Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

fahimci d'iyar k'anen Baban shi ce, sa6anin Saudat dake bin su da muguwar harara. Zuwa bayan isha'i ne Dad ya shigo gida, bayan Mum ta yi mai barka da dawowa ne take gaya mai cewa, "na fa tsayar da matar Son don ku gaisa". "Ai da kin bar ta ta wuce ba sai mun gaisa ba, tunda ke da kika k'ulla abin kin ganta kuma ta gan ki. Wai ma kina hankalce da yanda kika lalatamin rayuwar yaro?". "Haba Dadyn Alamein ban fahimce ka ba, me ya ka wo wannan maganar?, me yasa abu baya wuce wa a gurin ka?". . "Ba wai baya wuce wa bane, rai na ke 6aci in har na dubi yanda Son ya koma yanzu, walwala, farin ciki, nishad'i duk sun kau a rayuwar shi har wata uban rama ya yi duk ya zabge tamkar wanda ya kwanta ciwo". Murmushi ta yi irin na su na manya had'e da furta "Adalilin gatan da nayiwa Son in har muna raye za kaji dad'in abin, kai dai ka rik'a d'ora shi akan turba ta k'warai had'e da lurar dashi wasu abubuwan". Tana kaiwa k'arshen maganar ta fito zuwa falo ta janyo Zajlah sai falon Dad. Har k'asa ta durk'usa ta gaida shi cikin nutsuwa da girmama wa, har ga Allah yarinyar ta burge shi sosai, sai dai matsalar d'aya ce da Son baya son ta. Saboda shi fa duk abinda zai yi sanadiyyar farin cikin yaran shi yake yin shi, kuma in ba su son abu har ga Allah zai iya yafe abin nan duk son da yake yimai. Mum ce ta ta6o shi alamar yayi magana ya sanya wa auren albarka, hakan ya yi gyaran murya suka k'ara gaisawa ya sanya mata albarka had'e da fatar zaman lafiya. Da za ta wuce dubu goma ya ba ta, sai dai k'in kar6a tayi sai da Mum ta kar6ar mata. Mum kuma turarukka had'e da humra y'ar asali ta Maiduguri ta had'a mata, har za su wuce take tambayar ta ina wayar ta halan? Amsa ta ba ta kan ce wa wayar na cikin kayan lefen ta ko bud'a ta bata yi ba. "In kinje gida ki had'a wayar mana tunda can su Maman Sagiru sun hana kiyi amfani da ita, ko ba kyaso ki gaisa da k'awaye da kuma ni Mum d'in ki?". Murmushi ta yi ta soke kai, karaf Yusrah ta ce' "Mum ta bari gobe zan zo in had'a mata". "To anji sarkin iya yi", cewar Mum. Da hakan direba ya kai ta gida inda ta so Salmat ta shigo ta nuna mata ce wa dare ya yi, kuma ta san unguwar ta su sai a slow, amma za tazo ranar Alhamis ita da k'awayen su na makaranta. Warmers d'in da Mum ta ba ta ta d'auka ta shiga gida had'e da sauran kayan ta ita ko Salmat direba ya wuce da ita gida. ** Bayan Zajlah ta shiga gidan ne ta ajiye kayan abinci a falon, bedroom d'inta ta wuce, saboda tsabar gajiya tu6ewa tayi ta fad'a toilet ta yi wanka. Kayan ta na lefe ta bud'e wanda bata ma san ya suke ba, akwatin k'ana nan kaya ta bud'e ta samu wata night gown mai d'an girma ta saka, hijab k'arami ta d'ora sannan ta fice zuwa falon, plate ta d'auko kitchen ta d'ibi abincin ta koma d'akin ta. Bayan ta gama ne ta je kitchen ta wanke abinda tayi amfani dasu sannan ta koma d'akin ta, alwala ta yo ta shimfid'a carpet ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi lazimi sannan ta kwanta. Tabbas ta dad'e tana tsara ma kanta irin rayuwar da za tayi ta farin ciki a gidan auren ta, da