Chapter 15
Chapter 15
sosai ba kullum muna islamiya". "Duk da hakan na san zai yi dad'i gaskiya, don kin fi waccan sangartacciya da ko ruwan Lipton bata iya dafa wa ba sai d'an banzar girman kai da raina mutane". A rayuwar ta ta k'i jinin cin naman musulmi d'an uwan ta, saboda sanin illar hakan, duk laifin ka gare ta ba za ta iya zaman zagin ka a bayan idon ka ba. "Allah ya kyauta Mama, a yita hak'uri. Wai ma ina Saudat d'in tun shigowa ta banji motsin ta ba?". "Yanzu za ki gan ta tun da azahar ta yi, dama tana zuwa health makaranta, auren nan ne ya sa ta kwana biyu bata je ba". Da hakan har ta kammala girkin ta fito falo, har k'asa ta durk'usa ta yiwa Mum sannu da hutawa, hannun ta ta rik'o ta zaunar da ita gab da ita. "Haba Zajlah har yaushe wai za ki daina jin nauyi na? Na gaya maki ki saki jikin ki tamkar kina gaban Mama Inno, ko Mama Asabe zance ne?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. Da hakan dai ta samu tana jan ta da hira har ta d'an saki jikin ta, nan Zajlah ke gaya mata tana so gobe taje gida yiwa Baban ta bankwana zai wuce saudiya jibi. "Ba matsala Zajlah zan shirya gobe muje tare in ya so in baro ki can ki wuni ko, ina fatar kin gaya wa Son batun tafiyar Baban na ki?". Tunawa da cewa jiya Salmat ta furta mai maganar ya sa tace' "eh Mum yasan da maganar". Tana shigowa falon ta yi turus ta tsaya tana wani shan k'amshi, da murnar ta ta taryo ta duk da tsorace take saboda gudun hantara, hannu ta mik'a ta kar6i litattafan da ta rungume had'e da furta "sannu da zuwa, ya makarantar?". Yauwa ta furta a tak'aice, duk da taso yi mata wulak'anci ganin Mum ya sa ta yi shiru, don ta san ko ta sha giyar wake ba za ta fara ba. Littafan ta kar6a ta wuce d'akin ta, (ni dai Jegal da ido na bi ta saboda mamakin ko mahaifiyar ta bata gaida ba). "Wai Zajlah ki na da ra'ayin makarantar boko ne ko ya ya?", "a ah Mum an ce boko da wuya kuma ni iya primary kawai na tsaya, sai dai ba laifi ina gane k'ananun abubuwa". . "Kuma Mum ni yanzu d'inki kawai na sa gaba, in dai ina sa mu ba laifi nasan zan rage kewar wasu abubuwan". "Au kice da mad'inkiya nake zaune, da fatar kin iya kar ki 6ata kayan mutane a tarar da Mum ranko", tana dariya take wannan maganar. Yanzu ta fahimci Mum na da dad'in zama ga kuma raha da take da, tabbas albasa bata yi halin ruwa ba. "Mum hala Dad bai shigo ba?, yau yunwa nake ji sosai wallahi, ko break ban yi ba a skul". "Kira shi kiji in ba yanzu zai shigo ba sai kici na ki, kin san yau ko yayan ki nan zai ci abinci tunda ga matar shi nan gidan". Jin cewa Brother zai zo gidan ya sa ta hak'ura har sai da suka dawo. A tare suka shigo gidan wanda ya sa ya yi turus ya bi ta da kallon mamaki, sai kuma ya basar ya k'araso cikin falon, don dama ko ta kan gidan shi bai bi ba ya yo gidan saboda ya samu abinda ya ci. Durk'usawa ta yi ta gaida Dad sannan ta yiwa Alamein sannu da zuwa, Dad ya kar6a ba yabo ba fallasa sa6anin Alamein dake yak'e wanda ya fi kuka ciwo. Falon Dad suka wuce saboda nan