Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

Murmushi Hafsat tasa ki tana cewa "nasan mai ki ke tunani JAHAD, tabbas abunda kike tunani gaskiya ne, POISON nasanya muku a abincin saboda wannan ce hanya mafi sauƙi da zamu kawar da ku acikin arayuwarmu, kuma zaku huta da wahalar zaman duniya," Hankali atashe Jahad ta Zazzare ido waje jikinta na kerma tace "POISON!!!!!!!!!!!!!! "*🪩🪩🪩ABBAN SOJOJI🪩🪩🪩* •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·15-16•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•· ____________(✪)____________ Story & Written by *BOSS BATURE* Firgit jahad tayi daga zurfin tunanun da ta shiga tana faman sauke ajiyar zuciya, ɗagowa ta ɗanyi ta kalli hafsat samunta tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "Tun ɗazu na lura da kallon da kike yi mun Jahad, na menene? ɗan sunnar dakai jahad tayi tace "Babu komai kawai ina mamakin yarda kika canza mana ne ba kamar da ba, kin nuna tausayi agare mu, ba muyi tunanin haka ba, Hafsat tace "Nima kaina nayi mamakin yarda na canza wurin nuna muku tausayi, bayan ba hali na bane gaskiya, tun ina yarinya bani da tausayi ko kaɗan kuma bana son mutun mai tausayi, ban sani ba ko kunayin addu'a ne shiyasa Allah ya kawo muku sauƙi ta 6angare na.....' ta ƙare maganar tana kallonsu, Jinjina kai Jahad tayi jin abunda hafsat tace, Lallai ne Allah ne ya amshi addu'arsu ya kawo musu sauƙi ta wurin hafsat, Ajiyar zuciya Jahad tasa ki tare da juyawa ta kalli hosana wadda ke zaune wuri da ido, taci ta ƙoshi tayi hani'an, Hafsat tace "Ga maganin da dr yace abaki, tun da kin kammala cin abincin bari na baki ki sha, sannan zuwa anjima insha Allah zamu koma gida," jahad tace "Allah ya kaimu lafiya," "Ameen," ta amsa mata sannan tasanya hannu ta ɗauki ledar maganin, ta shi ga fiddo su tana duba su, kafin tasanya hannu cikin basket ɗin da tazo dashi ta ɗauko robar ruwa, ta buɗe ta bayan ta ciro maganin ta miƙa ma hosana tare da ruwan tana kar6a tana sha, haƙiƙi su Hosana da jahad ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, saboda sun ga tausayinsu ƙarara a fuskar Hafsat kuma da alamun zasu samu sauƙi ta 6angarenta, *Shin Ya maganar matar da ta ba Hafsat miliyan shidda don ta zubar mata dasu Jahad? Kuna ganin zata fasa wannan aikin ko kuwa*? 😳 *AUNTY BABBA* 😈 Sam ta gaza samun natsuwa hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hafsat ta fara damuwa da twins ɗin da OMAR ya kawo, tabbas dole ta ɗauki mataki akan hakan, kuma haryanzu tana akan bakanta na sai tasa an zubar mata dasu Hosana da Jahad, *Tabbas dole na ɗauki mataki akan hakan* tayi maganar tare da dakatawa daga zirga zirgar da takeyi acikin ɗakin nata, fitowarta kenan daga wanka, ta zumbula doguwar rigar Buba ta Material, hannu takai ta ɗauki wayarta dake ajiye saman stool dake agaban mirror, cikin hanzari ta shiga contact ta dannawa wata number kira wadda tayi saving ɗinta da *BABA ALAMU* Nan da nan kiran yashiga wayar ta soma ringing zuwa wani lokaci mai numbar data kira ya amsa wayar, Cikin sauri tace "Assalamu Alaikum," daga can 6angare wata murya kakkausa ta gawurtattun ƴan iska ta amsa mata da cewa,"Hajiya Laila manyan gari, ashe kuna neman mutane? Ae nayi tunanin daga in da amfanin mutun ya ƙare a wurinki yazama shara......' dakatar dashi Aunty Babba tayi da cewa "Baba Alamu ! mu aje wannan gefe, wlh ina cikin tsananin damuwa ne, tunawa dakai yasanya na kira ka domin nasan kai kaɗai ne zaka iya yi mun wannan aikin.....' ta ɗan dakata tana jiran amsar da zai bata , Baba Alamu yace "Ae dama ke ba'ki ta6a neman mutun sai in buƙatarki ta taso, tun da ansan muna da amfani ae a rinƙa ɗan kiran mu ana bamu hasafi don tafiya tayi kyau ko?, yanzu dai faɗa mun me kike so in aiwatar kawai ! Wa kike so akashe miki har lahira? Ko wa kike so In Naƙasa Miki kasusuwansa ajefar bayan Duniya?