Chapter 22
Chapter 22
suka ɗago atare, shiru tayi tana ɗan kallonsu, atare suka yatsina fuska suna yi mata wani irin kallon Tara saura kwata, ƙasa da murya Jahan yayi tare da cewa "Ayaan kalli yarda junaid ke fira da wancan yarinyar, shi junaid kowa nasa ne, baya tsoran mutane sai sunyi masa Illah," yayi maganar cikin nuna damuwa Ayaan yace "ba kai kaɗai ba jahaan, ni ma abun na damuna wlh, shiru kawai nayi amma na lura da yadda suke shiri, bazan ƙyalesa ba dole na buga masa warning Allah, Jahan yace "gasky kam, janyo shi yakamata muyi a ɗakin mu, muja masa kunne tunda shi shashasha ne kowacce baƙuwar fuska shige mata yake yi, sai kace ba Jinin mu ba," Ayaan yace "kwarai kuwa, ae shi junaid da kake ganinsa half cast ne, ruwan Abba ne dana Mommyn mu ya ɗauko, mu kuma ruwan mommy ne kawai ajikin mu, banda na daddy," Wannan maganar ta Ayaan tasa kanal yusuf fashe wa da dariya ashe duk yana jin firar tasu saboda shine kusa dasu a jere, ɗagowa su kayi suna kallonsa dukansu hada Abban nasu da junaid da sehrish da azmeee, Abban nasu yace "in ce dai ko lafiya? Kanal yusif yace "babu komai Abba, gasu nan su Ayaan da jahan ne suke fira su faɗa maka abunda suke cewa ka ji," tunkan Abbansu ya tambayesu suka haɗa baki wurin cewa "Babu komai Abba, firar wani film muke yi,' girgiza kai kawai Abbansu yayi, Haroon kuwa cewa yayi "Allah yayi wa ɗan iska uwa koda ta kara ce," ya faɗi yana kallonsu salon jan faɗa kawai, Babu wanda ya tanka masa miƙewa Ayaan da jahan su kayi tare da yiwa Abban su sallama suka fuce, 💪 Fito wa marshal Omar yayi daga upstairs yana saukowa down jikinsa sanye da jallabiya ash colour sai faman ƙamshi yake yi, tunkaro su yayi Abbansu na ganinsa yafara fara'a yana cewa "Omar sai yanzu ka tashi? tun ɗazu nake ta faman waige-waige naga ta ina zaka 6ullo, Ɗan ƙayataccen murmushi yasaki tare da cewa "Gm Abba ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya," "Alhamdulillah Son, Samu wuri ka zauna na baka abinci a baki," cikin zolaya yayi maganar su kuwa sauran dariya su kayi, ɗagowa OMAR yayi tare da gaishe da Azmee ta amsa mashi, sannan su kuma Su kanl yusif da junaid suka shiga gaishe shi, Haroon yace "Barka da fitowa Damusa mai maganin ƙananun ƴan iska," ɗan harararsa Omar yayi tare da cewa "Zaka fara wannan tsokanar taka ko? To ka shiga taitayin ka ko yanzun nan na saita maka waɗannan haƙoran naka, don naga ba'a jere suke ba,' shima da zolaya yayi maganar ayayin da yake zama azmee kuma ta soma zuba masa breakfast ɗinsa, Mayar da idonsa yayi kan JUNAID dake ta faman sakar masa murmushi yace "My shagwa6a boy, irin wannan kallon haka da kake mun ko kana buƙatar wani abu ne? Cikin jin kunya junaid yace "Babu komai ya Omar kawai inaso inta kallon ka ne, aduk lokacin danayi kewarka," Murmushi Omar yayi kafin yace "Ae da ka sani jiya ka shigo bedroom ɗina mun kwana tare," Junaid yace "ae Abba bazai bari ba, Kishi yake yi," gaba ɗayansu suka fashe da dariya jin abunda junaid yace, Abban nasu kuwa murmushi kawai yayi tare da ɗan jinjina kai yana kallon junaid ɗin, Haroon yace "Ae na Lura da yadda Abban mu ke ji dakai, kamar kai kaɗai ya haifa bayason komai ya same ka,' Junaid yace "Yaya haroon ka ta6a ganin inda mutun ke wasa da bugun zuciyarsa? to aeni zuciyar Abban tamu ce gaba ɗaya shiyasa Yafi sona," yayi maganar wit proud, ta6e baki Haroon yayi yana kallonsa, MARSHAL