Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

wanda sai ya ganta hankalin shi ke kwanciya, amma ya lura da ita yanzu wani basarwa take yi, bata cika shiga sabgarshi ba, asali ma indai ba d'inki take yi ba to tana part d'in su Mum don wani lokaci daga can za'a saka masu abinci ko da zai shigo gidan har ta rufe d'akin ta ta yi kwanciyar ta, hakan ba k'aramin damun shi abin yake yi ba. *** Yau gidan su ta shirya za taje saboda ta kwana biyu bata je ba, nan ta dad'e tana hira da mahaifinta har yana k'ara yi mata nasiha kan hak'uri da halin da suke ciki har yana yi mata nuni da kowane bawa bazai kaucewa k'addarar shi ba, kuma ta rik'a mijin ta hannu biyu ta girmama iyayen mijin ta. Bayan magrib ne aka aiko yaro ana sallama da Malam Abu, ita ko lokacin za ta shiga gurin Mama Inno ta yi mata sallama don tana son wuce wa gida, abin mamaki motar Dad ta gani k'ofar gidan su wanda ta yi mamakin hakan a ranta, sai kawai ta dake ta fad'a gidan su Salmat saboda tunanin ba shi kad'ai ne mai irin motar ba. Tana zaune suna hira da Mama Inno sai ga Naja'atu ta shigo da gudun ta tana gaya mata Baba yace ta fito ga mijin ta ya zo d'aukar ta, sai da safe ta yiwa Mama ta fice daga gidan tana ta mamakin wai Alamein ne ya zo d'aukar ta yau, mamakin ta bai k'aru ba sai da ta ganshi da Baban ta suna hira cikin girmamawa da mutuntawa, hakan ta shiga gidan su ta yiwa Mama Asabe sallama ta d'auko jakarta ta fito, nan Baban ta ya shige gida. Gudun ta shiga gaban ta janyo ma kanta ya sa ta je bud'e k'ofar baya amma ta ji ta rufe, gaban ya bud'e mata sannan ta shiga badan ta so ba. Yau ko gaisuwa bai samu daga gare ta ba sai wani cin magani da take yi, saboda bata ma son irin yanda yake bibiyar ta kaita unguwa ko d'auko ta, wayar ta ta fitar had'e da kunna data tana charting. Warce wayar kawai ta ji ya yi sai ta bishi da kallo kuma ta sadda kanta k'asa, saboda bata iya jurar had'a ido dashi. Wayar ya rik'a bincike ya ga group uku, na make up, mu koma kitchen sai musha karatu, contacts kuma Salmat, Saudat, Yusrah sai Shema'u ya gani. "Kasan dai bincike ba kyau, kabani waya ta", cikin zumb'uro baki take maganar had'e da mik'o mai hannu. Wayar ya mik'a mata tana mik'o hannu ya rik'e ya d'ora saman sitarin motar yana murza yatsun ta, abinda ya tsirga masu lokaci guda yasa ya yi saurin sakin hannun na ta sannan ya d'ora mata wayar saman cinyar ta, daga hakan ba wanda yak'ara magana har suka iso gidan. K'ofar motar ta rik'a za ta bud'e ta ji ta gam, sai da ya fita ya zaga ya bud'e mata k'ofar ya rik'o wayar ta da jakar ta inda har ta ji nauyin Baba maigadi daya bud'e masu gate, (nidai Jegal hab'a na rik'e nace sabon salo kiran sallah da usur, ina ruwan neman gindin zama, lolx). *** Ya dad'e yana bibiyar ta tun lokacin da ya rasa Zajlah lokacin tana zuwa school of health. Ko da ya yi tafiya ya dawo ne yake tambayar wani friend d'in shi dake aiki B.L.B plaza kan cewa ya dai na ganin yarinyar, nan yake bashi tabbacin sun k'are makarantar, bincike ya yi har ya gano gidan su yarinyar, inda bai son a kuma samun matsala ya rasa yarinyar saboda ya yaba da hankalin