Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

dukan uku-uku. Ruwan Mum ta watsa mai a fuska saboda tabbacin yana raye suma ne ya yi, firgigit ya motsa dafe da k'asan marar shi sai hawaye ne ke yi mai zuba. "Mum kice wa Zajlah ta so ni kamar yanda nake son ta, Mum wallahi na gano kuskure na, zan iya rasa rayu.....". Mum ce ta rufe mai baki, sannan ta kai duban ta ga Zajlah da ta nok'e kan ta tamkar wata marar gaskiya, "ki kula da mijin ki", hakan kawai ta furta ta bar masu falon, saboda dama tasan duk "So" ne ke d'awainiya dasu amma kowan nen su na basarwa a dole bai son d'ayan ya fahimci hakan. K'arasowa tayi gurin shi had'e da tattara kayan da ya yiwa amai ta kai toilet ta wanke sannan ta had'a mai ruwan wanka ta fito, taimaka mai ta yi ya shiga wankan, ko da ya fito ta kimtsa d'akin ta fesa turare, sannan ta had'a mai tea mai kauri. "Sannu ya jikin?". "Da na mutu ai kin huta tunda ba damuwa kika yi dani ba", cup d'in da ta had'a mai tea ta mik'a mai ya kar6a ya ajiye gefe, gaban ta ya zo ya gurfana had'e da rok'on ta gafarar abinda ya aika ta mata a baya. Bata San lokacin da ta rik'o hannuwan shi ba alamar ya tashi sai da ta ji ya fad'o mata ragwaf saman jiki, yunk'urin janyewa ta yi had'e da furta "wash! Hannu na", hakan ta sa ya yi saurin zabura, da saurin ta ta koma saman kujera tana dariya had'e da yi mai gwalo. Cup d'in ya rik'a sannan ya dawo kusa gare ta ya zauna, baki ya bud'e zai yi magana ta yimai alamar yasha tea d'in sannan su yi magana. Hakan ya shanye tass ya ajiye sannan ya tattara dukan hankalin shi zuwa gare ta yana wasa da jelar gashin ta, "Zajlah plxxxx kice kina so na", cikin kasalalliyar murya ya furta hakan. "Ai Kaine baka "So" na, amma ni tun farko ban ta6a jin k'iyayyar ka a rai na ba, sai dai kai da kake ji tamkar ka hasa wuta ka.......". Bai bari ta k'arasa ba ya dafe mata baki da hannun shi, "ki yarda ni kaina ban ta6a jin k'iyayyar ki ba, sai dai rashin son kula mata da baya gaba na". "To yanzu gaya min wane irin kalar so kake yi min". "Ni ba son ki nake yi ba K'aunar kice da ta dabai baye ni take batun mayar dani wani zautacce, saboda K'auna ba ta ta6a canja wa, So kuma wataran zai iya canjawa". Hira suka shiga sosai kowan nen su na nunawa juna irin yanda yake jin shi a ranshi, wanda ta kai tun suna saman kujera har suka koma saman gado (ni dai Jegal k'ofa na ja masu na fita, su Aunty Sis sunan Ku sorry Zajlah ta lula a duniyar ma'aura ta, kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah, lolx). ............ Kiran sallar magrib ya dawo dasu hayyacin su, inda Zajlah sai wata shagwa6a take mata zuba mai, wanka Alamein ya fad'a sai da ya fito sannan ya had'a mata ruwa ya taimaka mata ta yi wanka, ganin lokacin sallah ya kusa shigewa ya sa ya jasu jam'i suka gabatar da farali suka d'ora da nafila sannan suka jero addu'o'i, basu tashi daga gurin ba sai da suka gabatar da isha sannan Zajlah ta ja jiki ta koma saman gado ta k'udun-dune, gadon shi ma ya hau yana tsokanar ta had'e da saka mata albarka. Daka kalli fuskar shi za Kasan cewa yana cikin farin ciki, walwala had'e da nishad'i, "ya dace in fita