Chapter 46
Chapter 46
gaba ɗaya......................... dariyar mugunta baba alamu ya saki ganin abun yazo mashi cikin sauƙi, nan take ya shiga kwance zariyar wandonsa, daker hussana take jan numfashi saboda buguwar da tayi wani irin ciwon kai yafar mata lokaci guda, jin motsinsa dab da ƙafafunta yasa ta dumbuzar ƙasa a hannunta, ta daddage ta tashi zaune tare da watsa mashi ita a fuska, nan take yashiga yin tsalle yana faɗin "kai ! Kai!! Kai !! Don ubanki ni kika watsa ma ƙasa a ido! aiko bazan ƙyale ki ba, saina wulaƙanta rayuwarki, Jin hakan yasa hussana zabura tare da miƙewa tsaye zata gudu batayi wani aune ba taji yaja rigar jikinta nan take ta soma yage wa, juyowa tayi tare dasa hakoranta ta gartsa mashi Cizo, azaba da raɗaɗi suka sa shi sakin ihu, kuma hakan ya ƙara fusata shi, a fusace yabi ta tare da damƙo gashin kanta ya janyo shi da ƙarfi ta dinga sakin ihu tana kuka tana kiran Sunan Jahad, Matse ta yayi ajikinsa tare da sa hannun shi biyu ya ƙarasa yage rigar jikin hussana gaba ɗaya, hankali a matuƙar tashe husana ta watsa mashi miyau afuskarsa biji-bijin daya daya fara gani ne yasa shi ɗan dakatawa, hannunta ta sanya tare da ingije shi da ƙarfin gaske gaba ɗaya baba alamu yayi taga² zai faɗi ƙasa, Cikin sauri hussana ta tattare rigarta ta kare kirjinta da ita, hanyar fita daga ɗakin ta nufa da gudun gaske tana kuka burinta kawai ta isa kopar ta buɗe ta fuce tana cikin gudun nan baba alamu ya taso a matuƙar zuciye ya nufe ta da sauri yakai hannunsa tare da jan rigarta data rufe jikinta da ita, gaba ɗaya ya 6an6are rigar daga jikinta ya cire ta gaba ɗaya ya ruƙe a hannunsa, Wani irin kuka hussana ta saki mai matuƙar cin rai ganin yarda ya cire mata rigarta, gashi ko brazier bata sanya ba, ƙirjinta gaba ɗaya sun fito, hannunta ta sanya ta tarbesu tana kuka kuma hakan baisa ta daina tunkarar ƙopar ba, Bin ta baba alamu yayi da gudun gaske saboda ya ruƙo ta jikinsa don ya idasa nufinsa, Sai dae ina kafin yayi wani kwakkwan yunƙuri tuni anyi ma ƙopar ɗakin wani irin kwakkwaran Naushi nan take katakon jikinta ya farfashe gaba ɗaya ta buɗe, A tsorace baba alamu ya dakata yana faman zazzare ido don son ganin wanene wannan ya faɗo masa cikin gidan gonarsa !!!!!!!!!!!! Ita kanta hussana ta firgita tsayawa tayi jikinta na wani irin kerma ga zazza6i daya lullu6e ta, har lokacin hannunta na tarbe da ƙirjinta, Duro ƙafarsa yayi cikin ɗakin tamkar damusa wani irin kakkarfa ne mai ban tsoro, jikinsa na sanye da Jacket baƙa daga ciki kuma farar t*shirt ce wadda ta bayyana ƙirar ƙarfinsa, Sai dogon wando baƙi, bai bamu damar muga fuskarsa ba domin kuwa tana sanye cikin face mask baƙi, idonsa kuma na sanye da baƙin glass, gaban hussana ba ƙaramin faɗuwa yayi ba duk ta gama tsorata, baba alamu kuwa murya na rawa yashiga cewa "kai...Wai Wanene kai ! daga ina kake? Mai ya kawoka gidan gonata ! ya tambaya yana tada jijiyoyin wuya, Har lokacin bai da alamar yin magana, a hankali ya sanya hannunsa tare da ruƙo jaket ɗin dake ajikinsa ya cire ta gaba ɗaya yayi wurgi da ita, sannan ya mayar da hannun nasa ya tu6e t-shirt ɗin dake ajikinsa ya rage babu riga ajikinsa, Hankalin baba alamu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin damtsen hannunsa a murmuɗe ga ƙirjinsa dake motsi abun gwanin ban tsoro, tuni zuciyar hussana tayi wani irin bugu nan take ta tafi zata sulale ƙasa, da Hanzari ya tarbota jikinsa