Chapter 42
Chapter 42
gefensa, tayar da motar yayi sannan suka fuce daga gidan, A natse yake yin driving ɗin sehrish na satar kallon shi tace acikin ranta "koya akai ya iya driving yanzu yadda yake shagwa6a66an nan karfa wata rana ya tunkari babban mota damu kwatsam ta rotse damu duk mu mutu.....' "Matsalar ɗan nigeria kenan, duk wani bala'e shike fara kira ma kansa, yanzu ko menene na wannan tunanin"? Cikin mamaki tace "Acikin Zuciya fa nayi maganar" ta faɗi tana kallonsa Junaid yace "Eh nasani, ae muddin zaki yi gulmata acikin zuciyarki to fa saina ji don haka ki kiyaye," ya faɗi yayin da yake shan kwana dasu, Shiru tayi tun daga lokacin bata sake maganarsa ba acikin zuciyarta amma fa tayi mamaki don ita tasan cewa acikin zuciyarta tayi maganar amma gashi yaji," Tunkan su ƙarasa sehrish ke hangen katafariyar makarantar motoci sai shiga suke yi ciki suna sauke ɗalibai, tsayawa zayyana kyawun makarantar 6ata baki ne, gashi bani da isasshen lokacin yin wannan bayanin 😆 A parking space dinsu junaid ya sauke sehrish tare da cewa mun iso, atare suka fito gaban sehrish ne ya faɗi ganin tsala-tsalan ƴan mata young ladies irinta sun ɗau wanka, ƴa'ƴan masu kuɗi wayayyun gaske tun daga shigarsu zai tabbatar maka da cewa An sangarta su da yawa, saboda majority ɗin matan Mini skirt ne ajikinsa sai santala santalan cinyoyi awaye, kuma mafi yawancinsu babu hijab ajikinsu gyaran gashi ne kawai iri-iri, wasu kuma skirt ɗin nan ne ajikinsu waton pencil yabi shafe ɗin jikinsu, iya guiwar ƙafarsu ya tsaya, waro ido waje sehrish tayi tana cewa "kai!kai!!kai!!! Junaid mu koma gida, gaskiya bazan iya zama a school ɗin nan ba, wannan sunfi ƙarfi na Allah," Fashewa da dariya junaid yayi ganin yarda sehrish duk ta dabarbar ce, hannunta na kerma ta ruƙo rigarsa tana 6oyewa abayansa tana faman yi masa sambatun su koma gida, abu kamar wasa har hankalin wasu students ɗin suka dawo kansu ganin yadda Yarinyar ta ƙanƙame jikin dan uwan nata hada su hawaye a fuskarta, Shima kansa junaid sehrish ta rikita shi hankali atashe yake cewa "dan Allah sehrish ki daina, karki bani kunya mana kalli yarda hankalinsu yafara dawowa kan mu innalallahi, yanzu da ace school bus ce ta kawo ki bansan ya zaki ƙare ba," "Junaid nidai mu tafi gida, Allah bazan zauna anan ba" ta faɗi tana shesshekar kuka 😆 dariya kamar zata kashe junaid ba shi kaɗae ba hada wasu daga cikin ɗaliban dake a wajen, Wasu gungun ƴan mata ne suka ƙaraso kusa dasu, ɗaya daga cikinsu tana cewa " Wow friends kalli wani handsome guy nan ya burgeni sosai," Jin hakan yasa sehrish dakatawa da kukan tana ɗan kallonsu kai kana ganinsu kaga jarababbu, Murmushi ta gefenta ta saki tare da cewa "Kamar nasan shi a tiktok fa, zanso ko na tuna sunan shi daga gani cele ne shi sosai," Sai faman surutu suke yi suna yaba kyan junaid, "Kai nifa bazan iya jure ba, sai nayi ma shi magana," ɗaya daga cikinsu ta faɗi atare suka iso dab da su junaid da sehrish, su uku ne matan junaid yace "Sannun ku fa," suka amsa mashi da "Yawwa," sannan ɗaya daga cikinsu tace "Kamar na sanka,"ta faɗi cikin rangwaɗa Junaid yace " Sunanki Parveena," zaro ido su kayi jin yadda junaid ya faɗi sunan ɗaya daga cikinsu kai tsaye, Nuna ɗayar yayi ta tsakiyarsu yace "ke kuma Sunanki Amrish ta ƙarshen kuma sunanki Naja'at," ya faɗi da murmushi a fuskarshi, su kuwa sai faman yarfa hannu suke yi suna kallon shi cikin mamaki jin yadda ya