kuma kyautata wa duk wanda ta aura saboda samun lada a k'ark'ashin shi, sai dai kash tana ganin da wuya hakan ta kasance a yanda take ganin wannan auren. Gashi a tsarin ta tana son namiji mai tsayi kuma gashi ta samu sai dai a banza don bata gaban shi "ya Allah kakka d'ora min son wannan bawan Allah a zuciya ta". *** 6angaren Alamein kuwa har akaci aka sud'e bai lek'a gidan su ba saboda dama ba mutum ne maison shiga gurin harakar mata ba. Yana shigowa gidan ya ci abinci daya gani a dinning table sannan ya shiga part d'in shi, wanka ya yi ya nemi guri ya kwanta da tunane-tunane fal a ranshi har bacci ya yi awon gaba dashi. . WASHE GARI Bayan ta gabatar da sallah ne da abubuwan da suka dace tayi wanka ta shirya cikin atamfar ta kalar lemon green fitted. Bakin gado ta zauna ta zabga uban tagumi komi ya cunkushe mata, sai tunani take yi dama haka rayuwar auren take ko kuma nata ne yazo a hakan? Duk iya nazarin ta ta rasa gane wane matsayi take dashi a gurin Angon. Jin hayaniyar mutane a falon ne ya sa ta janyo gyalen ta ta yafa ta fita, saboda tana tunanin Yusrah ce kamar yanda ta yi alkawari za tazo jiya. Tana fita karaf idon ta cikin nashi yana dariya k'annen shi sun saka shi tsakiya. Gabanta ne ya yi mugun fad'uwa saboda annurin fuskar shi daya kau cikin second uku. "Laah Brother kace Amarya bata ta shi ba, ga shi har ta tsantsara kwalliya", da saurin Yusrah ta taro ta had'e da zaunar da ita, d'an zamewa ta yi k'asa ta gayar dashi, ya amsa ba yabo ba fallasa saboda k'in amsawar zai sa Yusrah ta dame shi. Breakfast ta had'a mata da kanta tana tarairayar ta sa6anin Saudat dake binta da mugun kallo. Zumbur ya mik'e ya wuce part d'in shi saboda bazai iya kallon kayan haushi ba. Bayan ta gama karyawa ne suka shiga hirar duniya ita da Yusrah har tana tambayar ta matsayin karatun ta. "Gaskiya iya primary school kawai nayi saboda na fi son islamiya akan bokon". "No wonder! Biri ya yi kama da mutum", cewar Saudat. Harara Yusrah ta dinga zabga mata had'e da yi mata alamar gamon ki da Mum, sanin za su iya komawa ta gayawa Mum ya sa ta yi shiru, wayar ta ta fitar tana latse-latse. Hakan ya tuna ma Yusrah maganar had'a ma Zajlah wayar ta, nan ta gaya mata taje ta d'auko wayar ta kawo mata. "Ina fatar kin saka charge". "Eh na saka tun jiya", ta ba ta amsa. Wayar ce ta had'a mata har da layi biyu cikin kwalin wayar da credit, Mtn da Etisalat. . Ba number kowa a wayar hakan ya sa Yusrah ta saka mata ta ta number data Mum, ko kad'an batayi gigin saka mata ta Saudat ba sai kuma number Alamein da ta yi mata saving da (HUBBY), lambar ta shiga kira sau biyu tana tsinkewa sai ana ukun kamar bazai d'aga sai kuma ya d'aga. "Brother number Madam kenan". Bata jira me zai ce ba ta tsinke wayar, wayar ya bi da kallo had'e da furta "lallai yarinyar nan ta samu sake, don ma ta samu shekaranjia Mum ta ce nakar6i lambar ta mu rik'a zumunci shi ne za ta wani zak'ewa da baiwa wata lamba ta", za mu had'u ne". Bayan ta nu na mata duk abinda ya kama ta tasani take gaya mata su shiga kitchen suyi girki

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38