Chapter 32
Chapter 32
lafiyayyen abinci ta kuma jera masu shi adining, su duka suka halarta suna ci jahad na kusa da uosana polyayin da Hafsat ke kusa da mommynta dama mai 4 seats ne, Duk sun kasa sakewa suci Abincin saboda fargabar da suke ji aransu, kwarama hussana tasamu tana shan kakkauran tea ɗin data haɗa mata tare da bread wanda yaji butter ajikinsa, ɗagowa Aunty babba tayi ta kalli jahad tare da cewa "My daughter me yake faruwa ne? Naga tun ɗazu sai fama juya cokali kike yi acikin plate, yakamata ki fara cin abincin ko saiya huce"? ta tambaya cikin nuna kulawa, murya na rawa jahad tace "babu komai Aunty zanci ne yanxu," Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa "kwara dai kici ta da zafin ta, saboda in ta huce baza tayi maki daɗin ci ba," Jahad ta amsa da toh sannan ta soma cin taiyar pasta din dake agabanta, Mayar da idonta tayi kan na hussana tace "Yawwa my daughter, ae ke na lura bakya wasa da abinci da alama, kamar ni kike, shiyasa gani nan kamar buhun masara sai uban auki," Jin abunda tace yasamu fashe wa da dariya su duka banda hafsat dake satar kallon mommyn nata, abun ɗaure mata kai yake ganin yadda lokaci guda Mommynta ta sakewa yaran aranta tana cewa "gaskiya Mommy ba ƙaramar ƙuruwa bace wurin iya tsara tuggu, ta iya shu'umanci Allah kaɗai yasan me take shirya wa, koma dai menene nidai ina nan ina zuba ido in gani......👀 Murmushi Aunty babba tasaki tana kallonsu ganin yarda tasanya su nishaɗi aranta tace "haka nake so don kutmar ubanku a hankali zan canza muku tunani har na cimma burina," a fili kuma ta washe baki tana cewa "ku hanzarta ku kammala ci dare yayi sosai yakamata ace yanzu kun kamma yi nisa a bacci, sannan jahad kada ki manta kafin ku kwanta ki tabbatar kin ba Hussana maganinta, Jahad ta amsa mata da "toh," Bayan sun kammala yin dinner ɗin nasu suka wuce bedroom din hafsat bayan hussana tasha maganinta sannan suka kwanta, bacci mai nauyi ya ɗauke su............. Kallon Hafsat aunty babba tayi a lokacin itama idonta nakan Mommyn nata, "tun ɗazu na lura da satar kallona da kike yi shiru kawai nayi," aunty babba ta fadi tana kallonta Hafsat tace "hmmmm mommy kenan ni so nake ki faɗamun abunda kike shiryawa game da twins ɗin nan yakamata na sani," Dariya aunty babba tayi kafin tace "bai da amfani koda kin sani hafsat ! ki ma daina tambayata domin kuwa bazaki ta6ajin mutuwar sarki abakina,!" Jinjina hafsat tayi tare da miƙewa daga kan dining ɗin tace "Shikenan Mommy kwarama ki ruƙe sirrinki, yarda in asiri ya tashi tonuwa ke kaɗai zakiji jiki ban dani, ni dae nayi nan," tana faɗin hakan ta wuce cikin bedroom ɗinta, Saman Sofa ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e jikinta, Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa "Yanzu wasan ya soma, " 😳 Nikuma nace Allah yaba mai rabo SA'A ***********AFTER 1 WEEK********* BAYAN SATI ƊAYA Acikin waɗannan kwanakin Jahad da hussana ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, sun samu ƴanci sosai acikin gidan jikinsu yayi kyau ba laifi sun ɗan murmure, gashi hafsat bata gajiya da ɗawainiya dasu har fita takeyi dasu yawan shaƙatawa, su fita shan ice cream ko kuma ziyarta gidan friends ɗinta, Aunty babba dae ta zuba ma sarautar Allah Ido burinta kawai Baba alamu ya diro Garin kaduna kafin Zuwan Omar, don tuni Baba Alamu yasanar da ita cewa suna kan hanya yau Litinin zasu sauka kaduna, 😳 A 6angaren Sehrish kuwa tana cikin farin ciki matuƙa saboda