in sawo maki kazar ki ta amarci amma kuma duk kin d'ibge min jiki". Ido ta gwalo waje alamar mamakin maganar da ya furta, kashe mata ido d'aya ya yi sannan ya furta "ko k'arya nake yi?, ni da ke jinya ko k'arfin jiki bani da". Kunya ce gaba d'aya ta lallu6e ta dole ta nok'e kan ta had'e da k'udun-dune wa cikin blanket, hakan ya sa ya zira jalabiyar shi ya zari key d'in mota ya fice daga gidan. Fitar shi ya sa ta yaye bargon da ta lullu6a dashi ta ja jiki sai toilet, jikin ta ta k'ara gasawa sannan ta fad'a kitchen, indomie ce ta dafa masu da ta ji kifin gwangwani, tana juyewa a kula ta ji motsin shigowar shi, a falo suka had'u ta d'auko kular abincin za ta kai dining, shi ko yana rik'e da ledoji a hannun shi, da Sauri ya saki ledojin da ke hannun shi ya taryo ta, kular ya kar6a sannan ya rik'o hannun ta suka k'arasa falon, sai da ya ajiye ta saman kujera sannan ya ajiye kular abincin k'asa, ledojin ya koma ya d'auko ya wuce kitchen ya had'o da plates had'e da spoon. Sai da ya ajiye kayan sannan ya kai duban shi zuwa gare ta "wa yace kiyi girki yanzu?, in je kawai in dawo ke ce makuku har kin fad'a kitchen", yana maganar ne da murmushi d'auke a fuskar shi tamkar gonar auduga. "To in banyi girki ba me kake so muci?, ko mu kwana da yunwa kake so?, ni da ma ka maida ma ciki tamkar an yimin yaso". Suna had'a ido ta nok'e kan ta tana murmushi, "yarinya za kiyi bayani ne". Daga hakan ya fitar da kaza biyu da fresh milk sai wani take away dake da ferfesun y'an ciki daya siyo B.L.B, baki ta saki tana kallon shi had'e da furta "da mu da wa way'annan kayan?, ka d'auki kaza d'aya ka kaiwa su Mum". Ido ya gwalo waje yana kallon ta, "wato so kike in bayyana kaina gurin Mum", dariya ta yi sosai sannan ta ware d'ayar ta bashi ya saka a fridge gobe a d'imama akai masu, saboda ita ma tasan baza ta iya zuwa part d'in ba yanzu. Da hakan suka ci suka k'oshi, sannan suka dasa baben hira da nunawa juna kula wa tamkar sa had'iye junan su, sai k'arfe *11:30pm*sannan suka kwanta. **** Kwanaki sun shud'e watanni ma haka, inda yau ne Zajlah ke ta shirye-shirye tun safe kan zuwa sunan y'ar da Salmat ta haifa, akwati d'aya suka had'a ita da Alamein na kayan jinjiri da kayan amaryar k'arni, saboda yanzu gwargwado hanyar samu na k'ara bud'ewa Alamein a cikin kasuwancin shi, tun 08:00am ta kammala aikin ta take ta tayar da Alamein kan ya tashi ya sauke ta gida ya k'i sai juyi yake yi saman gado, dabara ta fad'o mata ruwan sanyi ta d'ebo ta yayyafa mai a fuska, yana tashi ya janyo ta saman gadon sai da ta yi ta had'ashi da Allah sannan ya sake ta ya d'auko key suka fice. Gidan su Salmat cike yake da y'an suna, Yusrah, Saudat, Zajlah sun kammalu gidan inda akayi taron suna aka watse kowa yaci ya k'oshi sai dai fatar Allah ya raya Mus'ab, sai dare sannan kowannen su mijin shi ya zo d'aukar shi suka wuce. ***** Bayan sati biyu ne da sunan Salmat tana kitchen tana tafashen kayan ciki za ta d'ora girki ta fito aguje wurin toilet d'in su na tsakar gida tana lezaya amai tamkar za ta had'o da hanjin ta, k'arar aman ta ne ya

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38