Chapter 26
Chapter 26
nazari da hangen nesa? Lallai tabbas ba girma ne hankali ba, ba shekaru ne tunani ba, dame yarinyar nan ke aiki cikin kwanyar ta?". Duk shi kad'ai ke yiwa kanshi wad'an nan tambayoyin sanadiyyar mafita da ya ji Zajlah ta samo wanda iya nazarin su basu kawo hakan ba. Mum ce ta janyo Zajlah ta rungume kan jin dad'i tana hawaye, sai albarka take saka mata wanda take jin tamkar ta maida ta ciki kan irin son da take yi mata da kulawa da dukkan damuwar ta. Suna hakan ne ya yi sallama ya fad'o falon, wanda daka kalleshi zaka hango walwala, farin ciki, annashuwa kwance saman fuskar shi, har k'asa ya durk'usa ya gaida Mum, cikin farin ciki ta amsa fuskar ta sake. "Sannu da zuwa", cikin sanyin muryar ta ta furta hakan sannan ta wuce zuwa d'akin Saudat da Mum ta gaya mata tana fama da zazza6i, kuma tana so ta basu guri su gana da junan su. . Bayan ficewar ta ne Mum ta kai duban ta zuwa ga Alamein had'e da furta "ka fara ganin irin alkhairin da nake hango ma a cikin zamantake warka da yarinyar nan? Wallahi na yi imani da Allah da wata ce ko siyar da gidan kace za kayi sai kunsha artabu da ita, in ma bata ce sai ka sake ta ba". "Wannan zamanin da ake ciki mun kawo ga6ar da yawancin y'an Mata basu cika yin aure saboda Allah ba, farko kana zuwa neman yarinya za kaji ana fad'in da wacce mota yazo? Daga hakan sai kaji iyaye na fad'in ai ko ki auri abinki ance yana da hankali da nutsuwa, nan ko nutsuwar kud'i ce ba nutsuwar Allah da Annabi ba". "Ina mai baka shawara daka rik'e yarinyar nan amana domin ta wuce k'ask'anci yanzu daga gare ka, ina sane da har yanzu babu wani cigaba a cikin rayuwar auren ku saboda bak'ar ak'idar da ka saka a zuciyar ka na k'yamatar talaka". Cikin razana da mamakin ina tasan irin zaman da suke yi yasa ya tayar da kai ya dube ta. "Kar kayi mamaki kuma kar ka zargi Zajlah da abinda ba haka bane, don tun auren ku wata magana data shafe ka bata tab'a had'a ni da ita ba". "Na dad'e da fahimtar hakan tun ranar da muka je gidan su yiwa mahaifin ta sallama, kuma ko kukan da take yi nasan da biyu take yin shi saboda akwai abinda kayi mata". "Yanzu dai dabara ta rage gare ka ta yanda zaka shawo kan matar ka ku zauna lafiya, don yanzu ka tabbatar da ita ba k'ashin yarwa bace". ** ** Ko da ta shiga d'akin Saudat bacci take yi, hakan ya sa ta nemi guri ta zauna ta bud'e datar wayar ta ta hau whatsap, yanda taji ana comments kan wani novel ( *AL'ADUN WASU, BATUL MAMMAN) ya sa ta yi ta tambayar farkon buk d'in, nan take aka tura mata saboda musha karatu akwai kula juna. Datar ta rufe sannan ta hau karatun littafin, sosai buk d'in ke saka ta nishad'i da walwala, dariyar tace ta tayar da Saudat daga baccin da take yi, had'a ido da suka yi yasa tasha jinini jikin ta saboda jiran saukar rashin mutunci kwando-kwando. Kafad'ar ta ta dafa had'e da furta "matar Brother me ya saka ki nishad'i haka kike ta dariya?". Cikin sanyin jiki ta gaya mata har da nuna mata buk d'in, "kai an baro ki baya ai ni yanzu kullum cikin zuba ido nake in matsu ba'a turo cigaban ba, saboda novel d'in yayi gaskiya ga dariya cikin shi sosai". "Aiko da zan iya dana ajiye karatun har tagama