Chapter 35
Chapter 35
nasan ni mai laifi ne a gare ki, amma na yi ta baki hak'uri kin k'i ki hak'ura". "Tun farko wallahi bansan miye "So" ba ban ta6a tsayawa na yi magana da mace ta minti uku ba, a wancan lokacin na saka ma raina tsanar mace ne ba akan komai ba sai don ganin yanda suke taka rawa a ta6ar6arewar rayuwar d'a namiji cikin shu'uman cin su". "Bazan manta ba muna farkon shiga university mu hud'u muke tare, Salis, Imran, Salim sai ni Alamein, duk wanda ya san mu tare yake ganin mu, bamu shiga sabgar kowa karatun mu kawai muka saka ma gaba. Akwana a tashi Salim ya had'u da wata yarinya da ake cema Hafsat inda soyayya ta shiga tsakanin su, ganin rayuwar shi ta fara sauyawa muka nemi raba shi da ita saboda ya kula da karatun shi gashi maraya amma abin ya gagara, saboda y'ar mai kud'i ce yarinyar kuma gwargwado tana sakar mai kud'i, daga hakan ta ja ra'ayin shi suka rik'a holewa har ya zamo tamkar miji a gare ta, hakan ya yi silar muka tsame kan mu daga lamurran shi, wallahi tun daga lokacin na k'ara tsanar Mace a rayuwa ta". "Tabbas nasan ina da tak'ama da ji da kai, amma ba na saka Mace a tsarin rayuwa ta kwata-kwata, kuma kiyar da dacewa kece first love d'ita kuma last insha Allah, wannan horon da kike yimin ya yi tsanani don Allah ki sassauta min", hakan ya k'arashe maganar yana rik'e da hannun ta har da guntun hawayen shi. Tabbas ta tausaya mai, amma ita miye na ta ciki na hantara da hwulak'antarwa, tunda ita ma ba ita tace tana son shi ba, kawai daga sama akace an mata miji, me zai hana yayi wa iyayen shi biyayya ko da bai son ta ya shafa mata lafiya kowa tashi ta fisshe shi. Yatsun hannun tane da yake murza wa ya sa ta fincike hannun ta ta mik'e ta yi d'aki, key ta murd'a ta yi zaman ta d'akin. Har ga Allah tasan tana son Alamein kuma shine kalar namijin da take so tun bata san miye "So" ba tsayayyen namiji ke burge ta, sajen fuskar shi da dara-daran idon shi ke k'ara d'aukar hankalin ta zuwa gare shi, amma tabbas sai ta nuna mai darasi sannan za ta bada kai bori ya hau. Tsam ya tashi ya yi part d'in Mum, saman kujera ya zube ya yi kwance hannun shi d'aya ya yi matashi dashi d'ayan kuma ya dafe kanshi inda har jiyojin kanshi sun tashi rad'o-rad'o. Mum ce ta fito daga d'akin Dad ta risk'e shi hakan, tafi minti uku saman kanshi bai ma san tana nan ba. Tabbas kwanan nan tana lura da takon shi tsakanin shi da Zajlah, tasan ba komai ne ke wahalar da shi ba sai "Son" Zajlah dake d'awainiya dashi, saboda yanda yarinyar ta k'ara fresh yanzu ga wayewa dake shigo mata kad'an-kad'an, inda ko Mace y'ar uwar ta ta ganta cikin kwalliya sai ta k'ara kallon ta barranta na namiji, da hakan ta yi alk'awari ba za ta ta6a nuna mai ta fahimci matsalar shi ba, sai Zajlah ta gama gara shi ta sauko don kanta. Hannun shi da ya rufe fuskar sa dashi Mum ta janye had'e da furta "waini Son kwanan nan me ke damun ka?, duk sai in ganka tamkar kana cikin damuwa, ko gurin kasuwancin ne?". Ji ya yi tamkar ya gaya mata me ke faruwa ko za ta taya shi shawo kan Zajlah, sai dai kuma yana tunanin ko ya gayawa Mum ba lallai ne