Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin shessheƙar kuka, "Da gaskiyar hosana,Nima ina tunanin hakan Allah yasa karta faɗama auntyncan inda ƴar uwarmu take, amma dai ni inason naga matar na roƙeta akan ta faɗa mana inda sehrish take,yakamata musan inda take, wane hali take ciki, gashi yanzu sai mutuwa akeyi Ya Allah kasa sehrish tana araye har mu haɗu," tayi maganar idonta cike tab da hawaye, daga bisani ta kalli hosana tace "ki zauna hosana kada ki fito bari ni naje nayi magana da matar na roƙe ta, ta faɗamun inda rishi take," Hosana tace "toh," sannan tasamu wuri ta zauna gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya, Cikin sanɗa jahad ta futo daga kopar ɗakin ta tsaya tana ɗan leƙa kanta, mutane tagani gasu nan sai faman zarya sukeyi acikin babban falon, A hankali ta miƙi hanya ta soma tafiya tana faman waige-waigen neman hajjaju, ta ɗanyi nisa a tafiyar ta ta, tajiyo magana daga bayanta ana cewa "Nasan cewa ni kike nema ko"? Cikin sauri jahad ta juyo bayanta, hajjaju ce tsaye tana kallonta fuska ɗauke da murmushi, Ajiyar zuciya jahad ta saki sannan itama ta mayar mata martanin murmushin tare da gaishe ta, hajjaju ta amsa mata da cewa "Nayi mamakin ganin ku, anan gidan ko ba'a faɗamun ba nasan cewa kunsha wahalar rayuwa don nasan Laila sarai muguwace bata da Imani,kuma tana sanar dani game daku a waya sai dai bansan cewa ku bane," Jinjina kai Jahad tayi tare da cewa "Munsha Wahala sosai tamkar ba zamu rayuwa ba,dan Allah ki faɗa mana ina Sehrish take? Munyi kewarta sosai, rabon mu da ita, tun da ta tafi aikin nan da kika sama mata,bayan wasu kwanaki hosana ta 6atar mana da wayar da muke amfani da ita wurin kiranta, shikenan rabuwarmu da ita......' jahad ta ƙarasa maganar idonta cike tab da kwalla, ɗan shuru hajjaju tayi tana kallonta gwanin ban tausayi kafin tace "Kiyi haƙuri, amma bazan iya shaida a ina sehrish take ba nikaina,saboda nasaba hulɗa da yara ina sama musu aiki, bazan iya tuna a wane gari nakai sehrish ba, bazan iya tunawa ba......' Jin hakan yasa Jahad fashe wa da kuka mai cin rai, matsawa hajjaju ta ƙara yi gab da jahad tasanya hannunta tare da dafa kafaɗunta tace"kiyi haƙuri Jahad, ina mai matuƙar jin takaicin gaza taimaka maku akan halin da kuke ciki, haƙika kun ga rayuwa, amma ni abunda nakeson sani taya akai kuka haɗu da Omar? bayan naji labarin rasuwar tsohuwa ya gigita ni matuƙa, sannan naji labarin cewa ana zargin cewa kune kuka bata poison amma bansan ya ƙarshen labarin yake ba,'. Cikin shessheƙar kuka jahad tace "bayan tsohuwa ta rasu, mutane suka ce mune muka kashe ta alhalin mu bamu da masaniya akan mutuwarta, shine aka kaimu police station, munsha Wahala sosai saboda bamu da sheda, ana shirye shiryen za'a miƙa case ɗinmu kotu, hussana tayi rashin lafiya shine dalilin dayasa ƴan sanda suka tafi da ita asibiti tare dani, Acan ne Allah ya haɗamu da yaya Omar shine ya kwace mu daga hannun police ɗin kuma ya kashe case ɗin gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya, Murmushi hajjaju tasa ki tare da cewa "Allah sarki Omar mutumin kirki ne sosai, yana da tausayi inama ace tunfarko ba nan ya kawo ku ba, wlh da kun more rayuwarku,amma sai dai kash yayi kuskuren jefa rayuwarku cikin haɗari batare da sanin shi ba, Amma insha Allah Laila bazata ta6a cin nasara akanku ba,' Jinjina kai kawai Jahad ke yi, bayan sun ɗanyi shiru hajjaju tace "Muje ɗakin da kuke,ina son ganin ƴar uwarki danaji kin