gaba ɗaya tafaɗa a faffaɗan ƙirjinsa, hakan ya bashi damar zura mata t-shirt ɗinsa ajikinta donya rufe mata jikinta, bayan ya kammala sanya mata rigar, ya buɗe bakinsa ta cikin face mask ɗin yayi fito mai sautin gaske har saida baba alamu ya firgita yana faman kwalala ido, Da gudun gaske wani Saurayi ya shigo ya tunkare sa, batare da yace komi ba ya miƙe masa Hussana, cikin sauri yasa hannu ya ɗauketa tare da azata a kafaɗarsa ya fuce da ita, sai lokacin Yasa hannu ya cire glass ɗin fuskarsa tare da yin wurgi dashi, Azazafe ya sanya kyawawan idanuwansa waɗanda suka Canza Launi izuwa ja saboda tsananin 6acin rai, gadan gadan ya tunkari Baba alamu wanda ke shirin guduwa, hannunsa yakai tare da damƙar wuyan rigarsa ya ɗaga shi sama, ya dawo dashi ƙasa ya buga kansa jikin bulo nan take haƙora biyu daga bakin sa suka fito Jaga-jaga da Jini, saboda tsananin azaba da raɗaɗi ya sanya Baba alamun sakin futsari a wando yana cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un na bani na 6atare na lalace nashiga uku, Dan Allah ka ƙyale ni wlh nabi Allah nabi manzonsa .,........... tsawa mutumin ya daka masa tare da cewa "Kasan da Allah kake ƙoƙarin aikata ma ƙaramar yarinya faɗe tsofe tsofe dakai!! mutun mara imani da tausayi irinka wanda baisan darajar ƴa' mace ba Sam bai cancanta daya cigaba da rayuwa ba,' ɗagowa baba alamu yayi yana ja da baya da baya idonsa jawur, jini na kwaranyowa daga bakinsa yana cewa "Dan Allah kada ka kashe ni ! Kabarni a haka naji jiki sosai, ina da ƴa'ƴa da mata in ka kashe ni zasu shiga wani hali.....' bai bari ya ƙarasa maganar ba, yakai masa wata irin mahangul6a da hanunsa nan take yasake fasa ihu, "Karka kuskura ka sake buɗe wannan ƙazamin bakin naka da sunan zakayi mun bayani ! Bani da lokacin sauraron jawabin Ka, har kana da bakin da zakace mun kana da ƴa'ƴa da mata, don ubanka su yaran daka ɗauko donka lalata ma rayuwa daga sama suka faɗo? Ko su basu da dangi ne da zasuyi kuka in sun rasa su? Idan ka lalata masu rayuwa kana da tabbacin zasu ƙara numfashi ne ko baza suyi ba ? Ka yi tunanin hakan? ! idan wani ya lalata rayuwar ƴarka yaya zaka ji? Ka ƙiyasta yaya raɗaɗin yake azuciya............yana faɗin hakan yasa hannu ya rarumesa tare da wujijjiga shi ya sake buga kanshi ajikin bulo ɗin nan take kansa ya fashe jini ya soma kwaranya, ko shurawa baiyi ba nan take ya mutu a mace............ (Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar? Ka mutu kana aikata irin wannan mummunan zunubin batare da ka shiryu ba? Shin mai zaka ce ma Ubangiji? mutum baison lokacin mutuwarsa ba, shiyasa ake so koda yaushe mutun ya kansance cikin shiri kuma ya kasance yana aikata abun kirkiri, sam baba alamu baisan cewa yau wa'adinsa zai cika ba, Ga yarda ƙarshem shi takasance Ya Allah kasa muyi kyakkyawan ƙarshe, kuma ka kare mu daga aikata aikin dana sani 🙏😥 duk da ya mutu amma hakan bai masa ba saboda raɗaɗin da yake ji azuciyarsa, hannu yasa ya rarumi ƙaton dutsin dake ajiye a ƙasan wurin zai rotsa masa kai, cikin sauri matashin nan daya fita da husana ya faɗo ɗakin ya tunkaresa tare da hanzarin ruƙo hannunsa yana cewa "Yalla6ai kabarshi haka mana, ya riga daya mutu," fisge hannunsa yayi yayin da idonsa ke cike tab da hawaye da wani irin huci yake cewa "Kabarni kawai na tarwatsa kansa ko zuciyata ta samu salama, kasan yarda nake ji acikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47