Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za'ae mu dakatar dashi ba.....' ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama, Hankali atashe aunty babba ke cewa "Kisa wayar handsfree," cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce, Bayan ya amsa mata sallama yace "Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki," yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu, Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare, Murya tamkar zatayi kuka tace "Mommy duk ke kika ja mana wannan bala'en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,' Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace "hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,' Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai, Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah 😥 ______________________________________ Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa'ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin "Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya," Daga can 6angaren gwaggon katsina tace "Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa'ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu, Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace "Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya," Ajiyar zuciya tasaki kafin tace "Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana," omar yace "Goggo kin manta suna a kaduna,ae gidan Yaya ishaq nakai su..." Kamar tana agabansa ta zabga salati tana cewa "La'ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa'ƴan abusufyan ɗina suke ciki . ......fashe masa da kuka goggon katsina tayi, Sam omar ya gaza gane ma goggon tasu, a tunaninsa haukan nata ne ya tashi, in ba haka ba ina matar ishaq keda aibu har haka, gashi kuma ta fashe mashi da kuka, cikin rarrashi yace "Calm down your mind Goggona, ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna cikin ƙoshin lafiya, yau ma nake shirin zuwa in dubo su,' Cikin shessheƙar kuka tace "To shikenan amma dan Allah Omar nidai nafison su bar gidan matar nan, adawo mun dasu nan in basu kulawa kamar yadda na kula da mahaifinsu tun yana yaro," Murmushi Omar yasaki sannan yace "Insha Allah my aunt don't worry ur self abt them, suna Lou and insha Allah in naje zan basu waya ku gaisa kiji muryarsa may be u will be calm," "Shikenan Omar kada ka manta sai na jika," Ya amsa mata da cewa "Insha Allah" daga bisa ni su kayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da Cin breakfast ɗinsa, Acan ciki kuwa tuni Sehrish ta shirya kayan mazan ne ajikinta tunda su ke gare ta, hijab kawai tasanya ajikinta brown colour, azmee kuwa dama atampa ce ajikinta, Mayafi kawai ta lullu6a a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, suna a babban falon sai ga junaid shima ya sauko, bin shi da kallo sehrish tayi jikinsa na sanye da suits baƙaƙe kamar ma'aikacin banki, yayi kyau sosai acikinsu abun sai wanda yagani, sai faman murmushi yake saki da white teeth ɗin nan nasa kamar gonar auduga, "Gsky junaid bazan iya jerawa dakai ba, Irin wannan kyan haka," sehrish ta faɗi tana nuna shi da hannu, Ƴar dariya junaid yasaki kafin yace "duk kyan da zanyi bazan fi ki ba, ke fa maca ce, ni kishi ma nakeyi don nasan yanzu zaki fara ɗaukar wanka da zarar munyi Siyayyar nan," Murmushi sehrish tasaki ita kanta har ta hango ta cikin Gown ta gayu wow, azmee ma murmushin take saki, atare suka jera suka fuce, a cikin Motar Junaid haɗaɗɗiyar gaske, Shi ke driving yayin da sehrish ke a gefensa sai faman fira suke suna zuba, azmee na a back seat tana sauraron su wani lokacin ma tana sa musu baki suna firar atare, suna ta tiƙar dariya abinsu gwanin burgewa, har suka isa katafaren shopping mall ɗin mai matuƙar girman gaske, sehrish taga haɗuwa yau dae karo na farko data fito kuma karo na farkon data fara ziyartar wuri irin wannan, atare suka fito suka shiga wurin, Mutane gasu nan kowa ya ɗau wanka ana ta siyayya ba kowa ya tsone mata ido ba face ƴan mata da samarin dake a wurin, duk sai taji kunya ta kamata ganin yarda Matasan matan dake a wurin siyayyar suka ɗau wanka iya wanka, ita kuwa kallo ɗaya za'ae mata ansan bazata wuce ƴar aiki ba, 6oyewa ta rinƙa yi abayan junaid da Azmeee, dariya kawai junaid keyi don ya gano dalilin dayasa sehrish jin kunya tana la6ewa abayansu, Sam ruwan ido ya hana sehrish Sa hannu ta ɗauki wani abu, junaid ne kawai da azmee ke faman ɗebar mata kayayyakin sawa iri iri masu kyan gaske na mata, yawanci arab gowns ne, turkish dress, night dress, Pakistan, english wears komai jidar sa kawai suke yi, laces ne atampa ce, materials, shadda, Everything, Duk tana tsaye tana kallonsu kowanne ya cike shopping basket dake hannunsa, sai dai in sun matsa nan tabisu, in kuma anzo abunda zata gwada tasanya su bata taje dressing room ɗin dake a wurin ta sanya, lokacin da suka zo wurin jerin panties da bra, hannu junaid yasa ya ɗauko brazier ya ɗago da ita yana cewa "Sehrish Ga wannan gwada mu gani," Sam bata lura ba tana ta faman kalle kalle, ganin hakan yasa shi ta6o hannunta yana nuna mata bra ɗin dake hannunsa yana

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47