Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Abban Sojoji Book Two Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

da kallon da Omar keyi mata ba, juyawa Sgr yayi don yaga me Omar yake kallo ne karaf idonsa suka sauka ana sehrish wadda itama idon nata na akanshi, from up to down ya kelle ta kafin yace "Ke zonan," gabanta ne taji ya faɗi rass tayi firgit tana kallonsu, hankali atashe ta tunkare su gabanta na ɗarr!ɗaarr ta ƙarasa inda suke dab da Babban yayan nasu daya kira ta, Hannu yasa tare da ruƙo jalbabar dake ajikinta, saboda tsananin tsoro sai da sehrish ta kusa sakin fitsari tuni jikinta yasoma kerma kaf!kaf !!kaff! cikin sanyayyiyar muryar nan tasa ta natsastsu yace "Menene wannan haka ajikin ki,"? Ya tambaya in serious matter batare da ya aza idonsa akanta ba, Murya na rawa sehrish tace"hi..hij..hijabi ceeee...' "Masallaci zaki je ne"? Ya tambaya yana jiran amsa, "A'a fita zamu tare da aunty azmee," Cire hannunsa yayi tare da nuna mata hanya yace"maza ki koma, ki cire wannan abun, bana son sake ganin shi," cike da mamaki Omar ke kallon sgr har dai yagaza yin shiru yace "Rafayet nan fa ba Us bane Nigeria ce, kuma wannan shine best outfits da yace mace musulma tayi, Domin rufe surar jikinta daga jan hankalin mutane akanta saboda tsaro,' girgiza kai sgr yayi tare da cewa "ban yarda da wannan shigar ba, shin Omar taya mutun zai iya motsi acikin wannan abun"? Ya tambaya yana nuna hijabin jikin sehrish,😂 Fashewa da dariya Omar yayi kamar kamar me, ganin yarda Sgr ya haƙiƙance akan hijabin dake ajikin yarinyar, shi a ganinsa takurace kuma mutun bazai iya motsi acikinta ba, daƙer ya dakatar da dariyar tasa ya kalli sehrish tare da cewa "Ki faɗa masa yarda kike motsi acikinta may be ya fahimta," ɗan murmushi sehrish ta saki ita kanta abun ya gama ɗaure mata kai, ɗagowa da hannayenta tayi tare da cewa "Ga hannun hijabin nan, tun da na fiddo da hannun acikinsa lafiya lau nake motsi acikinta," ta ƙarasa bayanin tana kallonsa Jingina bayansa yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa "Its Okey, u can go,' har ta juya zata tafi Omar yace "Ya Sunan ki ne? Juyo wa tayi ta kallesa da murmushi a fuskarta tace"SEHRISH" Omar yace "masha Allah suna mai daɗi, amma menene ma'anarsa? ya tambaya yana kallonta, *kyawawan halayyu na mutun," ta bashi amsa, *ina fata zaki nuna mana waɗannan kyawawan ɗabi'un acikin gidan nan, har ma ki zama alkhairi agare mu," omar ya faɗi da ɗan murmushi a fuskarsa, duk Sgr na sauraronsu duk da ya ci gaba da dannar wayarsa, Sehrish ta amsa masa da cewa "Insha Allah," sannan ta wuce Sai lokacin Sgr yace "Ashe kana surutu har haka Omar? Kallonsa Omar yayi tare da cewa"Yarinyar ce tana tattare da wani abun al'ajabi a fuskarta shiya sanya Na sake mata," "Ba kowace baƙuwar fuska yakamata ace kana sakemawa ba irin haka ba, Mata Basu da tabbas they're trouble makers," acewar Babban yaya, ƴar dariya Omar yayi batare da cewa komai ba, Sehrish kuwa kitchen ta wuce ta zubo musu coffee tare da snacks a plate Cikin tray sannan tadawo inda suke tare da ajiye masu saman Table, Omar yace "thank u miss Sehrish," Murmushi tayi masa sannan ta juya ta nufi ɗakin azmee tunkan ta ƙarasa ɗakin nata sai ga Azmee ta fito itama ta kammala shiryawa cikin atampha ja, ta aza babban mayafi milk colour launin takalminta ƙafarta, atare suka fuce suna jiran isowar junaid, Ba da jimawa ba sai ga junaid ya fito daga upstairs yana saukowa down sai faman zabga murmushi yake yi, jikinsa na sanye da haɗaɗɗiyar shadda gezner