Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Luk'man. Saman katifa ya je ya kwanta yana sauraren ta har ta kai matsaya ta ajiye K'ur'anin sannan ta yi addu'o'in ta ta shafa inda shi ma Alamein ya taya ta shafawa. Sallayar ta ninke ta ajiye ta had'a K'ur'anin ta da littattafan ta na azkar ta ajiye, sannu da zuwa ta yi mai wanda bai ko samu damar amsawa ba sai fararen idon shi daya bi ta dasu. Towel ta d'auka ba tare data cire kayan jikin ta ba ta fad'a toilet, jimawa ta yi gurin wankan saboda ba taso ta fito ta tarar dashi a d'akin. D'aure da towel sanye da hijab d'in ta ta fad'o falon sai kuma ta ja ta yi turus sanadiyyar ganin inda ta barshi bai tashi ba, sai ma wayar ta daya janyo yana latse-latse, basarwa ta yi ta wuce saman kujerar ta da take d'inki ta janyo jakar kayan kwalliyar ta tana shafa mai. Tausayin ta ya ji ya tsirga mai, ba akan komai ba sai don ganin kowace Mace mai ji da kanta in tayo wanka saman mirror take zama ta yi kwalliya sa6anin ita data zauna saman kujerar keken d'inki. Jin shi kawai ta yi ya rik'o jakar yana mayar da kayan cikin jaka, sannan ya rik'o hannun ta ya ja ta sai d'akin shi, galala ta saki baki ta bishi tamkar rak'umi da akala, bai tsaya ba sai gaban mirror d'in shi, ita ko ya janyo kujerar ya zaunar da ita, "daga yau ga gurin kwalliyar ki kuma ga d'akin ki", daga hakan ya juya ya koma d'akin ta. Akwati nan ta ya janyo yayo d'akin shi dasu, baki kawai ta saki tana kallon shi har ya gama kwaso kayan ta kaf ya kawo d'akin nashi, har lokacin bata samu motsawa daga yanda ya ajiye ta ba. "Bara in maki kwalliyar in ba zaki iya ba", kayan ya fitar na kwalliyar ta ya jera saman mirror d'in, kiciniyar cire hijab d'in ta ya rik'a yi hakan ya sa ta daddafe jikin ta, tana rok'on shi yabari ta kimtsa da kanta. D'akin ta ya koma domin ya bata guri ta samu sakewa, saman katifar ya kwanta yana kallon videos na d'aurin d'ankwali. Mamaki ne ya ishe ta na Alamein, tamkar ba shi ne yake hantarar ta yana kira mata dak'ik'iya kuma jahila ba, da mamakin shi fal a ranta ta kimtsa ta saka riga da siket d'in ta na atamfa sannan ta fito domin taci abinci. Motsin da ya ji falo ne ya tabbatar mai da fitowar ta, hakan ya fito daga d'akin ya ganta zaune falon su ta saka filet d'in abinci tsakiya tana ci. Hannu ya saka suka rik'a cin abincin tare, sai satar kallon ta yake yi yanda yake ganin take tsantsara kwalliya kamar wacce ta shiga makarantar make up, gano cewa neman magana yake so ya sa ta k'yale shi har suka cinye abincin, na shi dake saman dining table ya d'auko ya zuba suka koma ci, da hakan ta tashi ta wanko hannun ta sannan ta fad'a toilet ta yo brush, d'akin shi d'in ta zauna saman kujera bayan ta d'auko wayar ta ta kunna data ta hau whatsap. Da hakan ya risk'e ta tana charting ya fad'a toilet ya yi wanka, d'aure da towel ya fito inda take satar kallon shi, mutum ne dogo ba sosai ba mai faffad'an k'irji sai dai ba za'a ce mai mai k'iba ba kuma baza'a ce mai siriri ba, fari ne ba sosai ba yana da hanci har baka, sajen fuskar shi ke k'ara fitar da kyawon shi had'e da fararen idon shi tamkar madara, sumar kan shi bak'a ce wulik ta kwanta tamkar ta Fulani, ya fi yanayi da