😳 Dariya aunty babba tayi cikin jin daɗi tace "Yawwa Mutumina, dama nasan kaine kawai zaka iya share mun hawaye na, abunda ke faruwa wani ƙanin Mijina ne wlh ya tsinto wasu ƴan mata tagwaye ya kawomin a gida na, na tsani yaran nan ko ganin su bana son yi, saboda zasu tarwatsamun target ɗina abunda nakeso kawai so nake kazo ka ɗauke su Ka fitar mun dasu daga gidan nan ka kai su can bayan gari ka jefar mun dasu Can cikin ƙurmin daji wanda zasu rikice su gaza gane hanyar da zasu fita daga cikin shi,"😳 tamkar tana agabansa haka take masa bayani tana faman cizon la66a, 😠 fashe wa da dariya baba Alamu yayi daga bisani ya tsagaita yace "Ƙaramin aiki kenan, ni nama yi tunanin wani za'a kashe maki ne yanzun nan mu kai shege lahira, amma tun da wannan ne kada ki samu damuwa, yanzun dai bana nan kinsan naje lagos ƙarƙashin gada amma maƙo mai zuwa bi iznil lahi, aikin ki zai kammalu, ƴan Canji kawai zaki tanada " Aunty Babba tace "in dai wannan ne an gama, zanyi maka biya na musamman babban kaso mai tsoka, Baba Alamu yace "Shikenan sai kin jini, da zarar na dira kaduna zan zo da rugwagwar mota ta na kwashe Maki Sharar azubar abayan gari,'😂 Jinjina kai aunty babba tayi har wani sauke ajiyar zuciya take yi jin burinta zai cika na kawar da su Jahad, Sun jima suna waya da baba Alamu kafin daga bisa sukayi sallama, ta ajiye wayar saman mirror tana cewa "Yanzu abunda ya rage mun shine, na dakatar da Omar don nasan zai iya zuwa yace zai tafi dasu na lura da hakan I ave to do something ❗‼ .........!👷wani irin shu'umin murmushi tasa ki, saboda plan ɗin da ta tsara, ********* Sai wuraren bayan Sallar La'asar sannan dr yayi discharge ɗinsu daga asibitin kamar yadda hafsat ta buƙata don bata son zaman su a asibitin gudun kada Omar yayi musu Dirar Mikiya, duk da dr yaso ya ƙara ma hosana Jini amma ta hana hakan sai dai tayi alƙawarin cewa zata mai do ta asibitin Next time, A hankali take driving ɗinsu acikin motar, hosana na'a a back seat kwance sai faman sharar bacci take yi, yayin da jahad ke agefen hafsat dake driving, adai-dai wani Store ta tsaya da motar, sannan ta kalli jahad tace "Ki kula yanzu zan dawo," Jahad ta amsa da cewa "Toh Aunty" Shiga cikin wurin tayi bayan wasu mintuna tafito hannunta ruƙe da leda, ta buɗe motar ta shiga miƙa ma jahad ledar tayi tace "Ruƙe wannan a wurin ki," Amsa jahad tayi ta ƙanƙame ledar a hannunta, sannan hafsat taja motar suka tafi gida kai tsaye, Bayan tayi parking suka fito daga motar daker jahad tasamu hosana tafarka ta ruƙe hannunta suka nufi ciki hafsat na biye dasu, sai faman jin fargabar haɗuwa da Aunty babba suke yi, Aikuwa suna shiga suka same ta zaune a babban falon saman sofa tana faman danna wayarta, tana ganinsu ta miƙe tsaye tare da cewa "Sannun ku da dawowa, Allah sarki hosana da jahad kuyi haƙuri ban samu damar zuwa asibiti ba na dubo ku, Ya jikin naku"? ta faɗi cikin nuna tausayin su, ai ba su jahad da

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47