jin dad'i hakan ya sa Saudat tace tana zuwa suka fice tare, saman titi suka samu napep suka wuce. *** 6angaren Alamein kuwa har ya dawo daga masallaci ya yi wanka ya kimtsa bai ji motsin Zajlah ba, hakan ta sa ya je d'akin ta, amma ga mamakin shi yana murd'a k'ofar ya jita rufe. Part d'in Mum ya wuce bayan sun gaisa yake ce mata ina Saudat halan?, amsa ta bashi da cewa ta raka Zajlah gidan Salmat, hakan ya ja motar shi ya wuce mamaki fal ranshi, amma kuma yasan wani 6angare tana shakkar fita dashi ne saboda gudun wasu abubuwan, amma duk zille-zillen ta bazai bari ta dawo a napep ba. **** Shigar su gidan kenan ana cire mata k'arin ruwan da aka saka mata, nan suka mata sannu suka zube a falon, wanka ta shiga ta fito duk ta jeme kan laulayi, dambun da Zajlah ta zo mata dashi ne ta saka mata, kad'an ta ci taji zuciyar ta na tashi ta ajiye, duk tsiyar da Zajlah ta so yi mata ta rushe saboda ta tausaya mata ganin yanda ciki ya mayar da ita gwanin tausayi. Suna zaune suka ji shigowar Salis da Alamein, a falon suka zube duka, "lahhhh Brother za ka ma zo baka gaya mana mu jira kaba?", fad'ar Saudat. Ido ya bi Zajlah dashi suna had'awa ta nok'e kai. Alamein ne ya yiwa Salmat ya jiki had'e da mamakin yanda bakin ta na tsiwa ya mutu. Sai bayan la'asar ne Imran ya kawo Yusrah, nan suka baje ana ta hira inda mazan suka fita. Bayan isha'i ne suka shigo gidan su uku, abinci suka ci sannan kowa ya yi haramar zuwa gida, inda Alamein ya kasa ya tsare wanda ya sa dole Zajlah ta bishi ita da Saudat suka koma gida ba don taso hakan ba. ......... Awanni sun wuce kwanaki sun wuce wanda abubuwa da dama sun faru, su Mum an fara shiga rayuwar k'unci komai sai manage, da hakan aka sallami duka y'an aikin gidan saboda zaman su na k'arin wasu abubuwa Mama Talatu kawai aka bari. *** Yanzu ne take ganin ya dace ta taimaka ma Alamein saboda ko mota babu hannun shi, abincin gidan kanshi ya sauya, saboda ga nasu yanayin kuma ga yanayin k'asa wanda ya shafi kowa, duk inda ka zaga za kaga gidan da aka saba tafiyar da abubuwa 80% yanzu sun dawo 40% saboda yanayin k'asa, abin kawai sai addu'a. **** Bayan sun karya ne ta Shiga gyara d'akin Alamein kamar kullum, zaune ta isko shi saman kujera ya yi zugum ya saka takardu gaban shi ga alama yana cikin damuwa. Nan ta gaida shi ta wuce ta fara gyara k'uryar d'akin, ko da ta fito falon yanda ta barshi hakan ta tarar dashi, guri ta samu ta zauna sannan ta tattara dukan nutsuwar ta guri d'aya sannan ta jefo mai magana kamar haka, "meke damun ka haka?, bai dace ka saka ma ranka damuwa ba, kar ka janyo wani ciwo na daban". Hankalin shi ya maida zuwa gare ta had'e da cewa "ya zanyi da raina kusan sati d'aya ina yawon neman aiki ban samu ba, kuma gashi takardu na sun yi kyau amma abu ya gagara". "A tunani na me zai hana a ajiye neman aiki gefe d'aya a kama kasuwanci?, kana ganin yanda k'asar ta zama yanzu, way'anda ke saman ma tsige su ake saboda bincike ina aka ga damar d'aukar wasu ma'aikatan?". Zurum ya yi baice komai ba saboda tuna lokacin da ya kori wani daga ma'aikatar su akan bada shawara kan cigaban su, inda