larabawan Sudan. Firgigit ta dawo hayyacin ta sanadiyyar ruwan kanshi daya sharto mata a fuska, cikin jin nauyi ta nok'e fuskar ta tana latsar wayar ta, "ko in zo ki taya ni Shafa mai ne, na ga hankalin ki ya tafi a kallo na, kinga sankacecen saurayi", yana maganar ne cikin zolaya da kashe mata ido d'aya, still kasa tayar da kan ta ta yi sanadiyyar kama ta da ya yi tana yi mai kallon k'urilla (Zajlah kar ki bada irin su Anty Sis, Hauwa Jidderh, Salmatun Innah, Namcy Sardeeyer, da Wamsyl, masu cewa sun matsu Alamein bai shigo hannun ki ba, toh fa ko reshe ne zai juye da mujiya ke ki shiga tarko?, lolx). Turare kawai ya fesa ya saka jalabiyar shi mai ruwan anta, ya hau gado ya kwanta, ita ko ta jona wayar ta a charge ta kwanta saman three sitter. "Wannan ne kuma baki isa ba, saboda haka ki taso ki dawo saman gadon ki kwanta, ba wani abu nace zan maki ba". Ji rainin hankali, to me tace zai mata, ina ga in na k'yale wannan mutumen rainin zai yi yawa, cikin zuciyar ta take wad'annan maganganun. Gaban ta kawai ta ganshi yana batun sunkutar ta, da hannu ta yimai alama sannan ta kalle shi sama da k'asa "ina ga ka hutar da kanka da shiga mu'amalar kucaka kuma jahila, saboda gudun kar ta6on ta ya shafe ka". Daga hakan ta juya ta bashi baya ta yi kwanciyar ta. Tamkar gunki haka ya dask'are a gurin, lallai tabbas magana zarar bunu ce, kuma yana da tabbacin watarana za ta maida mai amsa, wannan ba damuwar shi bace indai za ta hak'ura ta yafe mai laifin shi a gare shi, hakan dai ya ja jiki ya je ya kwanta. **** Yau ne aka d'aura auren Saudat Kabeer Aminu da Fadeel Ibrahim mai dala, inda aka yiwa Saudat abubuwa cikin tsaka tsaki na masu rufin asiri, sai dai fatar d'orewar zaman lafiya. Sai ranar da aka kai tane Zajlah tasan Fadeel ne da ya ce yana son ta, tuna abinda ya faru tsakanin shi da Mum ne yasa jikin ta ya k'ara sanyi da lamurran duniya had'e da ikon ubangiji. ............. Yau ne mummunan labari ya risk'e su cewa Allah ya yiwa Alh Ibrahim rasuwa akan hanyar shi ta zuwa Abuja daga sokoto ya yi hatsari, inda suka jajanta abin had'e da yimai murnar sauke nauyin marayin Allah dake saman kanshi, addu'a suka yi mai inda Mum taso ko Alamein ne yaje, sai dai a labarin shi bai gaya masu takamemen address d'in gidan suba, Allah ya gama rai da gafara, Amein. *** 6angaren Baban Zajlah yana ganin bud'i a kasuwancin shi saboda yanzu shine shugaban masu kayan gwari, don ya daina kasawa a table sai buhu-buhu da yake d'aukowa ana siya gare shi, amincin su sai k'ara k'arfi yake yi tsakanin shi da Malam Inuwa sun zamo tamkar y'an uwa na jini. *** Cikin Salmat yanzu ya kai wata bakwai, yanzu laulayi ya rage sai d'an banzar kwad'ayi dake taso mata inda Imran ke tarairaya da ita tamkar k'wai. Yusrah na mak'ale da na tacikin d'an wata biyu wanda ba kowa yasan da zaman cikin ba saboda ba wahala yake bata ba. *** Alamein ne zaune k'asa dirshan inda Zajlah ke zaune saman kujera tana fuskantar shi sai wani cin magani take yi, ta yi wanka ta ci ado tamkar wacce za ta je bikin aure sai cingum take tauna yana bada k'as-k'as. "Bazan iya jure wannan garawar da kike min ba, Zajlah

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38