Chapter 18
Chapter 18
Da sallama ta shiga palor dinsa baya aciki, ƙarasawa tayi ta ajiye masa kayan abincin saman table dinsa, sannan ta ɗan dakata ko zai fito amma shiru babu alama, . yanke shawarar zuwa bedroom dinsa tayi a bakin ƙopar shiga ta tsaya sannan tayi sallama, daga ciki taji ya amsa mata ƙasa ƙasa kafin ya bata permission ɗin shiga ciki, A hankali ta zura ƙafa ta shiga ciki jikinta na ɗan kerma Hango shi tayi daga shi sai bathrobe ajikinsa kwance abaje saman gadonsa, alamu sun nuna cewa baiji ma da fitowa daga wanka ba, ya kwanta gajiya ce tayi masa yawa, idonsa na'a lumshe yace "Wanene ne," sehrish tace "mai aiki ce dama dinner ne na kawo maka yana a palor naga baka fito ba, Jim yaɗanyi kafin yace "Tea kawai nake buƙata,akawo mun nan,' Amsa mashi tayi da toh, sannan ta fuce ta koma palor dinsa ta ɗauko kayan tea din dake acikin tray din da ta ajiye anan sannan ta shigar masa dashi, har gab da gadonsa ta ajiye masa saman madai-dai cin table din dake a wurin ta matsa masa dashi jikin gadonsa, bin shi tayi da kallo saboda bai buɗe idonshi ba kuma baiyi yunƙurin tashi ba, yayi wani fresh dashi, Ganin alamun fa zai iya zarcewa da bacci yasa tace "Na kawo maka Tea ɗin," "I knew," ya bata amsa, jinjina kai tayi ashe yasan ta kawo ɗin, wahalar tashin ce kawai yake ji, kusan 15 mins sannan ya ƴunkura ya miƙe tare da sauko da ƙafafunsa ƙasa, rigar iya guiwar ƙafarsa ta tsaya, saukin yasa shorts daga ciki amma chest ɗin shi a buɗe yake fari kal, Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah wani irin bacci ne ke fusgar shi, ga uwar yunwa yana ji, ji take tamkar ta bashi tea ɗin abaki yasha, cikin sauri ta haɗa masa tea ɗin a cup ta ɗan tura masa agabansa tace "gashi nan,' buɗe blue eyes ɗinsa yayi a hankali sannan yakai hannu daker ya ɗauki cup ɗin yakai bakinsa yana ɗan kurba da zafinsa, ya sha ba laifi kusan sau biyu tana ƙara masa yana shanye wa, Bayan ya kammala tace "kayan dinner ɗin fa na mayar dasu"? Ta tambaya cike da jin tsoran amsar da zai bata, "In akwai fruits ki haɗo mun," ya faɗi tare da mayar da jikinsa ya kwantar akan pillow, Tattara kayan tea ɗin tayi sannan ta fuce dasu ta ajiye su a tray din dake ɗauke da warmers na abincin sannan ta ɗauke shi ta fita dashi kitchen ta shiga ta ajiye su, sannan ta ɗebo mashi fresh fruits acikin fridge, A plate ta zuba mashi su sai da tafara yayyanka mashi su sannan, tana ƙoƙarin fita suka ci karo da Haroon tsaye abakin ƙopar kamar aljani, Da ƙarfi ta furta "A'uzu billahi minashshaiɗanin rajim,' Haroon ya fashe da dariya tare da cewa "Ni ne shaiɗan ɗin, ko kin ga ƙaho akaina ne? "Eh," ta bashi amsa, Yatsina fuska yayi yana bin jikinta da kallon frm up to down kafin yace "Haɗaɗɗiyar Sura," tace "Tubarkallah masha Allah," Murmushi yaɗanyi kafin ya kuma cewa "ki dai bi ahankali naga kamar zakiyi rawar kai Kada kici ka zaƙewa mana domin kuwa har yanzu fa baki da wani matsayi acikin gidan nan, duk inda za'aje adawo bakya wuce ƴar aiki, sannan na lura kina shisshige ma wancan ifritun ko? to inaso ki sani wancan dashi da dutse duk ɗaya suke indai agame da feelings ne, mace bata gabansa koda zai kula matan ma bana tunanin irin ki, ae ma zaren ba kalar yadin bane iska ce kawai zata wahalar da mai kayan kara......... tun da yasoma magana idon sehrish suka soma ciccikowa da