Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

cewa "Ina magana," aikuwa cikin jin kunya ta zaro ido tare da sa hannu ta rufe fuska tana faɗin "junaid dan Allah kadaina menene haka agaban mutane," fashewa da dariya yayi cikin mamaki yace "menene aciki? Kunya kuma ni bansan wannan zancen ba, ni dae ki amsa kawai kije ki gwada in tayi maki, in batayi ba acanza wata shine kawai," Hannunta na kerma ta karba tana ɗan kallon shi, har time ɗin dariyarsa yake Don shi mamaki ta bashi wai kunya, Shiga dressing room ɗin tayi hada datso kopa, faskekan madubi ne aciki ya cike bangon, cikin hanzari ta tu6e hijab ɗinta da rigarta, ta shiga kiciniyar zira bra ɗin daker hada su sakin nishi, Tsayawa tayi tana kallon kanta acikin mirrow ɗin wow, ta fito ɗas abunta dama tubarkallah masha Allah full ɗinsu suke, bra ɗin ta hau raɗau launin ta maroon colour ce, abunda sehrish take ma mamaki yarda akai junaid ya nemo bra dai-dai size ɗinta,duk jerin braziers ɗin dake a wurin, Cikin hanzari ta cire ta, ta mayar da rigarta da Hijab ɗinta, sannan ta fito, karaf suka ci karo dashi abakin ƙopan ɗakin, a ɗan razane tace"junaid yaushe kazo nan," hannu yasa ya ɗan sosa sumar kansa yana cewa "Naji kin jima ne, shine nazo in ga ko kin gaza sawa ne, sai in taimaka miki.....," ganin yarda ta waro ido waje yasa shi dakatawa, muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa "Junaid kana nufi brazier ɗin zaka taimaka mun nasa !!" ta tambaya a rikice, Kai tsaye yace "eh mana," Jinjina kai sehrish tayi tare da wuce shi aranta tana mamakin hali irin na junaid shidae ba ruwansa komai normal ne a wurinsa, tsayawa ta ɗanyi da tafiya ta ɗago ta kallesa Cike da tuhuma tace "Ya akai kasan size ɗina? Da buɗar bakinsa sai cewa yayi "Ni dana ga Zahiri," Cikin sauri yasa hannu ya rufe bakinsa saboda su6ul da bakan da yayi, kamar zatayi kuka take kallonsa tana cewa "Junaid hakan na nufin ka ta6a gani na babu kaya ko"? Girgiza kai yayi yana faɗin "No ba haka bane reeesh, baki fahimce ni bane, Ina nufin....," sam ya gaza samun amsar da zai bata gashi ta tsare shi da ido tana jiran amsar shi, Muryar azmee ce ta katse su da cewa "tsayuwar me kuke yi ne? Ku hanzarta mana muyi mu kammala, yaushe har muka wuce wurin Saloon ɗin," cikin sauri junaid yace "Hakane aunty azmee muje kawai yanzu saura me ya rage," Ya tambaya yana kallonta yayi hakan ne don ya gusarma sehrish da tuhumarsa da take yi, cikin sauri suka wuce tabi bayansu itama, A ranar yini su kayi siyayya Kamar zasu kwashe kayan Mall ɗin,komai sai da suka siyar mata shoes & bags ne Cosmetics komai wannan ba abunda suka bari, Daga nan suka wuce wurin haɗaɗɗen Saloon ɗin duk acikin Mall ɗin yake, a lokacin junaid ya koma cikin mota yana jiran su, Already sun kammala purchasing ɗinsu an jera Manyan akwatinan guda uku biyu sunfi girma a boot aka zuba su, Wasu kayan kuma na acikin Manyan Shopping bags an zuba su har a cikin back seat na motar, Murmushi kawai junaid ke saki ya langwa6ar da kansa jikin seat ɗin motar, babban burinsa shine yaga yarda sehrish ɗinsa zata fito amatsayin mace a fili ya furta "Can't wait to seee" tabbas yanzu ne yasan yasamu abokiyar rayuwa wadda zasu kasance atare na har iya tsawon rayuwarsu, shigowar sehrish rayuwarsa ta canza mishi wasu abubuwan da dama da yake kewarsu,daga ciki harda kewar Mommynsu da tatafi tabarsa