ta bashi had'in kai ba, tana ma iya basarwa da tuna mai baya. "Ba komai Mum yanayin rayuwa ne kawai, a dai taya mu da addu'a", "toh Allah yashige mana gaba, kaima ka dage da addu'a". Bayan ya amsa ne ya ji kuma zaman ya gundire shi ya tashi ya yi part d'in su, wanda har lokacin Zajlah na d'aki bata fito ba. D'ayan d'akin ya fad'a ya shiga toilet ya sakarwa kanshi ruwa, sai da ya yi wanka ya fito ba kayan sakawa suna d'akin da Zajlah take, k'ofar yaje yana bugawa had'e da magiyar ta bud'e zai d'auki kayan shi, hakan ya sa ta fito ta bar mai d'akin ta dawo falo. ................ Duk mahaluk'in da ya ga Alamein yasan cewa yana cikin damuwa, saboda har y'ar rama ya yi kuma ya tara wani uban saje a fuskar shi da ya maida shi tamkar wani Sabon shigar hauka. Ba k'aramin tausaya mai Mum ke yi ba sai dai kuma tana ganin in har tace za ta saka baki a maganar su tamkar ta so kanta dayawa, kuma in za ta duba bata San iya muzguna warda ya yi yiwa ita Zajlan ba har aka kawo yanzu, kuma a 6angare d'aya ta fi so Zajlah ta garashi saboda yasan darajar ta. Abincin rana ta gama ta kawo ta ajiye, amma ga mamakin ta yanda ta ajiye na safe hakan ta tarar da shi, mamaki ne fal a ranta saboda yanzu suna wasar y'ar 6uya tsakanin su in yana d'ayan d'akin to itako za ta koma d'ayan. D'akin da yake ta tunkara, har ta rik'a k'ofa za ta murd'a kuma ta fasa, saboda a tunanin ta in tayi hakan ta bada kanta, sai kawai ta dake ta koma d'ayan d'akin ta yi kwanciyar ta, whatsap ta hau amma duk da hakan zuciyar ta tak'i natsuwa guri d'aya, hankalin ta d'ayan na gurin me yasa yau bata ga Alamein ba. *** A daddafe ta kai la'asar bayan ta yi sallah ta fito domin d'ora girkin dare, still duka abincin ba abinda aka ta6a, cikin rawar jiki ta fad'a d'akin, can k'asa gurin gado ta ganshi zube male-male cikin amai yana dafe da cikin shi, da saurin ta ta kai gurin ta tallafo shi duk jikin shi ya saki. Toilet ta nufa domin samo ruwa da towel ta gyara mai jikin shi amma ya rik'e ta gam ya hana mata tashi, "Zajlah ki yafe min laifi na zuwa gare ki, inason kisan cewa ko da ta Allah ta kasance a gare ni to na tafi da d'inbin K'aunar ki a zuciya ta, ina sonki kuma bazan daina son ki ba har k'arshen rayuwa ta". Wani tari ya rik'a yi mai had'e da majina da jini-jini daga hakan ya some a jikin ta. Wata k'ara ta saki ta fito a guje sai part d'in su Mum, koda ta shiga tana zaune falo da remote a hannun ta tana kallon tashar Manara T.V. jin kawai ta yi mutum ya fad'o mata, "wayyo Mum Alamein ya mutu, Mum ki tausayamin kar in rasa shi, Mum ki gaya mai wallahi ina son shi nima". Sambatu kawai take saki wanda ta kasa yiwa Mum takamemen bayani kan abinda ke faruwa. Remote d'in ta ajiye ta ja hannun ta suka koma part d'in, ko Mum data ganshi a hakan ba k'aramar razana tayi ba, saboda har ga Allah ta zata bashi da rai. Da saurin ta ta doshi gurin ta tallafo shi, inda Zajlah ke ta shar6ar kuka tana gunza, "yi sauri bani ruwa a cup". Fridge ta bud'e ta d'auko ruwa ta bawa Mum ta koma gefe ta raku6e sai gaban tane ke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38