Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
Download Book

zayyana mata abunda ya faru tsakaninta da Babban yaya daga farko zuwa ƙarshe Baki washe azmee ta ɗaga hannunta sama tana cewa "Alhamdulillah ! Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala naji daɗin wannan lamarin sehrish domin kuwa Babban yaya shine nafi ji dama, gashi kuma cikin sauƙi ya amince wayyo Allah murna bansan inda zan sa kaina ba don daɗi" cike da jin daɗi azmee ke magana fuskarta a washe Sehrish tace "Amma aunty azmee su fa sauran kina ganin zasu amince in suka sani"? Ni ina tsoran ta yarda zan fara fitowa a matsayin mace cikin gidan nan," tayi maganar murya asanyaye tana kallon azmee Ƙarasawa azmee tayi ta dafa kafaɗarta sannan tace "Sehrish matsalarki tazo ƙarshe! tun da har babban yayansu ya amince ba ki da sauran damuwa, Abbansu ne kawai zamu jira muji ta bakinsa, yanzu abunda nake so dake kije kawai ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamu ga yadda badaƙalar zata kaya idan matasan gidan nan suka ga tukur mai aikinsu a matsayin Mace lallai akwai tashin hankali, " azmee tayi maganar da dariya a fuskarta, sehrish kuwa dafe saitin zuciyarta tayi tana zazzare ido tace "Allah sa su amince suma," "Insha Allah" azmee tabata amasa afterwards suke yi sallama, sehrish ta koma bedroom ɗinta cike da zullumi haye wa tayi saman gadonta, ta janyo pillow ta rungume tana sakin murmushi tunawa da haɗuwarsu ta yau da babban yaya, Allah kenan a daren nan Haroon ya ƙuntata mata, har tayi addu'ar sai Allah ya nuna masa Iyakarsa akanta, to yanzu ga Iyakar tasa nan muddin sauran suka amince da ita kuwa, taci alwashin sai ta Ci mutuncin Haroon 😡👊 A fili tasoma magana " gajan haƙuri kenan Irin na ɗan adam, yanzu da na kashe kaina da shikenan nayiwa kaina, ashe Allah yana dab da kawomin sauƙi arayuwata," ta faɗi tana faman murmushi wani irin nishaɗi take ji ayau , ta kuma cewa "Anya ma zan iya bacci kuwa? gashi ina fargabar mai zai faru gobe? kwara kawai nayi Bacci na goben tayi saurin yi, AYI TA, Ta ƘARE kawai🙅, In jalasa jalasa 😂 in Zahaba Zahaba shine kawai 😅😂😹😹😹 tana gama faɗan hakan bacci yayi awon gaba da ita, kai kana ganin yadda reesh ke bacci kasan tana cikin kwanciyar hankali, murmushi Hafsat Bature tayi tana kallonta wadda ke tsaye shigowarta kenan ta window tabiyo da suffar Farar Tantabara kasancewarta Aljanar sehrish, hannu tasa tajanyo bargo ta lullu6e sehrish dashi sannan ta 6ace 6aaat..............😇 ______________________________________ Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu? "Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa"? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido, Cikin sanyin murya tace "Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan," ta faɗi zuciya a karye Hosana tace "Dama Allah ya ɗauke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaɗai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaɗae ke son mu ko? Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me, Hosana ta ɗan 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba, Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace "Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an ɗauke daga nan an kaisa sama ? Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa "sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne"? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba...............wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi, Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace "Ya Allah hada sehrish za'a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari.....' dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin "Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za'ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji..............' jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana, "To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi," Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali Can tayi wani dogon tunani tace "Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna"? Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace "Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad," Shiru jahad tayi kafin tace "Akwai !!! Na tuna acikin wannan ɗakin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan ƴar lokar naga Memo da biro," Cike da farin ciki hosana tace "dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa," Miƙewa jahad tayi tana faɗin "Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in kika ja asirin mu ya tonu kashin mu ya bushe mu duka," Murmushi hosana tasaki tana cewa "sai dai in baki daɗe ba, kinsan ina jin tsoro fa nikaɗae anan," "Karki damu yanzu zan dawo," "To shikenan," hosana ta bata amsa, Ficewa Jahad tayi cikin sanɗa take tafiya babu kowa wayam sai hasken daya gauraye ko'ina, Wuce wa ɗakin tayi a hankali ta tura ƙopa tashige cikin hanzari ta nufi drawer ta zaro gidan farko ajikinta, anan taga memo ɗin da biron data gani, Fiddo su tayi jiki na rawa ta aza memon asaman drawer ɗin dayake ƙaramace, daga zukunne jahad ta soma bude papers ɗin sannan ta aza biro ta soma rubutu kamar haka _ya Omar naji ma inaso na faɗa maka halin da muke ciki, wlh bamu jin daɗin zama agidan nan, saboda basu son mu, uban aiki suke samu har bugun mu suke yi, dan Allah ya omar in kaga wannan takardar ka taimaki rayuwarmu kamar yarda kayi niya ka tafi damu inda kake rayuwa_ Kamar daga sama Jahad taji ance "Sannu da Ƙoƙari"!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!! Jin wannan maganar a bayanta yasa jahad dakatawa da rubutun da take yi, hankali a matuƙar tashe idonta sun firfirto azare, jikinta ya soma wata irin kerma, Tuni Zufa ta

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47