Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba.....' tsawa Jahan ya daka mata da cewa "Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaɗa miki shegen duka," Abbansu yace "Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana," shiru su kayi gaba ɗayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce, Shin ina haroon duk wannan abun dake faruwa yana a tsaye fitowarsa kenan, gaba ɗaya ransa ya gama jagulewa mamakinsa yarda akai yarinyar ta bayyana kanta A matsayin mace bayan bai idasa cimma burinsa ba, na tsoratar da ita, Amma ganin yadda su Jahan suka fusata yasa shi jin daɗi aransa burinsa karsu amince su tada 6alli sai anyi mata horo sannan a koreta shi kuma zaiyi amfani da wannan damar wurin ƙuntata mata, tsayawa yayi da murmushin mugunta a fuskarsa don yaga ya ƙarshen bada'ƙalar zata kaya, Daga shi sai gajeran wando fari ajikinsa tsaye ruƙe da ƙugu, ɗayan hannunsa na ruƙe da Brush da alama ma daga toilet ya fito, burinsa yaji mai Abban nasu zai ce, gyaran murya Abbansu yayi sannan ya soma cewa "Na riga da nasan komai game da yarinyar! Domin junaid ya jima da sanarmun komai agame da ita, duk abunda junaid ya nuna yana so aduniyar nan koma menene shi zan amince dashi, Junaid ya nuna cewar yana son Zaman yarinyar nan agidan nan, don Haka Na AMINCE masa,!" Cikin mamaki suke kallon abban nasu, Haroon kuwa tuni yayi wata irin raxana har Brush ɗin dake hannunsa ya faɗi ƙasa sbd jin abunda Abbansu yace, Murmushi kawai junaid ke saki, kallonta Abban su yayi tare da cewa "Ya Sunan Ki"? Sehrish dake tsaye agabansa idonta cike tab da kwalla duk ta tsorata murya na rawa tace "SEHRISH" Jinjina kai Abbansu yayi tare da sa hannun shi ya shafa gefen fuskar sehrish yace "Daga yau Ba sunanki Sehrish ba," cikin mamaki suke kallon Abban nasu, itama sehrish ɗin kallonsa take tana jira taji sunan daya canza mata, azmee kuwa Alhamdulillah kawai take faɗi aranta, "Kinsan menene sunan ki daga Yau"? abban nasu ya faɗi yana kallonta, Cikin sanyin murya Reesh tace "a'a". murmushi Abban nasu yayi sannan yace "daga Yau sunanki *SEHRISH SALAHUDDEEN HUSSEIN ABBAN SOJOJI*" 😇😇😇 Sakin baki su kayi suna kallon Abban nasu Duk wannan Abun dake faruwa akan idon SGR wanda ke saukowa down stairs jikinsa na sanye da t-shirt mai gajen hannu baƙa, sai dogon wando fari, sun bi shape ɗin jikinsa ya fito Handsome stylish ɗinsa, ya ɗaure sumar nan ta baya ba ƙaramin kyau yayi ba, a hankali yake tattaka steps ɗin cikin tafiyar nan tasa ta majiya ƙarfi, duk suka ɗago suna kallon shi................ __________________________________ Ku hanzarta yin Payment don in na tashi dakatawa gaba ɗaya ne wanda suka shirya suyi mun magana direct = 08103884440*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* *🔥The Father Of Soldiers🔥* ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖 *Story & Written by* *Hafsat Bature Muhammad* ~💋BOSSLADY💋~ *💫LAFAZI WRITERS ASSOCIATION 💫* *Abban Sojoji part 2* *EPISODE 5-6* Ida sa iso wa inda suke sgr yayi idonsa yakai kan Jahan daya zare belt ruƙe a hannunsa, tunkan yayi magana jahan yayi hanxarin mayar da belt ɗinsa, mayar da idonsa yayi kan Abban nasu tare da cewa "Gm dad fatan an tashi lafiya," murmushi Abban su yasaki da cewa "Lafiya Lou son ina fata kaima haka," Sgr yace "Alhamdulillah," sannan ya samu wuri ya zauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin, kowa so ya ke yaji mai Babban yayan nasu zai ce, musamman