Chapter 28
Chapter 28
sawa da sauran abubuwan buƙata na mata,' Azmee tace "wannan ai aikin lada ne, insha Allah Omar zamu yi komai yadda kake so," "Hakan yayi mun, bari na ɗauko maki key ɗin gidan ku tabbatar kunje yau, zansa Junaid ya kai ku a motarsa," ya yi maganar yayin da yake wuce wa izuwa sashen Abbansu, Hannu yasa ya ciro wayarsa daga cikin aljuhun wandonsa, contact ya shiga tare da dannawa Abban nasu kira, kamar jira yake omar ya kira sa awaya sai gashi ya ɗauka, Ƙara wayar Omar yayi a kunnansa yana cewa "Abba gani nashigo bedroom ɗin naka, wurin ina key ɗin yake"? "Ka duba cikin side drawer ɗita gida na tsakiya suna anan ciki makullan na zuba su," "Ok to ngde Sosai Abbana, take care of your self for me," yana jiyo sautin muryar Abban nasu Mai haɗe da Murmushi yana cewa "Nima haka ka kulamun da kan ka," "Insha Allah," Omar ya faɗi tare da rejecting kiran, ya mayar da wayar tasa cikin aljihunsa, Kai tsaye inda Bedside drawer ɗin Abban nasu take ya ƙarasa tare da zuƙunnawa ya janyo gida na tsakiya acikinta, Sai ga makullan sun bayyana hannu yasanya ya ɗauka sannan ya fito daga ɗakin nasa, Kitchen ya nufa azmee na ganinsa ta fito, ƙarasawa yayi tare da miƙa mata key ɗin yana cewa "Ga shi nan ku tabbatar kunyi aiki mai kyau, yanzun nan zan ma junaid magana yazo yakai ku can gidan," Azmee ta amsa masa da cewa "Toh insha Allah," sannan Omar ya fuce daga main palour izuwa filin buga ball ɗinsu tunkan ya isa yake faman kwalawa junaid kira wanda ke acikin filin kwallon sai faman buga ball suke yi su uku shi da wasu daga cikin security ɗin gidan, Jin kiran Omar yasanya shi dakatawa da yin kwallon ya wurgar masu da ita sannan ya fice daga cikin ragar izuwa inda Omar yake, tsayawa yayi agabansa tare da zuƙunnawa ya dafe guiwarsa sai faman haƙi yake yi daker ya iya cewa "Yaya Omar gani," Hannu omar yasa tare da bugun bayan junaid yace "Bana hana ka buga ball dayawa har haka ba? Tun fa ɗazu dana shigo nasame ka, cikin waɗancan gardawan sai faman wahalar mun dakai suke yi," Murmushi junaid yasaki tare da ɗagowa tsaye yana cewa "Yaya Omar zandaina ne, amma yanzu tana sanya ni nishaɗi sosai," Jinjina kai Omar yayi tare da dafa kafaɗarsa yace "ko don saboda lafiyarka junaid, yakamata kadaina yawan buga kwallon ɗin nan da kuma yawan yin guje-guje,' Cikin girmamawa junaid yace "insha Allah yaya Omar zandaina," dafa kafaɗarsa omar yayi sannan yaci gaba da cewa "ka shiga ciki ka shirya zaku fita tare da Azmee da wannan Yarinyar inaso ka kaisu Gidan Uncle Abusufyan, zasu yi mun aiki ne kaima sai ka taya su," Cike da zumuɗi junaid yace "To shikenan yaya Omar, bari naje yanzun nan nashirya nakaisu," "Yawwa My boy," Omar ya faɗi tare da wuce wa gaba, Shige wa junaid yayi da gudu cikin babban falon kamar ba wanda aka gama ja ma kunne akan yin gudu ba, A lokacin azmee da sehrish sun kammala gyara kitchen ɗin, kowan nan su ya wuce ɗakinsa domin kimtsawa, Da gudu yake tattaka Matattakalar benen adai-dai lokacin SGR ya fito shima yana ƙoƙarin saukowa down, jikinsa na sanye da jallabiya fara mai gajeran hannu abun ba'a magana, tsayawa yayi yana jiran isowar junaid Domin yayi masa kyakkyawan ruƙo, sai da junaid yakai ƙarshe sannan ya lura dashi, ɗan zaro ido yayi tare da dakatawa da tafiyar gabansa na faɗuwa, sarai yasan cewa sun hana shi gudu shi kuma abun ajinin sa yake yadda kasan wanda aka sanya