OMAR yace "Ae bama Abban mu kaɗai ba Haroon, Junaid farin cikin kowan nan mune acikin gidan nan, bamu son wani abu ya same shi domin tamkar mu yasha fa, JUNAID BUGUN ZUCIYAR FAMILY ɗin mune gaba ɗaya," Kanal yusif ya ƙara da cewa"Maganarka gaskiya Ce Yaya OMAR, Ni kaina aduk lokacin dana aza idona akan na baby junaid wlh farin ciki ne ke ziyarta ta, kuma aduk lokacin da wani ya 6ata mun rai junaid ne ke lallashi na da kalaman sa masu kwantar da hankali, tabbas shi Yaro ne amma yana da baiwar iya sarrafa harshe wurin farantawa mutane," Har cikin zuciyarsa yake wannan bayanin, junaid kuwa farin ciki ya hanasa idasa shan cornflakes ɗin dake agabansa, haka zalika Abbansu murmushi ne a fuskarsa saboda bai da Burin daya wuce yaga ana yabon Jininsa, kuma ma Junaid, Haroon kuwa tuni zuciyarsa tayi baƙiƙƙirin ji yayi bazai iya ci gaba da zama ba, don haka da hanzari ya miƙe tare da fuce wa daga babban falon gaba ɗaya, sam ba wanda ya damu dashi bare su son halin dayake ciki, Duk fa wannan abun dake faruwa a kunnan Sehrish tana sauraron su, sam tagaza gaishe da Marshal Omar tsoran ta kada ya ƙi amincewa da ita duk da ta lura bazaiyi Tsauri ba, Sai da tabari duk sun natsu wuri ya ɗanyi tsit sannan ta ɗanyi gyaran Murya tare da cewa "YAYA OMAR ina kwana," Jin Muryar mace yasa shi saurin ɗagowa yaga wacece karaf fararen idanuwansa suka sauka akan na SEHRISH, ae baisan lokacin da ya fesar da Tea ɗin daya kur6a abakinsa ba, hankali atashe yake kallonta, Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da miƙewa tsaye idonsa akan na sehrish wadda ta gama tsorata dashi ganin yadda ya firgita da ganinta kamar yaga wata ALJANA, tuni jikin sehrish ya soma kerma, ita kanta azmee ta tsorata da ganin reaction ɗin Omar akan Sehrish haka zalika Abbansu kanal yusif da junaid duk mama ki ya ɗaure musu kai Nuna ta da hannu Marshal Omar yayai tare da cewa "Keeeee !!!!!!!!!! " gaba ɗaya ya razana da ganin yarinyar, ganin haka yasa kowannan su ya tashi tsaye suna kallonsa, Abbansu yace "Omar meya faru ne? Na manta ban faɗa maka ba game da yarinyar nan ba, ƴa Ce Allah yabani daga sama.... .kallonsa Omar yayi a ruɗe kafin ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda tuni idonta sun cuccuko da kwalla saboda tashin hankali, da hanzari OMAR ya bar dining ɗin yayi saurin haye wa upstairs part ɗinsa, zuciyarsa a cunkushe sam yagaza gane ma Idonsa dayake yi masa Gizan Fuskar Hosana da Jahad a fuskar wannan yarinyar daya gani a yanzu, Bedroom ɗinsa ya shiga hannu yasa ya ɗauki wayarsa daya ajiye asaman pillow, cikin hanzari ya daddana layin aunty babba ya buga mata Call, kusan 3 times yana kira bata shiga, numbar Hafsat ya kira itama tana ringing ba'a ɗagawa, Wurgi yayi da wayar saman gadonsa, tsayawa yayi yana faman sauke ajiyar zuciya, hannu yasa ya dafe kansa tamkar wanda ke fama da ciwon kai, tabbas ransa na basa cewa Ba fuskarsu hosana bace a fuskar yarinyar, ya sawa ransa cewa tsananin Son da yake yi ma yaran ce da ƙaunar da yake yi musu da kuma kewarsu da yayi ya sanya Fuskarsu keyi mashi gizau afuskar yarinyar daya gani ayanzu, tabbas Omar yayi Confusion ɗin kansa, ya rikita tunaninsa bazai ta6a yarda da abunda idonsa ke nuna masa ba akan Waccan Yarinyar................ Ajiyar zuciya yasaki aransa yana ƙara jin cewa bai kyauta musu ba da baije
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47