Chapter 31
Chapter 31
na a bedroom ɗinsa, Sannan ta fito ta wuce kitchen ba ƙaramin daɗi taji ba ganin azmee ta kammala zuzzuba musu komai na dinner ɗinsu, a cikin tray guda biyu ta jera masu asaman table na kitchen ɗin, Hannu kawai tasanya ta ɗauki tray ɗaya ta wuce dashi sashen marshal Omar sallama da ƙarfi tayi saboda yaji ta da kyau, kasancewar yana acikin bedroom ɗinsa bayan tajiyo Muryarsa yana amsa mata sallamarta ta, sai ta shiga cikin falon nasa ta ajiye masa tray ɗin asaman table, sannan ta fita cikin sauri tunawa da Memo ɗin da azmee tace ta bashi, bedroom ɗinta ta shiga ta dauko memon data bari asaman gadonta, sannan ta koma part ɗin nasa a lokacin har ya fito jikinsa sanye da jallabiya ash, wuri yasamu yazauna saman sofa fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ganin Sehrish, Ƙarasawa tayi inda yake tare da gaishe shi "Yaya Omar barka da dare, ya gajiyar aiki," ? "Alhamdulillah miss Sehrish, ya maganar aikin dana saku? Ina fata komai ya tafi dai-dai, sannan ya gajiya nasan kun kwaso ta ko? Murmushi tasaki tare da miƙa masa memo ɗin hannunta tace"Gashi nan, mun dudduba gidan duka kuma mun rubuta duk wani abu na furnitures da za'a buƙata acikinsa," Jinjina kai Omar yayi bayan yasanya hannu ya kar6a yana duddubawa yace "Very good, naji daɗi sosai gaskiya kunyi ƙoƙari, insha Allah zuwa gobe zanyi oder na duk wannan abubuwan da kuka lissafa ana buƙata acikin gidan, zuwa dai next week zan sake tuntu6arku," Sehrish tace "toh Allah ya kaimu lafiya," Har ta juya zata tafi ya kuma cewa "kina zuwa school ne? Ko baki fara ba? Sehrish tace"a'a ban fara ba, amma aunty azmee tace zan fara cikin kwanan nan," Omar yace "Owk, inaso ne suma yaran da nakeson kawo wa cikin gidan can, su fara zuwa school amma zan jira naga wadda zaki fara zuwa, in yaso suma saina sanya su amakaranta ɗaya dake," Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "mata ne suma? ta tambaya tana kallonsa a lokacin harya fara cin abincinsa yace "Eh ƴan mata ne, kyawawan gaske inason yaran sosai tun dana ganki sai na ga fuskarki tana koma mun irin tasu, nasan saboda son da nake masu ne da kuma kewarsu da nake yi,......' ya ƙarasa maganar asanyaye, Hakanan sehrish taji gabanta ya ɗan faɗi raaasss! amma batasan dalilin faɗuwar gaban nata ba, taso ta tambaye shi sunayen su amma tunawa da cewa ba ta kaima babban yaya abincinsa ba yasa ta saurin cewa "Allah sarki yaya Omar Allah yabaka ikon Kula dasu, yasa su zama alkhairi agare ka,' Ya amsa mata da "Amin," Sannan cikin sauri ta fuce ta koma kitchen sai da tafara haɗa masa yankakkun fruits acikin madai-daicin plate ta azashi asaman tray ɗin sannan ta fuce hannunta dauke da tray ɗin acikin babban falon suka ci karo da haroon wanda fitowarsa kenan daga part dinsu, night dress ne ajikinsa riga dai-dai guiwa, kawar da kanta tayi tare da miƙar hanya tana jiyo shi yana cewa "a rinƙa haɗawa da sallar dare ko an samu adace asamu shiga," Murmushi sehrish tasaki batare da tace komai ba bayan ta isa part ɗinsa da sallama tashiga, baya acikin falon nasa ƙarasawa tayi ta ajiye masa asaman table dinsa, sannan ta tattaka izuwa bedroom ɗinsa tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin nasa, sallama tayi masa amma shiru babu amsa hakan na nufin yana cikin toilet ko kuma bacci ya ɗauke sa ne, aranta tace "Allah yasa baiyi bacci ba," ɗan sa ƙafarta tayi cikin ɗakin nasa ta shiga ciki sai uban ƙamshi ke daker hancinta kamar