blue colour mai maiƙo sai faman ɗaukar ido yakeyi kai kace wani sabon ango ne, shaddar tasha aiki a wuyanta tsantsararre, hannunsa na ruƙe da wayarsa haɗe da key ɗin motarsa, Lokacin daya ƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin, gaba ɗaya Marshal Omar da Sgr suka bishi da kallo, Zagayawa yayi inda babban yayan nasu yake yana isa ya manna mashi kiss agefen fuskarsa sannan yace "Zan fita, saina dawo," ko amsa bai jira ba cikin sauri ya lalla6a ya fuce yana cewa "yaya Omar kayi masa bayani, mu mun wuce ," Girgixa kai kawai SGR yayi sam ya kasa magana, wato junaid yasan cewa zai iya dakatar dashi daga fita shine yayi dabarar tserewa, Murmushi Omar yasaki tare da cewa "Junaid kenan ! komai nasa na burgewa, ya cika ƙiriniya ga shegen wayon tsiya, saboda kada ka hana shi fita shiyasa ya gudu bai jira amsarka ba," yayi maganar yana kur6ar coffee ɗin da sehrish ta kawo masu a cup, "Ina zasu je ne"? Sgr ya tambaya yana kallonsa, Omar yace "Gidan Uncle Abusufyan na aikesu, inaso zanyi amfani da gidan ne akwai wasu marayune da zan zuba acikinsa kwanan nan," Sgr yace "Omar kenan, meyasa baka sanarmun ba? ko ni ba'a buƙatar gudummuwata ne? ya faɗi yana kallonsa, Murmushi Omar yasaki dama sun saba indai irin haka ne, muddin akace aikin lada yasamu, to har rububi suke yi wurin bada taimakonsu, kowa burinsa ace da dukiyarsa za'ayi amfani wurin bada tallafi sam basa gajiya da irin wannan (Kaji masuyi don Allah) Shiyasa dukiyar tasu kullum hau hawa takeyi kamar kamar me, a ƙalla su kansu basu son adadin gidajen marayun da suka buɗe ba a kasashe daban daban kuma suke ɗaukar ɗawainiyarsu da komai, Manyan asibitoci kuwa da suka buɗe ba iyaka, wanda suma duk kyauta ne ake duba marasa lafiya acikinsu, ga makarantu na marayu da marasa hali da suke dasu ba adadi, wannan ba komai bane ba, kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke yi na taimako, Ya Allah ka bamu arziƙi mai albarka wanda zamu amfana dashi kuma ƴan uwanmu musulmai suma su amfana dashi, ba irin arziƙin da mutun zai mallaƙe ba, ka ga ko cikin gidansa fama ake dashi basa ciyuwa balle na waje su samu😧 *****GIDAN ABUSUFYAN******* Haɗaɗɗiyar daula, Aljannar duniya tun daga kan Tanƙameman gate ɗin gidan Golden colour & brown sehrish ta saki baki tana kallo Ikon Allah, Ba don daga gidan Abban sojoji ta fito ba da sai tace wannan gidan a dubai yake, tsayar da motar junaid yayi abakin gate ɗin sannan ya fito daga cikin Motar, ya nufi jikin gate ɗin, tunkan ya isa ya danna madannin da ke ajikin key ɗin gidan a hankali gate ɗin ya soma zugewa da kansa daker daker yake tafiya saboda gidan ya jima ba'ayi amfani dashi ba tunda Abusufyan yabar Nigeria a fusace gidan yake ahaka garƙame, ganin zai 6ata musu lokaci yasa junaid sanya hannunsa yana ƙoƙarin turasa da ƙarfinsa don yayi saurin f Buɗewa, aikuwa nan take zufa tasoma wanko masa kamar wanda aka watsa ma ruwa a fuska dama jiki bana wahala ba, muryarsa kamar zaiyi kuka yace "Aunty Azmee wai bazaku fito ba mu tura, Wlh ban iyawa ni kaɗai," Jin hakan yasa su fitowa daga cikin motar suna faman tikar dariya, azmee tace"Haba junaid wannan fa ƙaramin aiki ne, sai kace ba Namiji ba haba karka ban kunya mana, Be a Man,' Kallon azmee yayi yana faman sauke haƙi yace"In dai saina tura wannan jibgegen gate ɗin zan zama namiji, to Allah abarni a jinsin mace yafi mun," Fashewa da dariya sehrish tayi har tana dafe ciki jin abunda junaid yace,

Table of Contents

Chapters

47 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47