Chapter 20
Chapter 20
kuma ta sake cewa "Jahad komai yasa yaya Omar har yau baizo ya duba mu ba"? Jahad tace "muyi mashi Uziri hosana, ni nasan cewa yana sane damu kuma zaizo nan very soon,' Sun jima suna yin fira atsakanin su, ita kanta jahad tasan cewa hosana juriya kawai take yi tana yin surutu, daker tasamu hosana ta koma ta kwanta, itama a gefenta ta ra6a ta kwanta, lokaci guda bacci ya kwashe su su duka, Ba ƙaramin bacci suka sha ba, don kuwa har sai da gari ya waye rana ta fito sannan jahad tafarka, hosana kuwa nata faman sharar baccin ta, ganin yadda hosana ke bacci anatse ya ƙara tabbatarwa da jahad cewa tasamu sauƙi sosai, tashi tayi ta cire hijab ɗin dake jikinta, ta shige toilet ɗin dakin Alwala tayi sannan ta fito ta ɗauki hajiabin ta zura, tana faman tunanin in da zata samu tayi sallah don babu carpet, Fitowa tayi don ta duba hafsat samu tayi bata anan inda tabar ta jiya babu ita ba alamarta a wurin, sai taji hankalin ta ya ɗan tashi tsoranta kar ace guduwa tayi tabarsu a asibitin, Hankali atashe ta fito harabar asibitin ga mutane nan nata wuce wa wasu na shigowa wasu na fuce wa, sai faman waige waige take yi tana neman hafsat, har wurin ajiye motoci taje taga ko zata ga motarta amma babu ita, hakan na nufin tabar asibitin kenan, da alama ma tun asubahi tabar asibitin, tuni jikin JAHAD yayi mugun sanyi, Koma wa tayi tasamu wurin inda taga wasu mata zazzaune suna fira, tayi musu sallama suka amsa mata da fara'a Tambayarsu tashiga yi idan suna da abun sallah su ara mata, nan wata daga cikin su ta miƙa mata sallaya ɗinsu da suka zo da ita, anan harabar jahad tayi sallah bayan ta kammala ta mayar masu da dardumar sannan ta koma ciki a kasalance, bakowa tafi ji ba face HOSANNA, yanzu in da gaske hafsat tafiya tayi tabarsu yaya zasu yi? Ina zasu dosa? bakomai ma yafi damunta ba face Hosana in tafarka ta son dole akwai yunwa atattare da ita, gashi ita ba ta da ko sisi balle ta siya musu abunda zasu samu su Ci, Gefen hosana tasamu ta zauna wadda ke kwance tana faman sharar bacci, tagumi ta zabga tare da zuba mata Ido tana kallonta, in taƙaice muku tsawon lokaci ba hafsat ba alamarta 😧😳 Gashi in sunce zasu kai kansu gidan duka ba wanda yasan hanyar da zai bi, saboda da daddare ne kawai suka fito daga gidan baza su iya shaida kwatancen gidan ba, gashi ko Sunan unguwar basu Sani ba, ajiyar zuciya jahad tasaki aranta tana jin cewa hutu ne yazo musu, zasu ci gaba da rayuwarsu ne kawai akan titi, _____________________SEHRISH__________________ Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time ɗin rigar jiya ce ajikinta da rolling ɗinta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba ɗaya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace "Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner ɗinsa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,' Sehrish tace "Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,' Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that's why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,' Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa, Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faɗa mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi "Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere, Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace "idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan shi baki da duk wani abu daya mallaka da zaku zo ɗaya dashi kin ga kuwa ba sa'an yin ki bane,wannan shi ake nufi da Zaren ba kalar yadin bane......' Jinjina kai sehrish tayi aranta tana cewa "Wato abunda haroon yake nufi kenan hmmm," Sannan a fili tace "To Aunty azmee me ake nufi da cewa ISKA NA WAHALAR DA MAI KAYAN KARA,!"? Har sai da azmee ta ɗanyi dariya jin wannan, ɗan gyaran murya tayi kafin tace "Kamar mutun ya yi ta wahalar da kansa akan abunda bazai ta6a samu ba, yanzu in mutun ya sanya kayan kara ana iska shin kayan zasu zauna ne batare da sun tarwatse ba? Sehrish tace "Eh hakane kuwa," "Yawwa ma'anar kenan, mutun yasanya wa ransa abunda bazai ta6a samu ba, kin ga zai tashan wahala ne," ta ƙarasa maganar tare da cewa "Zo ki ɗauki breakfast ɗin ki kai masa na kammala," ƙarasawa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin duk jikinta yayi sanyi ga me da abunda Azmee ta fassara mata yanzu, amma taci alwashin duk runtsi duk wuya zata jaraba Soyayyarta Agare shi ba fashi 💔 Fuce wa tayi ta miƙi hanya kamar daga sama taji muryar haroon a kunnanta yana cewa "ƴar Shila barka da safiya fatan kin kwana cikin ƙoshin lpy, Shiru tayi bata bashi amsa ba, yana tsaye ruƙe da ƙugu daga shi sai gajeran wando ajikinsa, Ci gaba da magana yayi "Dole kisha ƙamshi baby, an fa samu Freedom dole a hura hanci, hallau dae bari na ƙara tunasar miki, shisshigi da kutsi ba zai kai ki ga cin nasara ba akan wancan Babban kayan da ki ke hari, ke bama shi ba ko junaid dana ga kina shisshige mawa wlh yafi ƙarfin ajin ki, kwara ma ni zan iya yin maneji na lalla6a ki mu rufa wa juna asiri, ke ƴar aiki ni kuma ɗan masu gida Fantsararre,,, takaici ya hana ta cewa komai wuce wa kawai tayi upstairs, Tun da ta nufi part ɗinsa take jin tashin ƙamshi ya gauraye ko'ina Har cikin hancin ta direct masu daɗin ƙamshi, Bayan tayi sallama tashi ga, babu kowa a palor ɗinsa ƙarasawa tayi ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗinsa, tsayawa ta ɗanyi don ta jira fitowarsa, Tana cikin tsayuwar nan wayarsa da ya bari asaman hannun Sofa ta soma ringing da ƙarfi har sai da sehrish ta ɗan yi firgit da ido, kai idonta tayi a inda wayar take hada sa hannu tana dafe kirjinta, matsawa tayi a ƙoƙarinta na ta ɗauki wayar takai masa, Adai-dai time ɗin yafito cikin sauri Don ya ɗauki wayar saboda Kira ne mai mahimmanci agare Sa yasan dashi Jin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47