ta had'e da nutsuwar ta, sai dai ga alama za ta d'anyi ji da kai irin na masu kud'i. Hakan dai ya ji ta kwanta mai a rai, da hakan ya gayawa iyayen shi kan yana so aje mai tambayar neman iznin ganawa da yarinyar. Manyan shi basuyi k'asa a gwiywa ba suka je gidan su yarinyar inda kuma magabatan ta suka bashi damar shigowa ya gana da yarinyar. **** Tun da aka gaya mata cewa za tayi bak'o ta shirya tsab sai zaman jiran ganin bak'on na ta. Ba'a fi minti goma da shirin ta ba sai gashi an aiko tazo bak'on ta ya iso. Sit room d'in Dad na bak'i aka saukar dashi shi da wani friend d'in shi, hakan ta je suka gaisa, nan ya Isar da sak'on k'ok'on baran shi zuwa gare ta kuma ba laifi ta yi na'am dashi, nan yake ba ta labarin tun lokacin da ya fara son ta da kuma shakkar tunkarar ta kamar bazai yi nasara ba, da hakan hira ta 6arke tsakanin su. Lokacin da zai wuce ne ya nemi tayi mai iso ga iyayen ta domin ya gaisa dasu, gidan ta shiga ta yi masu bayani sannan ta fito ta yi masu iso, bayan sun shiga falon ne suka gaisa da mahaifin ta, inda ya yaba da hankali da nutsuwar yaran kuma yana ganin y'ar shi ta dace. D'akin ta doso sanadiyyar y'ar ta data matsa sai ta zo sun gaisa da sirikin nata, suna had'a ido take gaban su ya bada rasssss!. .,,.......... Cikin azama ya zabura da k'arfi tamkar wanda ya zauna dama saman allura, wannan dattijuwar fuskar ba za ta ta6a 6ace mai ba. "Koma ka zauna, ina zaka je?". Nan ya gagara bata amsa saboda irin tsabar rud'ewar da yayi, cikin murmushin ta dake k'arawa kamilallar fuskar ta fara'a ta nemi guri ta zauna, "a cikin Ku waye sirikin nawa?". Farouk ne ya nuna Fadeel da yatsa yana mai Sosa kai. Shi ko Fadeel ji yake yi tamkar k'asa ta bude yanitse a gurin, tsabar jin nauyi duk da a wancan lokacin ya bata hak'uri. Kawai ganin shi suka yi durk'ushe gaban ta yana mai k'ara neman yafiyar kuskuren da yakusa tafkawa. Har ga Allah bata so hakan ba, kuma ba don hakan da ya yi ba to tayi alk'awari baza ta fad'awa kowa abinda yafaru ba, amma sai gashi yana batun bayyana kanshi. Mamaki ne k'arara a fuskar sauran mutanen da ke falon, kowa alamar tambaya fal a fuskar shi, muryar Mum ce ta daki dodon kunnen su yayin da take furta, "wannan abin ya riga ya wuce a guri na, kuma na d'auki faruwar hakan silar abubuwa da dama, saboda ta nan ne na samu sirika data zamo alkhairi a cikin iyali na, kuma ta hakan ne Allah ya had'ani da siriki na", nan ta k'arashe maganar cikin murmushi. Fadeel ne ya tayar da kai ya kalle ta, sannan ya kuma nok'e kai, alamar tambaya ta hango fal a fuskar shi. "Wannan yarinyar dai yanzu haka tana gidan nan matsayin matar yaro na". Daram! Ya ji gaban shi ya buga saboda jin Zajlah na gidan, duk da ya dad'e da cire ta a ran shi saboda hango irin nisan da ta yimai na tabbatar da ta yi aure. "Ni fa bangane ba sai wata magana kuke yi a dunk'ule wacce mu bamu fahimci ina kuka dosa ba, dama kinsan sirikin na ki ko yaya?", Dad ne ke yiwa Mum wannan tambayar. Hakan ne ya sa ta kwashe abinda ya faru tsakanin ta da Fadeel ta gaya masu, inda jikin kowa

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38