Chapter 41
Chapter 41
girgiza kai tace "Ba wannan zansa, basu son cewa ni musulma bace, taya zansa wannan gajeran skirt ɗin cinyoyi awaje kamar ƴar christiana," tayi maganar tana yatsina fuska, buɗe na biyun tayi riga ce tare da skirt pencil ba ƙaramin ɗame jikin mutun zaiyi ba, "Kamar dae wadda zata club," ta faɗi tana ƴar dariya, na ƙarshen ta buɗe riga ce tare da dogon wando, duka uniform ɗin suna da Top wadda ake sanyawa daga sama bayan an zura rigar sai kuma guntun hijab wanda daƙyar ya dire kafaɗa, "Kwarama wannan zasu fi dacewa dani," ta faɗi tare da hanzarin komawa gaban mirror sai da ta kammala shafe jikinta da body oil tabi ta feshe shi da turare ko'ina yakama ƙamshi sannan ta koma gaban gadon tana zura uniform ɗinta, lokacin da ta kammala zura kayan duka ta kalli kanta a mirror sai da taji gabanta ya faɗi saboda yadda kayan suka hau jikinta su kayi mata wani irin kyau, Rigar white colour ce wandon kuma Maroon colour launi ɗaya da Top ɗinta, jujjuyawa tayi agaban mirror ɗin sannan ta sakarwa kanta murmushi, sai da tagama shiriritar sannan ta ɗauko takalmanta, tsayawa tayi tana ƙoƙarin zura safa a ƙafarta, ta aza ƙafar asaman kujerar gaban mirror tana gyaggyara safar, Azmee ta shigo ɗakin da sallama tana yin arba da sehrish ta soma washe baki tana cewa La!la! Irin wannan kyan haka, Masha Allah gaskiya uniform ɗin nan ba ƙaramin kyau su kayi maki ba Sehrish sai kace donke akayi su," Murmushi kawai Sehrish ke saki tana ɗan kallonta a lokacin ta kammala sa safar da takalmin a ƙafar daman ta, saura ta hagun zata sanya mawa, "aunty azmee ina kwana fatan kun tashi lafiya," ta faɗi tana aza ɗayar ƙafar saman kujerar , Azmee tace "Lafiya lou Alhamdulillah, naga sai faman shiri kike yi, maganar breakfast ba? "Aunty azmee lokaci zai ƙure ne, idan nadawo zanci," ta faɗi tana zura safa a ƙafar hagunta, Azmee tace "Kin ta6a ganin inda akaje ɗaukar karatu da yunwa? gaskiya bazaiyiyu ba, akwai sauran miyar jiya na ɗumamata saina haɗa maki da dankalin dana soya kici, bari na kawo maki" ta fadi tare da juyawa ta fuce cikin sauri bayan wasu mintina sai gata ta dawo hannunta ɗauke da plate, soyayyan dankalin ne aciki tare da jar miya, ajiye mata tayi asaman side drawer ɗinta, sannan ta koma ta ɗauko mata kayan tea don ta haɗa tasha, "Nagade sosai Aunty azmee da kulawarki," sehrish ta faɗi a lokacin ta baro gaban mirror ɗin, wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana cin breakfast ɗinta, yayin da azmee ta fuce tana cewa "ki hanzarta ki shirya kafin Junaid ya fito," ta amsa mata da "Toh," A can ciki kuwa tuni junaid ya farka saboda ya tashi da wuri ya sanya alerm a wayarsa, shaf shaf yayi wanka ya fito ya kimtsa cikin pakistani riga da wando farare amma anyi masu ado da stone launi daban daban ajikinsu, ba ƙaramin kyau yayi ba, bin jikinsa yayi ya feshe shi da Spice bomb, sannan ya gyara sumar kanshi, gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa yace "Nima kaina nasan cewa Ni kyakkyawa ne, Son kowa ƙin wadda ta rasa, Allah kaɗai yasan ƴan matan da suke crushing akaina," ya faɗi yana tsumbula yatsansa na tsakiya a dimple ɗin fuskarsa daya Lotsa, daga bisani ya ɗauki key ɗin motar shi tare da wayarsa ya fito daga ɗakin, cikin hanzari ya sauko down babu kowa saboda duk basu tashi daga bacci ba, wuri ya samu asaman Royal sofa ɗin dake a falon mai mazaunin mutun 3 ya zauna yana jiran fitowar sehrish, wayarsa