Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

harara ya watsa mata yana hura hanci, Azmee na isa jikin gate ɗin tace"Matsa ka gani junaid, ni bari in zama Namijin, ni kaɗai zan tura sa," Jin haka yasa junaid matsawa suka bata wuri don ta jaraba, gefen Sehrish ya tsaya suka zuba ido suna kallon azmee, Hannu tasanya sannan ta soma tura gate ɗin nan take ya tafi da gudun gaske ya ƙarasa zuge kansa, Zaro ido Junaid da sehrish su kayi cikin tsananin mamakin ƙarfi irin na AZMEE, A ruɗe junaid yace"Aunty azmee taya hakan ta faru? Ni nakasa turasa amma ke kina aza hannu gate ɗin ya buɗe," Murmushi azmee ta saki tare da nuna masa damtsen hannunta tace "Tsohon ƙashi kenan! ba irin naku ba na ƴan shila," Fashewa su kayi da dariya su duka kafin daga bisani suka koma cikin Motar, junaid ya shigar da ita cikin gate ɗin kai tsaye yayi parking ɗinta a harabar gidan *Shin Kuna tunanin Cewa Omar zai samu damar ɗauko su hosanna da Jahad daga gidan Aunty babba*?😟 Ku hanzarta yin payment 300 ne ga acct 3196407426 Bature Hafsat Muhammad first bank, sai aturomin shaidar biya ta numberta 08103884440, idan kuma recharge sai ayimun magana ta numberta,👍👏 [9/9, 4:03 PM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────EPISODE 19-20 ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️ *Mallakin Hafsat Bature Moh'd* ~BossBature~ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• bayan sun fito daga motar kai tsaye suka nufi hanyar da zata sadaka da babban falon gidan, Sehrish sai faman bin ko'ina take da kallo aranta tana cewa"tab ! Mace ta samu wannan amatsayin gidan aurenta, ae kawai ta bi mijinta sau da ƙafa, tabi da addu'a don ni gaskiya na mallaki wannan hamshaƙin gidan amatsayin gidana, ko ƙofar gida bana leƙawa sai in ta kama,' sai faman zancan zuci take yi har suka ƙaraso wurin wani bene mai kanannaɗa, hawa junaid yayi sannan azmee tabi shi, itama sehrish tabi bayansu, sai faman jinjina kai take yi tana cewa"lallaine Aljanna ta mai rabo ce," daker take tattaka matattakalar benen saboda gajiya don yana da ɗan tsayi, bayan sun kai ƙarshensa, wata haɗaɗɗiyar ƙopa ce wadda kai tsaye in ka bi ta zata sauke ka upstairs inda main falo ɗin gidan yake, key junaid yasanya yabude ƙopar sannan suka shiga cikinsa,wurin ya haɗu an ƙawata shi ahaka ma wai ba furnitures acikinsa, to inaga ansanya mashi kujeru da sauran abubuwan ƙayatarwa, Batare da 6ata lokaci ba, sehrish ta buɗe handbag ɗinta, memo ta ciro tare da biro, junaid da azmee suka dunga dudduba falon suna karanto mata abunda za'a buƙata acikinsa, ita kuma tana rubutawa acikin memo ɗin hannunta, bayan sun gama da falon kaf sun lissafa duk wani abu da za'a sanya mashi, Sannan acikin babban falon akwai bedrooms guda biyar ƙofofinsu na acikin falon, ciki suka shiga suna dudduba ɗakunan masu girman gaske, nan ma azmee ta faɗa ma sehrish duk abunda za'a buƙata na furnitures ta rubuta, daga nan kuma suka sauko downstairs stairs shima bene ne zai biyo dakai ƙasan, Agajiye sehrish ta kalli junaid tare da cewa "dan Allah wannan wane irin gidane haka junaid? Nafa rikice wlh, mun shigo ta Upstairs yanzu kuma ga mu a downstairs yanzu ta ina zamu bi mu fita? Ba dai sai mun koma upstairs ɗin ba don wlh ƙafafuna a sanƙare suke hawa stairs ko wahala, Junaid da fuskarsa tayi jawur ya gama cika ya 6atse saboda uwar yunwar da yake ji, ga gajiya duk ta baibaye shi, daker ya iya cewa "wannan ne damuwarki, Ni ta cikina nake yi yaushe har muka kammala muka