Ma battery haka junaid yake, Tun kafin Babban yayan nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "Bazan ƙara ba wlh, na daina" ya faɗi yana ɗan raku6e fuska yana kallonsa wuri da ido, Sgr yace "Junaid na ta6a sa hannu na ajikinka, da sunan zan buge ka ga? Girgiza kai yayi tare da cewa "a'a babban yaya, baka ta6a ba kuma bana fata, ai nasan ma bazaka ta6a buguna ba," ya faɗi da murmushin nan nasa, Sgr yace "meyasa kake tunanin cewa bazan iya bugunka ba,"? ɗan cizon red lips ɗinsa tare da cewa "Because.......You love me so much......' ya ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin sauri yana dariya, bin shi da kallo kawai Sgr yayi, tunawa yayi da wata magana da aka ta6a faɗa masa cewa *Kowa ne ɗan adam yana da lagwansa, kaima haka ga lagwagonka nan, wato ƙanin ka JUNAID, Yakamata ka kula dashi sosai, Saboda duk wanda zai kawo maka hari acikin maƙiyanka, to ina da tabbacin cewa zasu 6ullo maka ne ta wurin JUNAID, So you've to be very careful,"! Jikinsa ne ya ɗanyi Sanyi amma ta wani 6angaren yana jin cewa bazai ta6a barin hakan ta faru ba A matsayinsa na SURGEON GENERAL RAFAYET, A babban falon ya zauna saman doguwar kujera mai mazaunin mutun uku, ya kishingiɗa tare da ciro wayarsa yana daddanawa, Shigowa Omar yayi cikin babban falon ganin SGR yasa shi sakin fara'a yana cewa "Ashe kana ciki yaushe ka shigo," tashi zaune Rafayet yayi jin muryar omar, Kallonsa yayi tare da cewa "ban jima da dawowa ba, what of u ,"? ya tambaya yana kallonsa, Zama Omar yayi saman Sofa ɗin da sgr yake suna ɗan fuskantar juna yace"Nima yanzun nan nashigo, bansan kana aciki ba ae dana shigo, dama inaso nace kunyi waya da EVA? tana so tayi magana dakai sosai tayi mun magana ɗazu, its better ka kira ta if not kasan halinta ƙaramin aikinta ne kaganta a Nigeria," ɗan ta6e baki sgr yayi tare da cewa "naga missed Calls ɗinta, na manta nabi kiran nata that's why," Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa "Har yanzu baka yanke shawara bane game da ita? Pls bro kodan saboda Uncle Donald yakamata ka sassauta mana....' Wani irin kallo Sgr yake binsa dashi kafin yace "Uncle ya riga da yasan tsarina, ko shi kansa ya tsawatar mata akaina amma taƙi ji so ni banson ya zanyi na fahimtar da ita ba," Omar yace "matsalar kenan, ni abunda yafi damuna taurin kanta, in banda ƙarfin hali irin nata taya zata ce dole sai kai zata aura? a ƙalla EVA ta baka kusan 10years aduniya, har yaushe ne zata daina wannan mafarkin? ya tambaya yana kallonsa, Sgr yace "Omar da ace zan iya canza ra'ayi na akan mace ,to ina mai tabbatar maka da cewa ita ce mace tafarko da ta cancanta ta mallake ni, saboda kusancin dake a tsakani na da ita..................." Karaf!! Maganar Sgr ta sauka a kunnan Sehrish wadda fitowarta kenan ta nufo cikin babban falon, har ta kammala shiryawa tsaf, ta zumbula jalbaba ajikinta har ƙasa maroon colour, hannunta na ruƙe da hand bag, ƙafarta kuma na sanye da flat shoes launin hijab ɗinta, fuskarta sam babu makeup ƴar hoda ce kawai ta shafa sai ta murza man baki a la66anta, amma ba ƙaramin kyau tayi ba, tsayawa tayi jiki amace tana sauraron firar tasu sam tagaza motsi, har sai da Marshal Omar ya ɗago da idonsa ya kalle ta, gabansa ne yaji yayi mugun bugu sam yagaza ganewa wannan ruɗanin dake a fuskar yarinyar nan, Sehrish bata lura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47