Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
Download Book

wuce ta kai kayan sannan ta dawo d'aukar na hannun Salis, abinda ta ji ne ya sa ta ja birki ta tsaya. "Yanzu don Allah A.K.A abinda kake yi a tunanin ka ya dace?, don kawai kar kaje d'auko yarinyar nan sai ka kira ni kace inje in d'auko ta wani aiki kake yi kallon ne aiki ko kuma chart da kake yi?". "Salis ya kake so inyi da rayuwa ta ne?, ka duba kaga yanda damuwa tayi min yawa, abubuwa duk sun ja baya, ko company sai ku ne ke kula dashi". "Wallahi in na ga yarinyar nan har wani k'unci ke ziyartar zuciya ta, na rasa ina zan tsoma kaina inji sanyi". "Hak'uri za kayi, muzgunawa yarinyar tamkar rashin bin umurnin Mum ne, kuma ni banga illar Zajlah ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa, don Allah ka sassauta mata dame za taji? Auren dole ko rashin bata kulawa da baka yi?". "Ko ma miye ita taja wa kanta, da ace da Mum taje da buk'atar neman auren tace ba taso ai da ta hutar da kan ta, to nasan kwad'ayi ya kawo ta shiyasa". "Ai ko da kaga iyayen ta kasan mutane ne masu wadatar zuci da neman na kansu, kwata-kwata wannan abin bai dace ba wallahi". Ganin cewa baza ta iya jure sauraren maganganun ba yasa ta fad'a falon ta yiwa Salis sai da safe ta kwashi kayan ta ta koma part d'in ta. "To yanzu duba don Allah alama ta nuna ta ji me kake fad'a, kasan dai ba dad'i". "Kai ni fa ko a gaban ta zan furta abinda nayi niya don ba tsoron ta nake ji ba". Ganin in ya yi gabas yayi yamma ne yasa ya yimai sai da safe ya fice daga gidan rai 6ace da halayya irin ta A.K.A. * * * 6angaren Zajlah kuwa tana shiga d'akin gado ta fad'a tana ta razgar kuka cikin damuwa da tsananin 6acin rai. A rayuwar ta bata ta6a saka ma ranta auren mai kud'i don taci kud'in shi ba, asali ma tafi hangen auren rufin asiri ta samu talaka d'an uwan ta da zai san darajar ta da k'imar ta, saboda yawancin masu kud'i basu cika d'aukar talaka wata tsiya a doron k'asa ba. Hakan ta ci kukan ta har ta gode Allah ba mai rarrashi. Alwala ta yo ta yi sallah had'e da kaiwa Allah kukan ta kan yakawo mafita acikin wannan aure na ta, bayan ta gama ne ta dunk'ula ta kwanta had'e da tunani iri-iri har bacci ya yi awon gaba da ita. * * * WASHE GARI Bayan ta gama sallah ne ta kimtsa d'akin ta, wanka ta yi ta shirya sannan ta nufi kitchen tea ta had'a iya cikin ta sai k'wai biyu data soya, bayan ta karya ne ta koma d'akin ta ta kwashi turamen da tazo dasu ta nufi d'ayan k'aramin d'akin da aka saka mata keken d'inkin ta da sauran komatsan ta, zaune ta yi ta fara yankan d'inkin sai da ta yanka turmi hud'u sannan ta hau keken ta fara. * * * 6angaren Alamein ko yana dosowa falon k'amshin wainar k'wai ta doki hancin shi, sai dai yaja ya yi turus da yaga dinning table d'in wayam sa6anin kullum da yake tarar da girki a gurin. Yau har ga Allah yaso yaci girkin ta kodon fad'an da Mum ta yimai ce wa kar yadawo gidan ta cin abinci in har ba matar shi ce taje mata wuni ba da tasan cewa babu mai bashi abinci ba. (Tabbb ni dai Jegal nace jin dad'in ferfesun kifi ne yasa Alamein zai la6a da fad'an