Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,189 words 0 views Progress saved
Download Book

gaisa suka yi mai Allah sanya alkhairi da fatar zuwa lafiya adawo lafiya. Dubu ashirin Mum ta ajiye sannan ta yiwa Alamein alama da ido yaba da nashi, hannu ya saka gaban rigar shi ya kwaso kud'in da shi kanshi baisan nawa ne ba ya ajiye, saboda a matse yake da subar gidan. Shi ya fara ficewa sannan Mum ta kai duban ta ga Mama Asabe tace' "ga y'ata nan ku kulamin da ita zuwa dare Son zai dawo yaje da ita", cikin jin dad'in irin kulawar da Mum ke bata Mama Inno ta furta "za ki samu y'arki lafiya in ma murnar ganin Baban ta baisa ta k'ara k'iba ba". "Ai ko in hakan ta kasance zanfi kowa murna da farin ciki". Da hakan dai suna ta walwala Zajlah ta raka Mum har gurin mota sannan ta dawo gidan. "Zo nan Zajlah inga me ke damun ki, na ga idon ki sun kumbura". Kusa dashi taje ta lafe tana wani zuba shagwa6a. Mama Inno ce ta kar6e da cewa "wacce ta shigo da kuka gidan har ta kayar min da gaba, ashe duk tsabar shagwa6ar zuwa gida ce", nan dai suka ta tsokanar ta ita ko sauraren su kawai take yi. ** *** 6angaren Alamein kuwa har suka kai gida fad'a Mum take mai kan abubuwan da yake yi marar dacewa musamman ga sirikan sa, tun tana fad'an har ta dawo rarrashi tana mai nuna mai irin yanda Zajlah ke mutun ta ta bai dace ya wulak'an ta na ta iyayen ba. Zurum ya yi yana sauraren ta tamkar mai d'aukar darasi, (ni dai Jegal na ce Allah yasa maganar Mum ta shiga kunnen ka Alamein). . Lokacin Salmat ta dawo daga islamiya saboda yanzu ta daina zuwa ta marece da safe zuwa la'asar take dawowa gida. Tana shiga gidan ta ci karo da Zajlah je kaga murna tsakanin su tamkar sun dad'e basu had'u ba, d'aki suka fad'a aka bud'e shafin hira. Bayan sun gaisa ne Salmat ke ce mata "ina gadararren mijin ki?, ina fatar kin fara gyara mai zama yanzu?". . "Hmm! Bari ke dai Allah ya had'a ni da miji marar tausayi, ai ni wannan auren nan kallon auren k'addara nake yi mai", nan dai ta kwashe yanda zaman su yake da yanda ya yi mata d'azun ta gaya mata. "Tabbb sai kika tsaya kallon shi gashin ki ya zamo linzami agare shi, wai ke wace irin Mace ce?, ni fa in mutum ya siyi mutunci wallahi zan nuna mai nice na raini mutuncin har ya girma, sa6anin ka nuna min rashin mutunci in nuna ma cikin shi nayi na haife shi". "Salmat ya kike so na yi ne?, wallahi ko Mum ban iya gaya wa irin zaman da muke yi dashi, nasan komai yayi farko zaiyi k'arshe watarana sai labari". "Lallai ko yarinya za ki zama goro ko abin saye, tunda kin za6i siyar da farin cikin ki ga wanda bai san darajar d'an Adam ba". "Ko dai ba za ki rama abinda yake maki ba to kiyiwa kanki gatan rashin d'aukar raini, saboda in kince ba za ki motsa to kin zama shara kenan duk abinda ya d'auko zai sauke shi saman kan ki". "Ni fa kinsan ko Mace y'ar uwa ta ban iya sa'insa da ita bare namiji, don haka kawai ki taya ni addu'a ita ce kawai mafita gare ni". "To Allah ya kyauta kuma ya dasawa Alamein bala'in son ki a ranshi". Suna had'a ido ta yi mata gwalo tana dariyar k'eta. Da hakan dai suka rik'a hira wanda Salmat ta so ta lurar da Zajlah muhimmancin k'watar