Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Sehrish bayan ta kammala dinner ɗin tare da azmee suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu izuwa kitchen, Sehrish ce ta wawwanke su tare da jerasu a ma'ajiyarsu, Bayan ta fito suka ci karo da azmee tace " Inaso naje na kwanta,pls kada ki bari bacci ya kwashe ki, idan Twins sun dawo ki tabbatar kin kai masu dinner ɗinsu, Shima Abbansu pls ki kaimasa nasan ƙila sai wurin 12 zasu shigo,. Sehrish tace "To aunty azmee insha Allah baxanyi bacci ba, zan kai masu in sun dawo," daga nan azmee ta wuce ɗakinta, itama sehrish bedroom ɗinta tashiga, sai da tafara shiga toilet ta kuskure bakinta, dama da alwalarta, Fitowa tayi ta ɗauki hijab ɗinta da ta ajiye saman gadonta, ta kabbara sallah _________________________________________________ Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami'an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci, "Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne"? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat, "Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah," acewar jahad Hussana tace "Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso....' Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace "Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya Kusa dasu taje sannan tasoma magana "Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane? Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Insha Allah aunty bazamu fito ba," ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace "Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana," ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta, Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta, Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa "Kaiii !!!" taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al'ajabin wannan Ikon Allahn, tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya, Cike da mamaki Aunty babba tace "Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne? Cikin sauri hajjaju tace "A'a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne," tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin, Kallon jahad hussana tayi tare da cewa "Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta," "Nima so nake na tuna inda nasanta," Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta, Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,. "Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta, Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa "Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al'ajabi? Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta, Aunty babba kuwa cewa take yi "Hajjaju kin barni acikin duhu, wlh har kinsa hantar cikina ta kaɗa dan Allah kisanar dani me kika sani agame dasu? dariya hajjaJu tayi tare da tafa hannayenta tace "Ana bura'uba a lagos! yo ke laila da kike cewa zaki sa a zubar maki da waɗannan yaran don ki nisanta su da Omar, idan Kin toshe wannan hanyar to ita waccen ɗayar hanyar da ta ruga isa inda bakya so ya zakiyi da ita? gaba ɗaya fa Aunty babba ta gama rikicewa da bayanin hajjaju, cikin tashin hankali tace "wai me kike nufi ne hajjau, kiyimun bayani mana yadda zan fahimta !!! ta faɗi tare da ɗan jan guntun tsoki, Murmushi hajjaju tasaki sannan tace "Ni baza kiji mutuwar sarki abakina ba!kawai abunda nakeso ki sani shine babu wanda ya isa ya hana ruwa gudu sai Allah! Bakin alƙalami dai ya ruga daya bushe, Amma fa waɗannan yaran da kike gani wlh ikon Allah ne su, tunda har Allah ya haɗasu da Omar aikuwa magana ta ƙare, Yakamata kisan abunyi,' Hajjaju tayi maganar tare da wuce wa ciki tabar Aunty babba tsaye abakin kitchen baki asake, lokaci guda taji ta ƙara tsanarsu hussana da jahad tabbas suna tattare da wani abu yaran, duk da bata fahimci inda maganar hajjaju ta dosa ba, ranta ya gama 6aci tsoki ta buga tare da cewa "ta tsaya tayimun bayani amma ta tsaya yimun wasu sambatun banza dana wofi,ni duk tasa hankalina ya ƙara tashi, kuma wlh goben nan zansa a Kwashe mun su aje can azubar dasu tsakar daji, sai dae abunda bangane ba acikin maganar hajjaju wacece ɗayar hanyar da take nufi wadda ta isa inda banaso!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!? ta tambayi kanta sai dae kash babu amsa hakanan ta koma ciki tana faman sambatu aranta, Zumbur !! Jahad tayi tare da kallon husana tace "Wlh nasanta!! Nagane ta !! Itace matar da ta taimaka mana a asibiti har ta biya kuɗin gadon Ki husana, wlh itace matar da tasama ma SEHRISH aiki, hakan na nufin ta son inda sehrish take.....!! Cikin tsananin farin ciki jahad tayi maganar, hussana ma aɗan raxane tace "dagaske jahad itace tasama ma sehrish aiki? Ke nan itace kawai zata iya faɗa mana inda ƴar uwarmu take kenan,. jahad tace "eh itace, nagane ta yanzu ya za'ayi muyi magana da ita, gashi aunty ta hanamu fita, amma ni dae inason magana da ita kodan saboda ta faɗa mana inda sehrish take,' jahad tayi maganar fuskarta tamkar zatayi kuka, Cikin sanyin murya hussana tace "Jahad kada ma musa rai don nasan bazata faɗa mana ba, ita fa ƙawar Aunty ce, kuma kinsan muguwace idan halinsu ɗaya fa? Bazata ta6a faɗa mana ba, Ni tsorona ma kada ta faɗa ma wannan muguwar auntyn inda sehrish take, suna iya zuwa su cutar da ita, Allah yasa sehrish tana lafiya banaso wani abu yasame ta.........'" tayi maganar

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47