Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

aka tashi kowa ya ka ma hanyar zuwa gida. Asaman hanyar ne Salmat da Zajla suke tattaunawa. "Gaskiya Salmat yau sai gaba na ke fad'uwa na zata Ustaz Lukman zai sanya ni a cikin masu karatun satin nan". "Tabbb! Ai kima shirya kinsan satin sama dole za ki shigo a cikin wa'anda za su yi". "Ni fa abinda naso su bar mu muji da karatun haddar mu tunda lokacin musabak'a na k'aratowa". . "Lallai ma Zajla kin kai, kawai kije kiyi ta bitar haddar ki sannan ki zauna da shirin fitowa larbar sama karatu gaban ko wa". "Muguwa kawai tunda kin ga kin yi yau hankalin ki ya kwanta ai zaki rik'a kayar min da gaba", tana maganar had'e da kai mata dundu a bayan ta. "Gaskiya kar ki tayar da hankalin ki abin baida wata fargaba kawai dakin fito dakewa za kiyi, kuma kar ki rik'a kallon mutane ki nok'e kan ki kawai". "Shikenan Allah yakai muna rai yasa fargaba ta fice min kamin ranar". "Ameen", ta amsa a gajarce. Da hakan har suka k'araso gida, a tare suka shige gidan su Salmat d'in saboda wannan k'a idar ta ce in sun da wo daga islamiya gidan su Salmat take zama har sai Baban ta sun k'are hira sannan ta fito su shiga gida. ** Cikin 6acin rai ya shiga d'akin meeting d'in wanda sanadiyyar hakan kowa ya sha jinin jikin sa. Hakan akayi meeting d'in rayuwar sa 6ace wanda mataimakin shi ne Imran ya jagoranci komai har aka k'are. Bayan bak'in sun wuce ne wani cikin ma'aikatan ke ba da shawara kan ce wa me zai hana ayi musaya da wa'ancan bak'in a basu fata suko su bada ire-iren takalma, jakunkuna da sauran dangin kayan da ake sarrafawa da fata d'in?. Ya cigaba da ce wa "a tunani na hakan zai fi akan abada fatar su bada kud'i ko ya kuke gani?". Ya k'arashe maganar had'e da kallon mutane cikin nu na bajin ta kan shawarar da ya bayar. Kallon da mutane suka bishi da shi ne na alamar ba kada hankali, wasu kuma na tausayawa gare shi ya sa ya sha jinin jikin shi ya yi tsit. Ko wa ya yi zugum domin jiran me zai biyo bayan maganar da ya furta, saboda duk yanda aka zauna meeting ba bu mahaluk'in da ya isa yace tak ba tare da ya bashi dama ba, barrantana yau da ya shigo rai 6ace wanda ya hana yayi magana har akayi meeting d'in aka k'are. "Duk da ce wa kai bak'o ne a wannan ma'aikatar bazai hana hukunci na yahau kanka ba". Cikin damuwa Imran ya tari numfashin shi had'e da bashi hak'uri amma ina ya gama furta "na sallame ka daga yau". Hakan ya ta shi tamkar guguwa yabar gurin cikin mintunan da basu wuce uku ba. Durk'ushe ya yi gaban mataimakin A.K.A kuma babban aminin shi yana mai bada hak'uri had'e da furta "In har kuka sallame ni bansan ina zan dosa ba, da wannan aikin nake kula da mahaifiya ta da sauran k'anne na marayu". "Sai dai kayi hak'uri aikin gama ya gama duk nan ba wanda ya isa ya janye wannan hukuncin". "An samu matsala ne tun farko ba'a gaya ma tsarin shi ba shiyasa, ko ni nan da nake mataimakin shi kuma babban aminin shi indai a office ne ban isa yayi magana inyi ba har sai ya bani dama". Hakan sauran ma'aikatan suka rik'a bashi hak'uri had'e da fatan alkhairi saboda bakin alk'alami ya bushe, don shine mutum na bakwai da hakan ta kasance dashi tun lokacin da mahaifin shi ya yi ritaya ya bashi kula da company