Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

soma gangarowa daga fuskarta da jikinta don bala'e hatta paper ɗin da take rubutun asamanta ta jiƙe sharkaf da gumin da take fitarwa 😳😳😳 *SHIN WACECE WANNAN*‼⁉❓❓❓ Mgnr payment 300 ne amun magana direct *08103884440*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* *🔥The Father Of Soldiers🔥* ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖 *Story & Written by* *Hafsat Bature Muhammad* ~💋BOSSLADY💋~ *Abban Sojoji part 2* *EPISODE 3-4* Sam jahad ta gaza yin kwakkwaran motsi saboda ta riga ta gane muryar wacece....... Idasa shigowa tayi da wannan takun nata, jikinta na sanye da sleeping dress red colour masu zanen flowers ajikinsu, abunka ga fara ta fito 6au acikinsu, kanta ko mayafi babu ba kowa bace wannan face AUNTY BABBA, Lokacin da ta isa inda jahad take, hannu tasa ta fisge takardar da take rubutawa, ta ɗago da ita tana karanta wa, zaro ido tayi hankali tashe tace "Keeeeee! Don ubanki ni zaki tonawa asiri!? Wato Omar kike rubutawa wasiƙa don ki faɗa mashi abunda muke yi maku ! Wlh kin shiga uku, bazan ƙyale ki ba sai kin yabawa aya zaƙinta!!!! a masifance take magana ƙarshe tayi Wurgi da takardar ƙasa sannan azafafe da wannan hannun nata ƙirar samudawa ta damƙo mayafin dake lullu6e akan Jahad nan take ya sul6e ƙasa hakan ya bata damar damƙar gashin kanta, wani irin zafi ne ya ziyarci jahad saboda ruƙon da aunty babba tayiwa gashin kanta, Janyo gashin tayi ta ɗago jahad dashi, jikinta sai kerma yakeyi duk ta rurruƙe hannun aunty babba dake ruƙe da gashin kanta tana faɗin "Aunty dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba....' bata ƙarasa ba aunty babba takai mata naushi a bakinta, nan take jini ya soma zuba daga bakinta le6enta suka faffashe, saboda tsananin azaba da raɗaɗi yasa jahad fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali, Wurgi da ita aunty babba tayi jahad ta tafi jiki a mace ta zube ƙasa, tattakawa aunty babbba tayi izuwa inda take don bata gama dukan nata ba, Tashi zaune jahad tayi tana jan jikinta da baya da baya tana faɗin "dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba.....nasan nayi kuskure.... "Ke ƙaramar ƴar iska ce ! bakisan koni wacece ba ! Har ni zakiyi wa iya shege acikin gidana ! Ni zaki tonawa asiri Wurin Omar? idan na so yanzu saina sa wuƙa na yanka ki, shashasha... ta ƙarasa maganar tare da sake damƙo gashin jahad tashiga yi mata azaba dashi, ta ja shi da ƙarfi tamkar zata tsige shi daga kanta, tuni idon jahad yayi jawur wasu irin jijiyoyi suka firfito mata a goshin ta, don rashin imani aunty babba sai ta naɗe gashin a wuyan jahad ta shaƙeta dashi gadan gadan zata kashe ta, murya ashaƙe jahad ke fidda sounds tana faɗin "Ahh...ah..ann...bazan..ƙa..ra..ba' sam aunty babba bata da niyar ƙyale ta sai ma ƙara shaƙeta da take yi Kamar daga sama Hosana ta faɗo ɗakin saboda tajiyo ihun jahad da farko sai tayi tsammanin kunnanta ne Suke mata gixau,amma rashin kwanciyar hankali da jin bugawar zuciya yasa hosana gaza samun natsuwa ta fito don tazo taga wani hali jahad ke ciki ta rubuta wasiƙar, Shine ta taras da wannan tashin hankali, ihu tasaki a haukace ta watsa da gudu inda aunty babba ta shaƙe jahad ajikin wardrobe, "Kada ki kuskura ki ƙaraso in ba haka ba zan haɗa dake kema," aunty babba ce tayi ma hosana wannan maganar batare da ta janye hannunta daga wuyan jahad ba, cikin kuka hosana ke faɗin "ki sake ta...! Ki kyale ta....kada ki kashe mun ƴar uwata.....' amma sam aunty babba