duka, saboda banson jira gaskiya matsuwa nake yi". "Ni ko nafi so ana yi ina biya kodon y'an comments dasu ke baka labari kuma ban iya karatu in yayi yawa". "Tabbb ai ina ga babu group d'in da suka kai musha karatu comments, kuma gasu da kula juna gaskiya, oh! kinga na manta, ya jikin ki?". "Ai naji sauk'i sosai don kan ya daina ciwo", hakan suka zauna suna ta hira wanda ni kai na Jegal nake mamakin hakan. ** *** Zaune yake jugum yana sauraren maganganun Mum had'e da nazari kan su duk jikin shi ya yi sanyi. "Abu na gaba shine ka dai ga yanda Allah ya sako mana jarabawa farat d'aya wanda bamu yi zato ba kuma bamu yi tsammani ba to ya kama ta ace ka natsu kasan me duniya take ciki, a wancan lokacin in har ina lurar da kai wasu abubuwan sai dai ka rik'a biyar zugar mahaifin ku na rud'in dukiya, yanzu gashi duk tak'amar ku da ji da kan ku da izzar ku ta rushe lokaci guda wanda baku da wata dabara sai yanda wanda ya baku ya yi daku". "A zamantakewar rayuwa ana so mutum yasan k'ima da darajar d'an Adam, ba akan komai ba sai don gama wa da duniya lafiya, wanda ka gani talaka haka Allah ya so ganin shi, ba don ba ya son shi ya yi shi hakan ba, sai dai ban-ban cewa tsakanin rayuwa da kuma hankalta". "Yanzu ka duba kagani yanda Allah ke baiwa kafiri kud'i ya hana wa musulmi, kuma fa ba don ya fi son kafiri d'in akan musulmin ba, a'ah don ya gwada k'arfin ikon shi ne da kuma tsara abubuwan shi yanda yaso. Da wuya kaga kafiri yana fama da talauci tamkar musulmi, ko yaushe za ka ganshi cikin jin dad'in rayuwa, to wannan jin dad'in na duniya shine ribar su gaba d'aya saboda lahira jahannama ce mazaunin su". "Sannan kayi nazarin wacce Sana'a ta dace ka fara, saboda yanzu zama haka kawai ba naka bane, don kaga kaine Babba kuma kaga yanda mahaifinku yake, ko babu ciwo akwai yanayin girma daya kamata kad'auke wa mahaifinka wasu abubuwan". "Ba matsala Mum bari zan binciki Imran da Salis gobe muyi shawara, daga nan asamu mai sayen gidan, in an kammala kud'in sai muga abinda yayi saura sannan asan Sana'ar da za'a kama". "To Allah yasa a fara a sa'a, Ameen ya furta a taka'aice had'e da dogon nazari na rayuwar shi. Duk wad'annan abubuwan da Mum ke jerowa har ga Allah yasan hakane, amma me yasa a wancan lokaci bai yi duba zuwa gare su ba? "Giyar kud'i", hakan wata zuciya ta bashi amsa. Lallai tabbas ya yarda da hakan, saboda yasan in can inda aka fito ne bazai tsaya ya saurari Mum ba har maganar ta tayi tasiri akan shi ba kamar yanzu. Bayan sun gama tattauna wa ne ya k'arasa gurin Dad suka gaisa ya yi mai ya jiki, sannan suka d'an ta6a hira, duk da ba magana mai tsawo yake iya yi ba sosai. . WASHE GARI Wata shawara ce ta yanke a ranta bayan ta kira Salmat ta gaya mata abinda ke faruwa, inda ita ma ta tausaya masu sosai had'e da k'ara k'arfafa mata gwuywa kan abinda za tayi. Bayan ta gama breakfast ne ta jera a dining table sannan ta fad'a wanka ta fito ta kimtsa, sanin cewa yanzu yana gurin Dad ya sa ta shiga ta kimtsa d'akin na shi kamar kullum sannan ta fito ta ci abinci. 11:00am Ta fita zuwa gidan Shema'u mak'ociyar ta, "yau wace rana Zajlah a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38