tun yana jinjiri wannan abun ya ta6a mishi zuciya sosai raɗaɗin na'a ransa yana jin cewa duk cikinsu shike bata so, hakan yasa shima baya sonta duk in ta kira waya tana so abashi tayi magana dashi baya kar6a, har ila yau junaid bai ta6a ganin Mommynsu ba ido da ido sai dae a hoto, babu yarda batayi ba akan akawo mata shi Sydney amma abbansu yace muddin tana son ganin shi ta tako tazo da kanta in ba haka ba ita dashi har abada, saboda batayi mashi adalci ba,' wannan kenan Ya jima yana tunane tunane shi kaɗae abunsa yana ta faman sakin murmushi, adai dai time ɗin Sehrish ta fito tare da Aunty azmee, Ƙaraso wa su kayi ta bude gaban motar ta shiga aunty azmee kuma ta shige baya sannan junaid ya tayar da motar yana faɗin "Har an kammala saloon ɗin"? ya tambaya yana ɗan kallonta tace mashi "Eh,'. "In munje gida za'a nuna min," ya faɗi da ɗan murmushi a fuskar shi, kai tsaye yabar bakin Mall ɗin yaja Motar kai tsaye ya nufi hanyar gida dasu duk da yaso su biya wurin shan ice cream amma shi kanshi a gajiye yake yafi buƙatar gidan don ya huta, Dama jikinsa sam ba irin na ƴan wahala bane, Motarsu na shiga babban entry ɗin gidan adai-dai time ɗin kuma Motarsu Marshal Omar ta fuce daga gidan, Tasu na shigowa tashi na Fice wa, 🙅 Bayan yayi parking ɗin motar, wani sergeant ya ƙaraso ya kwashe akwatinan da junaid ya fito a boot ɗin motarsa, , Hada jakunku nan siyayyar na cikin back seat ɗin duk ya fiddo su, yayin da sojan ke kwashe su izuwa cikin gidan, Agajiye azmee da sehrish suka shiga cikin Babban falon bakowa alamar duk sun fita, azmee ta taimaka mata suka shigar da kayan ɗakin suka jibge su da nufin in sun huta an jera su a wardrobe ɗinta, Cike da zumuɗi sehrish ta cire hijabinta don taga gyaran gyashin da akayi mata, Gaban mirror ta tsaya tana kallon gashinta, haɗaɗɗen gyaran gashi akayi mata mai haɗe da Twist, Sai ta rinƙa jinta tamkar Queen saboda haɗuwa, ta jima tana kallon kanta a mirror kafin ta wuce toilet don yin wanka da alwala, Shaf shaf ta fito jikinta ɗaure da toilet, wardrobe ta wuce ta samu riga da wandonta ta zura ajikinta sannan ta ɗauki hijab da dardumar salla ta shimfiɗa, ta kabbara sallah A natse ta Gabatar da sallar, Bayan ta kammala Jiki na rawa ta cire hijab ɗinta ta ninke tare da abun sallar asaman gado ta ajiye su, Zama tayi tana bubbude kayayyakin da aka siya mata na cikin jakun kunan, sam bakinta yaƙi rufuwa, wani haɗaɗɗen takalmi ta ɗauko high heels ta ciro shi daga kwalinsa tana gwadawa a ƙafarta ita kanta ta razana daganin yarda ƙafarta ta fito ɗass acikinsa gashi ash colour jikinsa duk kyalli yake ga wasu igiyoyi na ɗaure sa ya haɗu, Shigowa azmee tayi tana faɗin "Kai!kai! Irin wannan zallar kyau haka gaskiya naji tsoran haɗuwar da zakiyi anan," . Dariya sehrish tayi tana cewa "dama yanzu nake so in jera kayan acikin wardrobe bansan ma ta inda zan fara ba," Azmee tace "kada ki damu ae shiyasa nazo saboda nata Ya ki jera su Muyi mu gama, akwai sauran aiki agabanmu ga gyaran cikin gida ga kuma aikin Kitchen,' Miƙewa sehrish tayi ta janyo akwati nan biyu da hannunta izuwa wurin wardrobe ɗinta ta jingi ne su,itama azmee ta janyo ɗayan akwatin tana cewa "Ki barmun jeran kawai, kije ki gyara cikin gidan kafin na kammala Canza ma ɗakin nan naki kamanni," . Murmushi sehrish tasaki tare da

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47