ya tuna lokacin da yake neman yafiya gare shi kan yabar shi ga aikin shi wanda ko sauraren shi bai yi ba ya wuce, hakan ya sa ya ji tausayin kanshi da kan shi kan yanayin da yake ciki sai ga hawaye shaaaaa. Ba k'aramin rud'ani ta Shiga ba ganin yanda hawaye ke ambaliya a fuskar shi, zumbur ta mik'e ta koma d'akin ta sai gashi ta dawo da wata leda bak'a a hannun ta har lokacin hawaye yake yi, gaban shi ta je ta durk'usa had'e da mik'a mai ledar, handkerchief dake hannun shi ta kar6a tana shafe mai hawayen dake ambaliya a fuskar shi, saboda Zajlah akwai raunin zuciya. Ledar ya kar6a ya bud'e, abinda ya gani ne ya sa ya tayar da kanshi cikin mamaki yana mai kallon ta, bud'e baki yayi zai yi magana ta yi mai alamar yayi shiru, nan ta d'ora da cewa "kayi shawarar wace Sana'a ce ta dace dakai, na baka su halak malak". Sakin bakin da Alamein ya yi yana kallon Zajlah ne har ta 6ace ma ganin shi ya sa na lek'a ledar na hango kud'i, wanda duk iya biyar kwakkwafi na na d'aukar rahoto naso insan ko nawa ne don in feso maku amma abin ya gagara. Ledar ya k'ara lek'awa had'e da murza idon shi don tabbatar da abinda yake gani cikin ta, hawayen idon shine suka k'aru sai kuka yake yi tamkar wani yaro. Kud'in ya d'auko ya nufi part d'in Mum ya tarar tana d'akin Dad, nan ya shiga da sallamar shi suka amsa sannan ya shiga, kud'in ya ajiye gaban su had'e da yi masu bayanin inda kud'in suka fito, dukan su baki suka sake suna masu tarabbabin yanda matar shi ta zamo mai halarci a gare shi duk da irin cin fuskan da ya rik'a yi mata. "Je ka kiramin matar taka", cewar Dad. Mum ce ta mik'e tana mai cewa bara ta kira ta da kanta, da hakan ta fice har part d'insu ta sako Zajlah gaba, wanda har ga Allah bata so yagayawa iyayen shi wannan abin ba, ta so yabar shi tsakanin su. Cikin jin kunya ta shiga falon ta nemi guri ta zauna tana mai gayar da Dad had'e da yimai ya jikin kanta na nok'e k'asa. Gyaran murya Dad ya yi bayan ya kar6a mata sannan ya furta "na ga alkhairin da kika yiwa Son, muna masu taya shi godiya, amma zan so ki gayamin ta wacce hanya kika samu wad'annan kud'in?". Nan ta yimai bayani kan cewa kayan d'akin ta ta saida sai kuma na d'inkin da take yi ana biyan ta. "Ai ko bai dace ki sai da kayan d'akin ki ba, da ki bari ak'ara duba abinda ya dace don har ina shawarar saka mota ta kasuwa musan abinyi". "Dad wallahi babu komai, a dai saka mana albarka a cikin abinda za'a fara dasu", daga hakan ta tashi sum-sum ta koma falon Mum. Kowan nen su ya yi jugum saboda gaba d'aya ta kashe masu jiki, don basu ta6a tunanin hakan daga yarinyar ba, nan dai suka tattauna abinda ya dace Alamein ya yi da kud'in. (Ni dai Jegal na yita baza kunne inji ko za su fad'i adadin kud'in da Zajlah ta bawa Alamein amma shiru abin tamkar had'in baki, don na hango su Hindatu shehu da Fati Salihu ana baza kunne, lolx). ......... Sana'a ya fara gadan-gadan inda ya shawarci Dad kan yayi zaman shi ya huta shi zai tashi da nema yanzu. Duk inda yake yanzu da tunanin ta had'e da muradin sauraren muryar ta yake,

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38