ne gurin cin abincin su, sa6anin Mum data tsaya suje tare da Zajlah aci abincin, inda ta nuna ma Mum ak'oshe take duk da yunwar da take ji tasan da nauyi taje cin abinci da surikin ta, duk da ta hango su a gurin su ba komai bane, kuma ita ma da tana gida tare da Baban ta take cin abinci. Tsinkayo muryar Mum tayi tana ba Talatu umurnin ta had'a abinci ta kai mata falon ta. Hannun ta ta rik'a ta kaita falon ta, sai da Talatu ta kawo komai sannan ta ba ta umurnin taci abinci kamin ta dawo, da hakan ta fice zuwa falon Dad. A DALILIN GATA Pape 16-20 . Falon Dad ta koma ko da ta shiga har sun gaji da jiran ta sun fara cin abincin sai santi suke yi, guri ta samu ta zauna ta saka abincin ta fara ci. "Mum baki ta6a ferfesun kifi da ya kai na yau dad'i ba, ga shi ya ji garlic sai k'amshi ke tashi". "Kawai Son ka fito ka gayan cewa matar ka ta fini iya girki, shiyasa har gaba na kake kasa hak'uri sai ka yabi girkin ta". Cak su duka suka tsayar da cokulan su daga cin abincin, kallo ya koma gurin Mum, Dad ne ya kasa hak'uri ya furta. "Yanzu kina nufin wannan mitsitsiyar yarinyar ce ta yi wannan girkin?, lallai Son kana kwasar ragwada, sai dai har yanzu banga ka fara kaurin wuya ba". Yana maganar yana Shafa wuyan shi alamar tsokana. Shi dai kawai basar da abin ya yi yana dariya yana nok'e kai, sai tunani yake yi ashe kan shi yayi wa da baicin abincin ta. "Gobe ma zanje gidan su yarinyar saboda mahaifin ta zai wuce saudiya, don haka kai ma Son ka shirya don kai za ka kaimu gobe d'in ni da ita". Ji yake yi tamkar yafasa ihu saboda yanda Mum ke son kusancin shi da yarinyar, shi ko har ga Allah ko ganin ta bai son yi, hakan dai ya kar6a ba don ran shi ya so ba. ** ** ** 6angaren Zajlah kuwa abincin ta ci sai da ta k'oshi sannan ta kai kayan abinci kitchen, d'akin ta dawo ta hau gyaran shi duk da ba wani gyara ne a d'akin ba, har toilet ta wanke ta shimfid'a sabon blanket ta feshe d'akin da air fresheners sannan ta dawo falon ta zauna, don jin take yi ba ta da ra'ayin fita falon gidan saboda kar ta had'u da Alamein. Tun daga k'ofar shigowa falon wani dadda d'an k'amshi ya tarye ta, ko da ta shigo falon ta gan ta kwance saman 3sitter barci ya yi awon gaba da ita. D'akin Mum ta za ga ko ina fes dashi sai k'amshi ke ta shi, a ranta take ta saka ma Zajlah albarka had'e da hango alkhairin da ke tattare a cikin auren. Sai la'asar Mum ta ta da ita ta gabatar da sallah ta kuma fad'awa kitchen suka yi girki ita da Mama Talatu, bata wani samu sakin fuska daga Saudat ba shiyasa take mak'ale da Mum ko Talatu. Har k'arfe 09:00pm ba labarin Alamein ba bu alamar shi, kuma wayar shi ma ta k'i shiga dole direba ne ya maida ta duk da ba nisa da gidan sai dai shirun unguwar. Kulolin abincin da ta zo dasu ne ta ajiye a falon ta wuce part d'in ta, saboda ba yunwa take ji ba sai da ta ci gidan sannan ta fito. *** Alamein kuwa da gayya ya k'i ko ma wa gidan, saboda yasan da ya je dole shi zai dawo da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38