d'in, da hakan kowa ya Kama gaban shi. Mutum biyu ne suke tattaunawa akan matsalolin da ke faruwa a ma'aikatar. "Gaskiya wannan ma'aikatar ba ta nesa da rushewa, kaduba kaga yanda yaron nan ke shuka rashin mutunci son ranshi", cewar tsamurarren. "Tabb to ai abin gado ne haka mahaifinshi yake tsula tsiya lokacin da yana manager, don ni na rasa gane tsakanin d'an da uban wa yafi rashin mutunci", a cewar bak'in mutumen kakkaura. "To Allah yayi masu magani, kuma yaganar dasu". "Ameen". . . Hakan ya fad'o gidan ko sallama babu sanadiyyar wani huci da yake yi shi ala dole an 6ata mai rai fuska tur6une tamkar namijin zaki. Da saurin shi ya ta shi ya taryo shi yana bubbuga bayan shi, sanadiyyar ya k'i jinin jure damuwar d'an shi komi k'ank'antar ta. "Wa ya ta6a uba ga Dad kuma d'a ga Dad?, bazan juri ganin ka cikin 6acin rai ba komai k'ank'antar shi". Ruwa ya tsiyaya a cup ya d'ora mashi a baki ya kauda kai yana huci, d'ayan gefen ya mayar da cup d'in sannan ya sha kad'an ya kauda kai tamkar wani jinjiri. "Gayamin Babana meke faruwa, kuma wa ya 6ata ma rai?". . Mum baki ta sake tana kallon sarautar ubangiji, abu gwanin haushi. Cikin yanga tamkar wata mace ya kora mai abinda ke faruwa. "Yo banda abinka Son miye laifin wanda ya baka shawara akan cigaban ka?, kuma wai har za ka iya ta da hannu ka fallawa dattijon mutane mari", Mum ce ke wannan maganar cikin 6acin rai da fad'a-fad'a. "To shi dattijon titin uban sa ne da zai zo yana tafiyar yanga akai?", cewar Dad. "Wallahi dai ku bi duniya a sannu daga kai har yaron ka, shin kud'i hauka ne? Su talakawan su sukaso ganin Kansu a hakan? Ku da kuke hakan siya kukayi aka baku gyara?, bai dace ka rik'a nunawa yaran nan gatan da yazarce misali ba". "Mu shiga daga ciki Son, saboda ta fara wa'azin nan na ta da take zama alarammar kan ta taja kuma ta fassara", hannun shi ya rik'a suka haura sama sai bedroom d'in shi. "Mum wannan abin fa ya kusa yawa, miye laifin wanda zai kawo cigaba akan lamurran ka da Brother zai yanke wannan d'anyen hukuncin". "Rufamin baki ai duk halayyar ku iri d'aya ce ku ne masu uba mai kud'i to wallahi ina guje maku ranar nadama saboda wannan abin ba gata ne uban ku ke nuna maku ba", cikin fad'a sosai ta k'arashe maganar. "Kin san dai Mum na d'ara Brother don bazan yi abinda ya aikata yau ba". "Ku dai kuka sani, Allah ya ganarda ku daga ku har uban na ku don wallahi rayuwar ku kanta abar tausayi ce, don mutumen da baisan darajar d'an Adam ba yana cikin matsalar rayuwa, komai za kuyi ya kamata ku rik'a duba cancantar abin". "Kullum game da tarbiyar ku tufka nake yi mahaifin ku na yiman warwara, a tunanin shi wannan gata ne". "Mum tunda munsan girma da darajar ku ai ba muda laifi, dama ca akayi mu girmama iyayen mu". "Sai akace ku taka duk wanda kuke so wannan shine dai-dai a cikin aya da hadisin Dad d'in ku?, wato mu ne mutane saura dabbobi ne a gurin ku". "Mum ba kya ga newa ne, shi fa Dad raini da wulak'anci ne bai d'aukar mana ba shiyasa kike ganin tamkar wulak'anta mutane muke yi, amma ba hakan bane". "Mum fa su mutane ba ka iya masu idan kayi sake sai su ta ka ka son ransu". Mugun kallon da ta bi ta dashi ne yasa ta ja

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38