kirata da hussana, bazan manta ba itace a lokacin kwance saman medical bed ansa mata oxygen tana shaƙar numfashi cikin mawuyacin hali, Amma yanzu naganta taji sauƙi sosai jiki yayi kyau,' hajjaju ta faɗi da ɗan murmushi a fuskarta yayin da suke nufar ɗakin hafsat atare, Suna shiga suka samu hussana atsaye sai faman zirga-zirga take yi burinta kawai jahad tadawo kusa da ita, Tsayawa tayi ganin sun shigo tare da matar, Murmushi hajjaju ta sakar ma hussana tare da ƙarasawa inda take ta rungumo ajikinta, tana ɗan bubbuga bayanta tace "nasan ke baki sanni ba,sabosa lokacin kina kwance rai hannun Allah, amma ni nasan ki saboda naganki a lokacin, naji daɗi sosai dana ganki cikin ƙoshin lafiya, Hajjaju ta ƙarasa maganar tare da janye hussana daga jikinta, ita dai hosana kallonta kawai take yi don batasan ta ba, mayar da idonta tayi kan jahad tace "ta faɗa maki inda sehrish take? Jahad tace "a'a hosana, tace itama ta manta inda takaita aiki saboda ta saba kai yara aiki bazata iya tuna inda takai su ba," Jin haka yasa Hosana fashewa da kuka tana cewa "..yanzu shikenan bazamu ƙara ganin sehrish ba.... Hajjaju tace "Ki daina kuka hosana,wayace maki bazaku sake ganin sehrish ba? Ki daina wannan tunanin Insha Allah zaku haɗu da ƴar uwarku, abunda nakeso daku kawai ku cigaba da addu'a insha Allah zaku dace," Jahad tace "kullum muna cikin yin addu'a,Kuma zamu cigaba da yi har illa masha Allah" Murmushi hajjaju ta kuma yi sannan tace "Ni zan wuce,Ku kula da kan ku,Allah ya Albarkanci rayuwarku, yaci gaba da tsare ku aduk inda zaku kasance arayuwar nan," Suka amsa mata da "Amin," sannan tasa kai ta fuce tana mai jin rashin daɗin gaza taimaka masu da tayi na ƙin faɗa masu inda ƴar uwarsu take, bayan ta son inda take, Komawa sukayi atare suka zauna jikinsu amace, Shin mai zai biyo baya?😥 Bayan wasu lokutta, duka baƙin da suka zo suka tafi gidan yayi tsit ba hayani, suna cikin wannan zaman na jimamin Ga samu ga rashi, na hajjaju da suka haɗu da ita yau, sun son itace kaɗai zata faɗa masu inda Sehrish take gashi itama tace bata sani ba, hakan ba ƙaramin kashe musu zuciya yayi ba, daker suka samu bacci ya ɗauke su, _______________________ Fitowa daga wanka general ishaq yayi jikinsa sanye da gajeran wando, Closet ɗinsa ya nufa tare da sa hannu ya buɗe ya ɗauko jallabiya ya zumbula ajikin shi, Sarai yasan cewa tana ɗakin Amma sai yayi tamkar bai ganta ba, sai da ya kammala kimtsa kansa sannan yace "Ya Rashin Ji"? Ya tambaya yana kallon kansa acikin Mirror, mamaki ne ya kama aunty babba jin abunda yace, tana zaune daga gefen gadonsa tace "Nifa ce ba hafsat ba," ta faɗi tana kallonsa Ishaq yace"Nasani ae, dake nake magana, duk rashin jin hafsat ae bata kai ki ba, kefa tamkar 6eran gida kike wurin 6arna da rashin ji," ɗaure fuska tayi jin abunda yace rai a6ace tace "Alamu sun nuna cewa ba kayi kewata ba ko? shiyasa kake gayamin magana, ko da yake dama kai ae ba ka iya soyayya ba, Iya ruƙe bindiga kaɗae ka sani," ......juyowa Ishaq yayi yaɗan kalle ta tare da ta6e bakinsa yace "ban iya soyayya ba, amma gashi nan har kin haifi hafsat dani ko? Naga wannan ma ae wani sashe ne na soyayya," ya ƙarasa maganar tare da wuto wa ya haye saman gadonsa ya kwanta yana cewa "Idan kin tashi fita daga ɗakin kada ki manta, ki kashe mun hasken inaso nayi bacci," a ƙule aunty babba ke kallon shi, can kuma ta miƙe fuuuuu ta nufi hanyar fita

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47