taƙiya, Ganin jahad ta soma kakarin sheƙawa barzahu yasa hosana fita hayyacin ta, aikuwa ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe tasamu damtsen hannun aunty babba ta Gartsa mata lafiyayyen Cizo da hakoranta 30 cufffff A firgice aunty babba ta saki jahad tana yarfa hannun ta sai ga jini na ɗigowa, cikin hanxari tasa ɗayan hannunta ta zame hannun rigar jikinta don taga inda hosana ta cije ta, wurin yayi jawur ga sahun haƙoran hosana nan rerass a farar fatar hannunta dama gashi dumurmur na ƴan hutu, Cike da jin raɗaɗi tace "Innalallahi !ni kika ciza har kika fasa mun fatar jiki na !! Ya salammmm !! Kin mutu wlh !! Kin shiga uku !! tayi maganar idonta jawur saboda taji raɗaɗin cizon hosana wurin har wani Zogin azaba yake yi mata, Ja da baya hosana tashiga yi a tsorace ganin aunty babba na tunkaro ta Kamar Damusa, gashi jahad tunda aunty babba ta sake ta, ta sulale ta sume a ƙasa balle itama ta taimaki hosana, Hanyar fita ta nufa da gudu zata fice, cikin rashin sa'a aunty babba tasanya ƙafarta ta taɗiyo ƙafar hosana, aikuwa ba ƙaramin buguwa hosana tayi ba, gaba ɗaya ta kife ƙasan tiles ɗin ɗakin, fuskarta ta dake sa, nan take hancinta ya fashe jini ya soma kwaranyowa, haka goshinta ma ya fashe da La66anta duk sun farfashe ihun azaba kawai hosana ke saki tana faɗin "wayyo Allah na ....! Nashiga uku...na mutu na lalace !! Aunty babba tace "baki mutu ba, don ubanki, yanzu ne zaki mutun.....tayi maganar tare da kai hannunta kan Gashin hosana wanda ya barbaje ƙasa, kwakkwarar damƙa takai masa, ta ruƙo shi dakyau ta janyo hosana dashi har sai da hosana ta miƙe tsaye tana ihu kamar ranta zai fita, daddagewa aunty babba tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta buga kan Hosana jikin bangon ɗakin wayyo Allah zoka ga yarda jini ya wanke bangon, Razanan nan Ihu hosana tasaki na azaba tamkar maƙoshinta zai ballo waje nan take ta sulale ƙasa a mace....... Ihun da hosana tayi na ƙarshe wanda ya karaɗe ko'ina harya sa Hafsat dake kwance ɗakinta saman gadonta farkawa a firgice, ta diro daga saman gadonta jiki na rawa ta fito ta tunkari inda sautin ke fita cikin hanxari ta faɗo ɗakin, gabanta ne yayi wani irin bugu ganin Momynta a tsaye tana huci kamar wata zakanya, ga kuma twins ɗin da Omar ya kawo a baje ƙasa jina jina musamman hosana an zubda jini Hankali tashe hafsat tace "Mommy me nake gani haka !! Me kika yi masu ne !! Kashe su Ki kayi da hannun ki !!! tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa "Eh kashe su nayi,akwai magana ne ! babu ruwanki dani ki koma ɗakinki zai fi miki," Cikin rauni hafsat tace "mommy duk rashin imani na bazan iya aikata abunda kika aikata ma yaran nan ba, ashe baki da Imani ko misƙala zarratin ! Kisan kai da hannun ki........' Bata idasa maganar ba saboda jin saukar wani irin zazzafan mari a kuncinta, tashin hankali da ba'a sama shi rana, Saboda zafin marin da aunty babba tayi ma hafsat yasata dafe kumatun ta ido jawur take faɗin "Mommy yau ni kika mara da hannun ki"? "Naje na mara ! duk kece sular da kika 6atamin raina harna aikata abunda na aikata yanzu!!" shiru hafsat tayi yayin da idonta ke fitar da wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske, Jikin aunty babba ne yayi mugun sanyi ganin hawayen dake fita a idon hafsat ƴarta tilo, Cikin tashin hankali tace "ba da son raina nayi hakan ba ! Hafsat ke kika 6atamun rai da 6acin ranki na kwanta, cikin daren nan na fito saboda zuciyata batamun

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47