koma gida ni daga nan ma, ba abunda zan ƙara yi Allah, ku je ku ƙarasa sauran aikin in kun kammala kuyimun magana," Wuri yasamu a sitting room ɗin dake a downstairs saman wani benci ya zauna, da alama tun lokacin da akayi ginin gidan aka barsa, don akwai tarkacen kayan aikin da aka bari acikinsa, Acikin sitting room ɗin akwai ƙofofin bedrooms guda biyu, sai kitchen mai girman gaske, sunsha aiki kaf sai da suka zagaye gidan bayan sun tabbatar sun bincika ko'ina sun dudduba abunda ya dace duka kaf sehrish ta rubuta a memo ɗinta, Ana cikin kiran Sallar magrib suka bar gidan kowa agajiye, Suna ƙarasawa gida daga babban falon kowa ya wuce ɗakinsa, shaf shaf junaid ya tu6e kayan jikinsa ya faɗa toilet donyi wanka, haka itama sehrish tana shiga ɗakin nata bayan tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado tare da memo da biron duka, kai tsaye ta tu6e Jalbab ɗin dake ajikinta, ta cire rigar jikinta, cikin sauri ta faɗa toilet wanka tayo tare da Alwala, tana fito ta ɗaure da towel ta bude wardrobe ta ciro wata doguwar rigar mara nauyi ta zura, daker tasamu tayi sallah bayan ta kammala ta baje saman gadonta, bata ƙara sanin meke faruwa ba sam ta manta da batun jera abinci adining, gana babban yaya da zata kai mashi bacci kawai take kwasa, Azmee ce kawai tayi ƙoƙarin fitowa bayan ta canza kayan jikinta, tunda ta leƙa tasamu sehrish na jan minsharin wahala, bata tashe ta ba kitchen kawai ta wuce ta shirya masu abincin dinner ɗinsu ta dunga kaiwa a dining tana jerawa harta kammala, Daker junaid yasamu ya fito sai da yaci ka cikinshi sannan ya wuce masallaci yin sallah, Sai bayan sallar isha'i sannan sehrish tafarka tana faman zazzare ido, agogon bangon ɗakinta ta duba kusan ƙarfe goma da rabi cuf, arazane ta miƙe tana faman dafe ƙirji tuna cewa bata kaima SGR dinner ɗinsa ba, cikin sauri ta ɗauko mayafi a wardrobe tayi lagensa a kanta, sannan tafito dakin azmee tafara wuce wa don taji ko takaimasa, kwankwasawa tayi sannan ta jira ta buɗe mata, A lokacin azmee bacci takeyi jin bugun ƙofar sehrish yasanya ta, farkawa daga baccin nata, tasowa tayi ta buɗe mata ƙofa, Ganin sehrish yasa ta cewa "ashe kin tashi daga baccin? Lafiya naganki ko akwai wani abune? Sehrish tace "dama babban yaya na manta bacci yaɗauke ni ne, bankai masa ɗina ɗinsa ba, shine nazo na tambaya naji ko ankai masa," Azmee tace "Ae basu kai ga dawo cikin gidan ba Shi da Omar, pls kada ki koma bacci ko kuma ki sanya alerm na wayarki in sun dawo ki tabbatar kin kai masu abincinsu, sannan kada ki manta ki bama Omar list din da mukayi masa acikin memo dinki,' Sehrish ta amsa mata da cewa "to shikena insha Allah zan bashi, mu kwana lafiya," Tayi ma azmee sallama sannan ta fito ta wuce nata ɗakin, gefen gado tasamu ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ɗauko handbag ɗinta, wayarta ta ciro daga ciki sannan ta shiga dannata, Tunawa tayi da maganar Azmee da tace mata in zatayi amfani da data, wi-fi kawai zata kunna, Cikin sauri tasanya yatsanta ta janyo top of the screen din wayar ta, danna wi-fi ɗin ya kunnu, tsayawa tayi tana tunanin me zata fara yi da wayar yanzu, tana cikin tunanin nan taji ƙarar shigowar motocinsu cikin gidan kusan ƙarfe 11-30 na dare, mayar da wayar tayi saman bedside drawer ɗinta ta ajiye asamanta, miƙewa tayi tana jiran su kammala shigowa sai taje ta kai masu, sai da tabari 12 tayi dai-dai a lokacin tasan sun kimtsa kowannansu

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47