wadda tashiga gonar turare, samun shi tayi baje a saman gadonsa daga shi sai Short ajikinsa, ji tayi gabanta ya faɗi rass saboda yadda surar shi ke ɗaukar idonta, sam tarasa me zatayi ta tashe shi don tasan dole akwai yunwa atattare dashi, kuma in ya tashi da safe yaga ba'akai masa abinci ba zai iya tuhumarta, Shawara ta rage ma mai shiga Rijiya, tana cikin wannan tsayuwar abakin ƙopan ɗaki nasa ƙafarta har ta soma rawa saboda gajiya da tsayuwa, Wani irin Juyi taga yayi daga saman gadon nasa gaba ɗaya ya tafi dukansa zai faɗo daga saman gadon, agigice sehrish ta watsa ciki da gudun gaske ta ƙarasa tare da kai hannu zata tarbesa sai gashi ya buɗe blue eyes ɗinsa kuma nan take yasanya hannusa ɗaya ya dafe ƙasan yarda bazai faɗi ba, Tsayawa tayi tana faman sauke haki tare da sauke ajiyar zuciya, matsawa yayi tare da cire hannunsa ya gyara kwanciyarsa saman bedmattress ɗin sannan ya ɗan ware idonsa akan Sehrish dake atsaye, mamaki ne ya kamasa ganin ta tsaye dab da gadonsa me hakan ke nufi badai tazo bane don ta hanasa faɗuwa ba, ƙarfin halin ta yabashi mamaki shin ko ta ina zata iya ruƙoso daga faɗuwar da ya kusan yi? tabbas da ace sehrish takai hannunta da nufin ta dakatar dashi daga faɗowa daga saman gadon,ƙarshenta ya faɗa mata ajikinta ya danneta tagaza tashi don kuwa ko kusa sehrish bata da ƙarfin da zata iya taimakonsa daga faɗuwa,' Sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya sam tarasa gane ma kanta, ita dai kawai burinta karya faɗo ƙasa yaji mummunan rauni shiyasa tayi yunƙurin tarbosa, Kasalalliyar muryarsa ce ta ratsa ta da cewa"Sannu da ƙoƙari, amma kada kiyi attempting cewa zaki ruƙoni next time, if not jikinkin ki nei zai gaya maki," Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"kayi hakuri bazan ƙara ba," Shiru yayi tare da mayar da idonsa ya lumshe su, yana faman sauke ajiyar zuciya, ɗagowa ta danyi tare da kallonsa tace "dama......na kawo maka dinner ɗinka ne, yana a falo na ajiye," Kusan minti 5 da yin maganarta ta sannan yace"Shigomin da fruits tare da Coffee, su kawai nake buƙata," Juyawa tayi cikin sauri ta koma cikin falon hannu tasa ta ɗauki plate ɗin dake dauke da fruits ɗin ta shigar masa dashi saman front table ɗim gadonsa ta ajiye masa, sannan ta koma ta dauko masa hadaɗɗen Coffee din dake acikin Cup ta dawo ɗakin nasa a lokacin har ya tashi zaune ya sauko da ƙafafunsa ƙasa, a gefen plate ɗin ta ajiye masa sam yagaza buɗe idanunsa da alama ba ƙaramin bacci yake ji ba, sai faman cizon pink lips ɗinsa yake yi, Ita dai burinta ya buɗe idonsa yafara shan fruits ɗin kafin ta tafi, don batason ya kwanta bai ci komai ba acikinsa 😒 Muryarsa taji yace"What are u waiting for? Ko zaki ban abaki ne? ya faɗi a time din yaɗan ware idanunsa masu ɗauke da bacci, Cikin sauri sehrish tace "a'a sai Allah yakaimu, mu kwana lafiya," ta fadi tare da juyawa cikin sauri ta fuce daga ɗakin nasa sai da tafara tsayawa ta dauki food stuffs din dake acikin tray ɗin da ta ajiye masa sannan ta fuce dasu, a kitchen tasamu wurin ta zauna saman dining table ɗin ciki, buɗe kayan abincin tayi tazauna ta shaƙe plate tana ci, bayan ta kammala ta koma bedroom ɗinta sai da tafara yin sallar isha'e sannan tayi addu'ar yin bacci taja bargo ta lullube jikinta cikin wani irin yanayi na abunda yafaru tsakanin ta da SGR, ***************AUNTY BABBA********** Da kanta ta girka masu hosana da jahad
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47