kwalla amma bata bari hawayen sun zuba ba, ganin zai bata mata lokaci yasa ta bi ta gefensa ta fuce da sauri, tana jiyo dariyarsa sam tarasa gane ma haroon, batasan mai ta tsone masa ba, time ɗin da tashiga bedroom ɗin SGR samun shi tayi yana ta faman sharar baccinsa alamu sun nuna cewa ma tunda tasa ƙafa ta fuce ya fara baccin, tsayawa tayi akansa tana kallonshi hannunta na riƙe da fruits ɗinsa, Yayin da idonta Suke cike da hawaye saboda kalaman haroon ita kanta tasani tabbas SGR ba tsaran yinta bane kwata-kwata bama haɗi, jinjina kanta tayi aranta tace "nasani kafi ƙarfina nesa ba kusa ba, kuma nasan cewa kafin ni akwai wanda suka ruga ni faɗawa wannan tarkon bila adadin, Amma inaji araina babu wadda zata soka dan Allah kamar yadda nake sonka, tun bansan ya kamannin fukarka suke Ba, da sunanka kawai nakamu da tsananin ƙaunarka kuma zan cigaba da addu'a akan hakan koda bazan ci nasara ba aƙarshe...Ana ahabbuk kasiran BABBAN YAYA.........❤💘 Wani irin juyi SGR yayi har sai da Sehrish ta ɗan tsorata gudun karya farka ya ganta, gyara kwanciyar shi yayi, yadda yake sakin numfashi anatse yana bacci ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba, Ajiye fruits ɗin tayi saman table sannan ta matsa a hankali cike da fargaba ta janyo lallausan blanket ɗinsa jikinta na ɗan kerma ta samu ta hayo dashi jikinsa ta lullu6a masa har zuwa neck ɗinsa, Murmushi ta ɗan saki ganin ta kammala batare da ya farka ba, juyawa tayi ta tattaka izuwa inda makunnin hasken ɗakin yake ta kashe mashi shi, nan take ɗakin ya soma kyalli yana bada wani irin haske har sai da ta ɗan razana, ashe furnitures ɗin dakine masu wannan sparkling light ɗin launi daban daban suke badawa, aduk time ɗin da aka kashe hasken ɗakin Yayi dark gaba ɗaya su kuma sai su soma bada nasu hasken mai launuka, fuska ɗauke da murmushi sehrish ke kallon wannan ikon Allan Bin su take yi da kallo tun daga Bed ɗinsa da bedside table ɗinsa, drawer ɗin da ke ɗauke da mirrow jerin wurin Closet ɗinsa gaba ɗaya sun ɗau hasken nan, sai taga ya ƙara yi mata kyau sosai, Lalla6awa tayi ta koma inda yake kwance tana kallon fukarshi yadda eye lashes dinsa suka fito radau zira zira dogaye kasancewar idon na'a rufe, sun kwanta luf, Addu'ar bacci tashiga yi mashi saboda tasan cewa bai samu damar yi ba ayarda ya kwanta ɗin nan agajiye ta jima sannan ta ɗan tattofa masa ajikin bargonsa, kamar karta bar ɗakin haka take ji (Nace ba mai zai hana kawai ki kwana anan Ehen 😂) hannu tasa ta ɗauki Kayan marmarin dake acikin plate ɗin sannan ta fuce dashi bakowa a babban falon Dama tun fitowar farko da tayi duk sun kammala dinner ɗinsu sun shige cike aranta tace "Allah sarki su fawan hada rashin su yasa yanzu basu cika haɗuwa atare suna cin abinci ba ko zama a palor suna fira, ko yaushe zasu dawo? Duk da ina tsoran abunda zasu ce in suka ganni a Matsayin mace, Especially fawan nasan halinsa sosai baijin magana shine ya ta6a bani horo harna galabaita," ta ƙarasa zancen zucin nata , bedroom ɗinta ta wuce da fruits ɗin saboda dama itama bata ci komai ba, asaman gadonta ta zauna tsakiyar gadon ta lankwashe ƙafa tana shan fruits ɗin tass ta shanye su sannan ta ajiye plate ɗin asaman side drawer ɗinta, dama empty yake tunda ta rotsa ma haroon fitilar saman shi akai,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47