haroon burinsa Sgr yace bai amince da zamanta ba, don yasan in dai yace hakan to Zaman sehrish ya ƙare a gidan, Ita kuwa sehrish hankalinta kwance saboda tasan yarda su kayi jiya dashi haka azmee ma, gyaran murya sgr yayi kafin yace "tsayuwar me kuke yi"? Ya tambaya yana kallon su jahan Ayaan da kanal yusif, koma wa su kayi kowa ya xauna junaid ma yasamu wuri ya zauna, sai Abban nasu dake tsaye sehrish na agabansa yaci gaba da cewa "daga yau kin zama ƙanwarsu kema ƴa' ce acikin gidan nan, duk wani abu da uba keyi ma ƴarsa nima zan miki shi, kuma duk wani abu da junaid zaiyi acikin gidan nan kema zaki iya yin shi, kuma duk wanda yayi yunƙurin 6ata miki acikinsu ki sanar mun zaki ga yarda zanyi dashi," Zuru su kayi suna sauraron Abban nasu, sehrish kuwa murmushi kawai take saki koba komai yau tasamu Uba wanda zatayi prouding dashi a faɗin duniya, ɗago idansa yayi ya kalli Babban yayan nasu, wanda azmee taci gaba da saving ɗinshi breakfst ya kira sunan shi "RAFAYET" amsa wa yayi da "Na'am Abba," batare da ya juyo ba ya kalle su, Abban yace "Ina fata kaji komai ga me da yarinyar nan ? bansan ko kana da abun cewa ba" ya tambaya yana kallonsa, kowa ya saurara don jin ta bakinsa, haroon Allah Allah yake akan Babban yaya karya amince da zamanta, Boss man ɗin sai da ya gama sipping Coffee ɗin dake hannunsa a natse sannan yace" Umarninka Shine abun bi" amsar da ya bayar kenan, wani irin farin cikine yaci ka Abban nasu saboda shi da yake tunanin zai ƙiya gashi ya amince da duk jawabinsa kai tsaye ma yace Umarninsa shine abun bi, wato duk abunda yace game da yarinyar ya amince, "Kufa kuna da Abin cewa"? Abban nasu ya tambaya yana kallom su, cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Abba ae magana taƙare kawai tunda Babban yayan mu ya amince mu su wanene da baza mu amince ba"? Wannan maganar tasu tasa Azmee yin ƴar dariya ƙasa ƙasa, Jinjina kai Abban su yayi sannan yace "hakan yayi mun, sannan ko da gigin wasa ban amince wani ya cutar mun da ƴa ta ba," "An gama magana Abba" suka bashi amsa atare yace "Yawwa haka nake son ji, sannan ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda ke faman sakin murmushi tayi zuru tana cizar akaifar hannunta da takai bakinta, ba kowa take tunani ba face Haroon yadda zata Zazzaga mashi rashin mutunci, dama taci alwashin hakan Muryar Abban su ce ta katse mata tunanin nata da cewa " daughter ki zauna kiyi breakfast tare da Abban ki da kuma ƴan uwanki," ɗan zaro ido sehrish tayi jin yace zata zauna taci abinci acikinsu cikin mamaki tace "Abba anan," tayi maganar tana nuna dining table ɗinsu, "Eh nan nake nufi" ya bata amsa sannan ya ruƙo hannunta gavan ta na faɗuwa suka samu wuri suka zauna tana gefen Junaid Abbansu kuma na gefenta sun sa ta tsakiya, Babban yayansu kuma Na a side ɗin Abban nasu, ta hannun dama yayin da suke facing Ayaan Jahaan da kanal yusif su da suke hannun haggunsu, "Azmee ke ma ki samu wuri ki zauna A cikin mu," abban su ya faɗi yana kallonta , da fara'a a fuskarta tace "ngde ssae Abba, amma ni nafison a barni a iya matsayi na, nafi jin daɗin kasancewata haka, dama damuwa ta Sehrish ce gashi kuma ta samu Ƴanci ka ƴanta ta, Allah ne kaɗai zai iya saka maka, haƙiƙa kai na musamman ne ka kasance ɗaya daga cikin mutanen da ake Alfahari dasu aduniya kuma ake alfahari da Ƴa'ƴansu kowa burinsa yayi koyi da kyawawan ɗabi'unka da

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47