ya shiga daddanawa, message ya tura mata cikin wayarta, na cewa yana jiranta ta fito, a lokacin ta kammala kur6ar tea ɗin data haɗa, message ɗin junaid ya shigo mata karantawa tayi "Am waiting for u reesh,' murmushi ta saki cikin sauri ta miƙe tare da ɗaukar guntun hijabin ta zura ajikinta, sannan ta ɗauki School bag ɗinta ta ɗan sagala hannun jakar a kafaɗarta, sai da ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin, kai tsaye ta nufi falon tunkan ta ƙarasa junaid ke kallonta baki asake, Ganin hakan yasa ta sakin dariya, ƙarasa wa tayi wurinsa tare da tsaya agabansa ta ruƙe waist ɗinta tace "Nayi kyau,"? Cikin mamaki yace "Reesh irin wannan kyau haka? Anya karfa malaman makarantar su rikice? innalallahi," ya faɗi tare da aza hannunsa akansa, ɗan bubbuga ƙafarta tayi tare da cewa "ka tashi mu tafi junaid har 8:30 fa tayi," Mamaki tayi ganin yarda yake kallonta hannunsa yakai tare da cafko wutsiyar gashinta da ta sauko har tsakiyar bayanta yace "Sehrish jibi fa? Babu wani dogon hijabin ne sai wannan? Taya zaki bar gashin nan haka bainan nasi? Kowa ya kalla? Sai lokacin ma ta ankara sam ta manta bata sanya ribom ba ta ɗaure gashin, dafe kanta tayi tare da cewa "kash ! Wlh mantawa nayi ban ɗaure gashin ba, kuma fa in na sanya ribbom gyaran gashin da akayimun zai 6ace," tashi junaid yayi tare da ruƙo hannunta yace "Mu shiga cikin ɗakin na ɗaure maki shi, nasan yarda zanyi batare dana 6ata maki gyaran gashin ba," bin shi tayi suka wuce ɗakin nata, duk wannan abun dake faruwa akan Idon haroon sam basu ankara dashi ba, tun fitowar sehrish yake tsaye ruƙe da qugu daga shi sai gajeran wando fuskar nan a murtuke kamar ta shanu, jinjina kansa yayi tare da cewa "Wato ni waccen ƴar shilan zata raina ma wayau, in na ta6a jikinta taita ƙyamata amma gashi junaid har wani ruƙe hannunta yake yi, hada su shiga ɗaki ko uban mi zasu yi aciki,"? Ya tambayi kansa can kuma ya saki wani irin shu'umin murmushi yace "Wannan babbar dama ce agare ni ! Zanyi amfani da ita wurin gur6ata sunanta acikin gidan nan, Zan ƙala mata sharrin cewa ta koyama junaid lalata, kuma na kama su hannu dumu-dumu, " fashe wa yayi da wannan mahaukaciyar dariyar tasa kafin ya juya ya nufi hanyar komawa dakinsa yana cewa "Yarinya kin gama yawo acikin gidan nan, sai kin gane baki da wayau !," yana tafiya yana sambatu har ya shiga ɗakinsa, Junaid kuwa bayan sun shiga ɗakin sehrish ta cire hijabin nata agaban mirror suka tsaya, ribbom ɗinta dake ajiye saman mirror ta ɗauko tare da miƙa masa, hannu yasa ya kar6a sannan yashiga kiciniyar tattara gashin kanta donya ɗaure mata, Murmushi ta dunga saki saboda jinsa yadda junaid ke faman nishi aranta tace"junaid ba ƙaramin rago bane, yanzu gashin kan nawa ma yagaza ɗaure wa, shi dai sai kace ba namiji ba, sam babu wannan karsashin na maza atattare dashi...... Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Gulma ta kike ko"? Cikin sauri tace "a'a ni na isa," Murmushi kawai yayi, daƙyar yasa mu ya tattara sumar kan sehrish ya ruba ta biyu ya haɗa ya ɗaure," sannan ta mayar da hijabin nata, "Gaskiya junaid ka iya dabara, gashi nan yanzu babu gashin bai leƙo ba," ruƙo hannunta yayi tare da cewa "Mu tafi ko," cikin sauri ta bishi suka fito da hanzari suka fuce, Buɗe mata motar yayi ta shige sannan shima ya zagaya yashiga ciki, yana a driver seat ita kuma tana a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47