zayyana sunayen su gaba ɗaya, Cikin mamaki wadda ya kira da Amrish tace "Dan Allah ya akai kasan sunayen mu"? Ta tambaya cike da zumuɗin son jin amsa, Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan sehrish wadda ke ruƙe da rigar junaid taɗan la6e abayansa, Junaid yaci gaba da cewa "Ban son ku ba nima kawai abunda nasa ni ke Amrish kece kullum kike isarmu da surutu a group, ke kuma parveena baki da aikin yi sai turo hotunan Chacolate iri-iri, Sannan ke kuma Naja'at kinfi kowa iya turo hoton abinci duk in zaki ci sai kin turo mana hotansa," Gaba ɗayansu suka saka ihu da sowa har suna haɗa baki wurin cewa "Wai dama kaine ! junaid romeo ko? Murmushi junaid ya saki tare da cewa "Ni ne, bamu ta6a haduwa ba amma muna yin chat sosai ta whatsapp a group, na ruƙe fuskar kowannan ku da sunayen ku,". Ba ƙaramin farin ciki su kayi ba, Amrish ta nuna sehrish tare da cewa "wannan fa? sister ɗinka ce"? Junaid yace "Eh, younger sis ɗina ce, new comer ce yau tafara zuwa," Parveena tace "No wonder, that's why naga tana hiding kanta abayanka, amma kamar batason mutane ko? Naga ko son kallon mu bata yi," Junaid yace "No just kin gane shagwa6a6iya ce, Last born ɗin mu ce bata saba shiga cikin mutane ba kullum tana a gida, so aduk lokacin da aka fito da ita cikin mutane tana ɗan razana," tunda ya soma jawabi sehrish ke kallon shi baki asake, jin irin ƙaryar daya zuƙa mata nafarko yace ƙanwarsa ce ita, kuma ya laƙwafa mata sharrin cewa tana shagwa6a bayan shine shagwa6a66e, jinjina kanta kawai takeyi, Amrish tace "Ayyah na tausaya mata but she's so cute kuma ta fito daga babban gida yakama ace tana shiga mutane," ta6e baki sehrish tayi tana ɗan kallonsu, 6an6aro hannunta junaid yayi daga jikin rigar shi, sannan ya miƙa ma Amrish yace "Gata nan dan Allah amana na baki ita, ki tafi da ita ba ta son komai ba da yake ita ɗin rainon kakarmu ce, sai ahankali," 😆 Murmushi Amrish ta saki tare da kar6ar hannun Sehrish tace"aikuwa na gode sosai da wannan kyautar, kuma zan ruƙe amana," Cikin raha sukayi sallama da Junaid yayin da suka shiga ciki da Sehrish duk ta zama tamkar mutun-mutumi , suna tafiya tana waiwayon junaid shima kansa sam yagaza tafiya kallonta kawai yake yi, sai yaji duk kewarta ta kama shi daker ya ɗaga mata hannu tare da yi mata bye-bye,' Sannan ya buɗe motarsa ya shige, yayi mata key sannan yaja ta da gudu yabar makarantar, sai da yayi nisa da driving ɗin sannan yayi parking ɗin motar agefen titi yana shesshekar kuka yana cewa "ko na minti ɗaya bana son rabuwa dake sehrish kewarki nake yi," yayi maganar tare da curo handkerchief ɗinsa daga front pocker ɗin rigarsa yana faman share hawayensa, ya jima acikin motar duk kasala ta dabaibaye shi daker ya iya tayar da motar yaci gaba da driving ya miƙi hanyar komawa gida 😥 Parveena da Naja'at Class ɗinsu suka wuce, Amrish ce tayi ɗawainiya da Sehrish ta raka ta har Admin ɗinsu wurin principal ɗin makarantar, maca ce hamshakiyar gaske tun da taji sunan sehrish tagane cewa daga Family ɗin Salahuddeen Hussein take, hakan yasa ta sake mata sosai har tana jan ta da fira, daga bisa ni taba ma Sehrish Sunan Class ɗin da zata zauna, Science department ne kuma an ci sa'a Class ɗinsu ɗaya da Amrish SS1 science C, Madaddalar ƴan iska ba 😂 (Nima Science C nayi a school ɗinmu wlh basa jin magana, dama anyi ittiƙafi babu wanda yakai ƴan C
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47