Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

maku bazan saka baki na a wannan auren ba har sai na ga cewa Son ya sauko yana walwala kamar kowa". "Yo ko yanzun ce ma akayi baya son maganar?, ni fa na rasa gane wane irin mutum ne kai, don Allah kayi hak'uri ka saka ma wannan auren albarka". Dak'yar da lallami ta samu ta shawo kanshi ya sauko har suna tattaunawa kan abubuwan da suka dace ayi na auren. *** Akwana a tashi wataran jariri ango ne, yau dai ga shi har ansaka Zajlah a lalle duk wani abu da za'a yi na al'ada 6angaren amarya da ango duk anyi, inda a 6angare d'aya Amarya tasha gyara daga wata shuwa dasu Mama Asabe suka d'auko musamman domin wannan rana. Yau ce ranar da za'a yi walimar Amarya a makarantar su, inda ba k'aramin jurewa Ustaz Lukman ya yi ba cikin Maluman da suka gabatarda walimar. Amarya tasha nasihohi sosai ga Malaman ta sai dai fatar d'orewar zaman lafiya ita da angon ta. "Yanzu Yusrah duba kiga wai wannan yarinyar ce Brother zai aure, da ace auren da yake so ne da events da za'a sai mun ture". "Ai ko hakan ba laifi, don ni dai abin ya burge ni sosai har ina tunanin in aure na ya tashi ni ma irin wannan walimar za'a yiman". "Ni kam wallahi ranar aure na sai an gwangwaje bazan yi irin wannan ba, kinga har Mum ta biye wannan abin wai ita ma za tayi liyafa gobe". "Ke inda Dad na son wannan auren ai wallahi da yanzu gari ya d'auka tun ana saura wata d'aya auren, amma duba yanzu wai gobe d'aurin aure amma abu shiru tamkar mutuwar sarkin gari". Dariya sosai Yusrah ta yi tana mamakin wannan ak'idar ta Saudat na k'yamar talaka, ta san da ace Zajlah masu kud'i ne to da duk yanda suka tsara abin ba za ta kushe ba. "Mu wuce gida Yusrah tun da an k'are". Maganar Saudat ce ta dawo da ita hayyacin ta. "Kibari mutane su rage sai mu gaisa da amaryar sannan mu wuce, kin ga yanzu jama'a sun mata yawa". "Don Allah ki wuce muje, ai dai tasan ba za'a rasa zuwa daga dangin Angon ba kuma munzo buk'ata ta biya ai shikenan". "Miye amfanin kiran sallar kurma?", ce war Yusrah. "Ban fa fahimce ki ba, ke sai ki rik'a je fawa mutum magana a dunk'ule". "Ke kuma ga ki ba cikakkar bahausa ba, to ina nufin miye fa'idar mu zo bamu gaisa da Amarya ba mu fice". "To ni dai ba don ta na zo ba, saboda yaya na nazo kuma babu lallai sai na tsaya". "Yo ai duk d'aya an cewa shege marar uba". Maganganun na Yusrah suka ishe ta ya sa taja bakin ta ta tsuke, ba don ta so ba ta tsaya har mutane suka rage sannan suka k'arasa gurin ta, cikin yatsinar fuska Saudat ke kallon su da d'ai d'aya sun sha manyan hijabayyen su har k'asa. "Kyawon zaman takewa ka samu abinda yada ce dakai, amma wasu da ka gansu kasan abin sai maneji". "D'an hakin da ka raina shi ke tsokane ma ido, kuma mutunci siyen shi ake yi ba shi ke kai tallan kanshi ba, mai hikima shi ke tauna magana kamin ya watso ta, wani ko maganar ke neman mak'alewa domin ya suturta ta shiko yana k'ok'arin hankad'o ta". Cikin muzan ta Saudat ta bi Salmat da kallo had'e da mamakin kalaman da ta feso mata tamkar dafin maciji. Yusrah ce ta tsaya suka yi gaisuwar mutunci har suna ta6a hira tsakanin su, daga nan suka fice su kuma suka shiga napep sai gida. . Yaune ranar Assabar misalin k'arfe 12:00 dubban jama'a suka