y'ancin ta ga Alamein amma abin ya ci tura. D'inkin da aka ba ta na ashobe ta kwaso kusan turmi goma sha biyu ta jibge ma Zajlah had'e da furta "ga d'inki nan kije dasu kiyi ko za ki rage nisan gadin gida, gobe nake so in ba Sagiru su ya kai maki ki ragen aiki". "Zan dai d'auki goma inje dasu, sauran kuma kya k'arasa tun da ke kika yi had'ama kika kar6i kayan mutane". "Yi hak'uri matar Alamein, uwargida kuma amarya daga ke babu k'ari". Share ta kawai ta yi ta fad'a kitchen domin kama ma Mama Asabe girkin dare, ita ko ta fice gida tana mata dariyar shak'iyan ci. * * * * Babu abinda yake tunawa ran shi yayi mugun 6aci sai tunanin komawa d'auko waccan kucakar yarinyar da Mum ta mak'ala mai. Tabbas ba abinda Mum za ta sa shi ya kasa yi mata, kuma yaji fad'an da tayi mai d'azu sai dai ranshi ke 6aci ko yarinyar ya tuna da ita. Murmushi yayi sosai saboda samun mafitar ba sai ya je d'aukar Zajlah ba kuma abinda zai yi Mum ba za ta ta6a sani ba. * * * Kud'i Zajlah ta fitar dubu goma ta bawa mahaifin ta inda dak'yar ta samu ya kar6i kud'in, a cewar shi na mijin ta da Mum sun isa, duk da hakan sai da ya tambaye ta inda ta samu kud'i. "Baba abokanen shi suka bani dubu ashirin cikin su na ba ka goma na ajiye sauran saika dawo in yima dafuwa". Murmushi ya yi dajin dad'in yanda take kula dashi tun bata kai hakan ba. *** *09:00pm Aka aiko daga waje wai anzo d'aukar Zajlah, kayan ta ta had'a hadda d'unkunan da Salmat ta jona mata, har da guntun hawayen ta na rabuwa da Baban ta. Salmat ce ta d'auko mata kayan ta domin ta taka mata daga nan ta wuce gidan su, da biyu ta yi rakiyar saboda tana so Alamein ya yiwa y'ar uwarta ba dai-dai ba a gaban ta tayi mai tasss, sai dai sa6anin hakan suna fita suka ganshi jingine ga mota da fara'ar shi kamar kullum. "Ustaziya barka da fitowa", Salis kenan yaro mai kamala da ganin mutuncin manya. Nan suka gaisa har yasa Zajlah ta kira mai Baban ta su gaisa, ko da ta dawo hira ta 6arke tsakanin shi da Salmat domin hali ya zo d'aya kowa akun kanshi ne gurin surutu. Har k'asa ya durk'usa ya gaida Baba had'e da yimai fatar alkhairi, shi ma kan shi kud'i ya ba Baban suna ta yimai godiya. Mota ya bud'e mata ta shiga ya kai duban shi ga Salmat "to sai na ganki alhamis d'in banda karya alk'awari". Cikin jin kunya Salmat ta shige gidan, shi ko ya shiga motar ya ja suka fice. Mamaki ne fal a ranta, lallai ta tabbatar da Alamein bai san darajar aure ba, wato ya fi k'arfin yazo d'aukar ta sai dai yaturo abokin shi, irin haka ne shaid'an ke samun kutsawa zuk'atan masu raunin imani sai daga baya azo ana fad'in wane da matar abokin shi yake mu'amala alhali abokin ne ya bashi wannan damar. (Allah ka tsalkake mana zuk'atan mu ka k'ara mana k'arfin imani, kasa mufi k'arfin zuk'atan mu). . Har suka kai gida ba wanda yace da wani uffan, kowa da abinda yake sak'a wa a ranshi, fitowa tayi daga motar bayan maigadi ya bud'e masu gate sun shiga godiya ta yi mai sannan ta nufi hanyar shiga falon da kayan ta Salis ya rik'o mata wasu. A falon suka tarar da shi zaune yana kallo yana latsar waya, part d'in ta ta

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38