makaranta da zata fara zuwa, an riga da an kammala yi mata komai hatta Uniform ɗinta an kawo mata su kusan kala 3, ga sandals ɗinta masu kyan gaske, ga jibgegiyar school bag ɗinta da aka siya mata tare da textbooks na amfani da sauransu, abunda ya rage mata yanzu shine fara zuwa makarantar acikin satin nan, 😇 Tuni Marshal Omar yayi oder na haɗaɗdun furnitures made in dubai, kamfanin da yayi siyayyar kayan su da kansu, suka tsara mashi gidan wa'iyazubilla wurin kyau ba'a magana, komai sabo fal acikin gidan, kayan kitchen ne kayan ɗaki kayan falo komai fa wannan an zuba acikinsa ba abunda ya bari, bari in taƙaice muku zance hatta wannan kayan store na abinci yasa an jibge masu shi, duka freezer ɗin dake acikin gidan yasa an cike masu shi da Kayan marmari dana sha, komai fa Omar ya tanadar musu na jin daɗin Rayuwa, dama abunda ya hana shi zuwa kaduna kenan saboda yafi son saiya fara gyara masu gidan ya sanya musu komai na more rayuwa acikinsa sannan ya je yaɗauko su, kuɗi sosai Omar yaba Sehrish da azmee don suje yi musu siyayya, koda suka tambaye shi size dinsu na kayan da zasu siya masu gudun kar ayi kuskure, sai yace musu komi zasu siya irin na Sehrish saboda yana da tabbacin cewa tsayinsu da komai na jikinsu bazai wuce na SEHRISH ɗin ba, da sukayi masu siyayyar kaya masu yawan gaske kamar irin na sehrish amma nasu yafi yawa saboda su biyu ne, ƙarshe sai dai motar kamfanin da su kayi siyayar ta kawo musu kayan har gidan Abusufyan saboda motar junaid bazata iya kwashe su duka ba, saboda shine ke ɗawainiya dasu duk in da zasu fita, finally dae komai ya kammalu,👍 Ga masu karantawa a facebook indai kuna son Cigaba da kawo muku littafin Abban sojoji to ku hanzarta yin payment recharge card zaku tura ta wannan numbar 08103884440, 200 ne saura 3 pages free ya qare, Ga masu acct gashi nan 3196407426 first bank, Bature hafsat Muhammad, wanda sukayi payment ina sane dasu kuma kuɗinsu bazai tafi abanza ba🙌 [9/12, 8:44 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────EPISODE 21-22 ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️ ~Story & Written~ *BossBature* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• Ringing ɗin da wayarta ke faman yi ne ya tashe ta daga guntun baccin daya ɗauke ta, farkawa tayi tana faman yin Hamma, hannu ta miƙa tare da ɗaukar wayarta dake ajiye saman side drawer, duba screen ɗin wayar tayi don taga wanene ke kiranta, lokaci guda gabanta ya faɗi rass ba arziƙi ta miƙe zaune saman gadon tana duban sunan mai kiram nata, sam tagaza sa hannu ta ɗaga kiran saboda tasan mai zai biyo baya, Kusan sau uku kiran nashigowa cikin wayar ta ta, amma taƙi ɗagawa daga bisa ni mai kiran nata yadaina kira, Can sai ga ƙarar shigowar Message cikin sauri tasa hannu ta buɗe sakon ta soma karantawa kamar haka _Babu buƙatar yin Sallama! Malama hafsat kin ban mamaki,Na kwashi uban kuɗi nabaki donki gudanar mun da aiki na, amma sai gashi Labari ya risƙeni cewa Anganki kina yawo dasu agari,Don haka ina so ki mayar mun da kuɗina yau ɗin nan in ba haka ba kotu ce zata raba ni dake_!!!!!!!! Wata Irin nannauyar Ajiyar zuciya Hafsat tasaki afili take furta "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un, ni sam na manta da maganar wannan matar ashe tana sane da kuɗinta, gashi har na fasa su, yanzu dole ne na biya ta kuɗinta ko na samu salama, tabbas zata iya ja mun bala'e Ya zanyi ni! Gashi Yau
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47