shaida auren. AL'AMEIN KABEER AL'AMEIN (A.K.A) DA ZAJLAH ABUBAKAR ZUBAIR (ZAZ) Wanda ya samu halartar manyan bak'i daga gurare da dama duk da ba hakan Dad ya soba, musamman gidan su yarinyar da yake ganin k'ask'anci ne kamar shi yaje wannan k'azamar unguwar kuma ace auren d'an shi ake yi gurin. Dak'yar da lallami k'anen shi Abban Yusrah wato Alh Muttak'a ya shawo kanshi kan zuwa gurin auren. A 6angaren Alamein kuwa shi ma dak'yar da lallami Mum dasu Salis suka ciwo kan shi ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin dakakkiyar shaddar shi fara k'al wacce ta k'ara fito da kyawon shi na asali, sai dai daka dubi fuskar shi babu annuri sam a tattare dashi. Bayan gama d'aurin auren ne Imran ke yimai tuni kan gaisuwar da Ango da abokanen shi ke shiga yi gidan su Amarya, tur6une fuska ya yi tamkar wanda aka yiwa wahayi da mutuwa. "Kayi hak'uri A.K.A kakka bijirewa umurnin Mum in kayi hakan ba za taji dad'i ba kuma kasan da za mu fito sai da ta k'ara jaddada mana hakan". Da hakan suka d'an shawo kanshi suka shiga gidan su Zajlah shi da tsirarrun abokanen shi suka gayar da iyayen, sai yak'e yake yi wanda ya fi kuka ciwo had'e da wani tur6une fuska tamkar yad'ora hannu Saman kai yafasa da kuka. Muryar Salis ya ji had'e da wasu friends na su suna tambayar ina Amarya ta fito a gaisa. Zumbur yamik'e tamkar wanda ya zauna akan kunama, hanyar fita daga gidan ya dosa ganin hakan ya sa suka mara mai baya. Can na tsinkayo maganar wata daga cikin dangin Zajlah na giwa tazo na furta. "Gaskiya wannan Angon na da kunya akan wasu mazajen da za kaga sun shigo gaida iyaye an saka Amarya gaba har da su d'aukar hoto". "Gaskiya kam wannan na da sauran kunyar shi", inji wata mata. Da hakan sauran k'awayen Zajlah suka shiga gidan su Salmat suna ta yabon kyawon angon, har wasu na zolayar ta da cewa' "shiyasa ake mana 6oyon Angon ashe ansan mai tsada ne hakan, gaskiya kin more Allah yabada zaman lafiya". Salmat ce ta kar6e da Ameen had'e da cewa ai dole mu 6oye angon mu ga irin ku masu hangen kyawawan Maza. Da hakan dai suka ta zolayar juna wanda Zajlah tayi shiru ita d'ai tasan me take tunani a ranta saboda tana hango abubuwa da dama. *** 10:00pm Aka kai Amarya d'akin ta had'e da y'an rakiyar ta iyaye da abokanai har da dangin ta y'an giwa tazo, a unguwar G.r.a aka kaita gida ne d'an matsakaici mai part uku wanda yasha shuke-shuke na flowers sai k'amshi ke tashi. Nan dai dangi suka yi mata nasiha gwargwado had'e da lurar da ita muhimmancin hak'uri da biyayya, har wata na cewa duk da munsan abinda za mu fad'a duk malaman Ku sun riga mu. Da za su tafi ta ci kuka sosai har ta gode Allah inda take ta tunanin wace rayuwa za ta fad'a yanzu. Har k'arfe goma sha biyu bataji d'uriyar kowa ba, da hakan ta rage kayan jikin ta ta zazzagaya d'akin wanda ta jinjina ma mahaifinta da k'ok'arin da yayi duk da cewa yawanci siyayyar da kud'in da ta samu a musabak'a ne, ta ji dad'in ganin cewa har da keken d'inkin ta aka had'o mata dashi. Da hakan ta shiga ta watsa ruwa had'e da alwala ta yi karatun K'ur'an had'e da addu'o'in ta, ba ita ta kwanta ba sai wurin k'arfe d'ayan dare. ** 6angaren Alamein kuwa ba yanda su Imran

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38