Mum ya kwashi girki, sai ga shi ran Zajlah ya 6aci yau bata ajiye ba, lolx). Zaune ya yi turus a falon yana tunanin mafita, ga shi yana so yaje office cikin lokaci saboda wani meeting da zasu yi da wasu dasu ke da share a company d'in. Ga shi shi ba gwanin girki ba don ko ruwan Lipton bai iya dafawa ba. Kitchen ya fad'a ya yi sa'ar ruwan lipton har sun fara hucewa, hakan ya zuba madara da sugar kad'an ya sha ya fice daga gidan. * * * Zajlah ko na can na fama da d'inkin ta, har wani nishad'i take ji na ganin ta samu abinda zai rage mata damuwa, don har ga Allah ta manta wani 6acin rai data shiga jiya. Jin cikin ta na k'ugi ne ya sa ta ajiye d'inkin ta shiga kitchen macaroni ta yi jallof d'inta da dama ta saka a kula ta d'auki plate da cokali ta koma d'akin. Bayan ta zuba ta ci ne ta tsinkayo kiran azahar, nan ta yi sallah sannan ta hau d'inkin ta. . Kwanaki hud'u sun shud'e ba wani cigaba tsakanin zaman Alamein da Zajlah sai ma abinda ya k'arasa kwa6e wa, don yau kusan kwanan su biyu basu had'u da juna ba. Alamein ya fara shiga takura saboda ga shi ba gwanin yawon restaurant ba, asali ma yana iya cewa tun tashin shi bai ta6a cin abincin waje ko na wani aure ba sai dai na gidan su. A hakan yake buge-bugen shi in ya fita office yasha lemo da biskit, sai kuma maltina rabon shi da abincin kirki tun ranar da Zajlah ta wuni gidan Mum. ** ** ** Yau tun safe ta taya Mama Inno aikin gida saboda tana so taje gidan Zajlah, k'arfe 11:00 ta gama kimtsawa ta shiga gidan su Zajlah ta ja Naja'atu domin ta raka ta, saboda tun auren Zajlah ba ta jin dad'in fita ita kad'ai. Naja'atu y'ar k'anen Mama Asabe ce mai kimanin shekara tara a duniya, tun auren Zajlah Mama Asabe ta ji gidan ya yi mata shiru dayawa ta shawarci Mal Abu ta d'auko yarinyar ta dawo hannun ta da zama. Keke napep suka samu suka shiga sai G.R.A, gidan su Alamein ta fara shiga ta gaida Mum saboda karamcin dattijuwar, da murna ta tarye ta kamar ta had'iye ta, nan suka had'u da Yusrah ita ma ta zo ma Mum hutu kwana biyu. Tare suka rangad'a sai gidan Zajlah har Mum na mitar Yusrah ba ta gajiya da zuwa wurin Zajlah, basu had'u da Saudat ba akan tana makaranta. * * ** Zaune take saman tela ta duk'ufa d'inkin saboda yau take so ta k'arasa ta samu ko d'an mak'ociyar ta ne Shema'u ta aika yakai wa Salmat d'inkin, saboda Salmat ba ta da waya haka ma iyayen mata, su Mal Inuwa ne kawai suke da kuma Baban ta ya wuce saudiya kwana biyu da suka wuce. Jin sun shigo falon ne tsit ya sa direct suka yi part d'in ta, ganin su ba k'aramin farin ciki ya saka ta ba, da gudun ta ta rungume Salmat ta saki ta rungume Yusrah sannan ta saki baki tana kallon su. "Daga ina kuka had'u haka ba sanarwa sai dai ku diro ma mutum ba shiri?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Allah ne kawai ya had'a mu don mu d'ebe maki kewa yau, Mum na shiga gaidawa na tarar da ita a gidan". "Ai ko gaskiya na ji dad'i sosai da ganin ku", hannun Naja'atu ta rik'o had'e da tambayar ta lafiyar gida, yarinya mai surutu ta yita zubawa har

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38